FOURTY

3.9K 378 123
                                    

And help one another in goodness and piety, and do not help one another in sun and aggression | Surah Ma'idah (5:2)

♧♧♧♧♧♧♧

ALIYU SODANGI RESIDENCE
MAITAMA

Zaune suke a falon Daddy suna hira a lokacin da ta shigo a hargitse.

Gaba dayan su sun cika da mamakin ganin ta. Mummy ce tayi saurin miqewa ta janyo ta suka zauna yayinda tace "Maleeka lafiya? ya haka? ina MK din??"

Cikin kuka tace "Mummy wallahi bazan iya zama a gidan ba.."

Daddy wanda yake kallon ta ne yace "akan wane dalili??"

"Daddy wallahi Honey baya so na kuma.. kullum yana maqale da yarinyar nan, wulaqanci suke yi mun. Kullum yana cikin masifa da zagi na sannan har mari na yayi saboda yarinyar.. yanzu haka hatta kwana na duk ya bata"

Nikuwa nace what??

Tunda ta fara magana suke kallon ta. Daga Daddy har Mummy basu gamsu da zancen Maleeka ba.. musamman Mummy wadda ta san mugun kishin Maleeka... ita ta ma ga qoqarin ta da ta zauna tsawon lokaci ba'a jiyo wata rigima ba sai yanzu.

"yanzu kina nufin dan uwanki MK ne yayi miki haka??" Daddy ya tambaye ta cike da takaici.

"eh Daddy.."

"tashi ki tafi sashen ki"

Cike da jin dadin response din Daddy ta miqe ta wuce sashen ta yayinda suka bi ta da idanuwa.

Bayan ta shige ne Mummy tace "wallahi yarinyar nan bata jin magana... yanzu fa daga jin wannan bayanin nata ka san qarya take yi"

Daddy wanda ya fashe da dariya ne yace "Allah yasa ba wata muguntar tayi ma yarinyar ba ta gudo.. "

Ya kalli agogo sannan yace "Allah ya kai mu gobe MK din yazo mu ji abinda ke faruwa tunda dare yayi yanzu"

♧♧♧♧♧♧♧♧

Washegari!!

Zaune suke a falon yayinda yake sauraron Mummy wadda ta fadi dukkanin abinda Maleeka ta fadi musu jiya.

Tunda Mummy ta fara magana MK yake kallon Maleeka cike da mamaki... where did all the lies came from??

Bayan Mummy ta gama magana ne MK wanda yake kallon Maleeka yace "Babe abinda ya faru kenan??"

Dago kai tayi tana kallon shi yayinda hankalinta yake a tashe.. ita fa ta san qarya tayi toh amma what was she supposed to do??

Gani suka yi ta fashe da kuka yayinda ta matsa kusa da shi tace "Don Allah honey ka saki yarinyar nan.."

Mummy ce ta kalli Daddy wanda shima ita yake kallo.

Ban ankara ba na ga Daddy ya miqe cikin fushi ya nufi wurin Maleeka zai zabga mata mari amma MK yayi saurin kare ta yace "Daddy don Allah kayi haquri.."

Tuni Maleeka ta firgice ta fara rusa kuka.

Cikin masifa Daddy ya nuna ta da yatsa yace "dan ubanki mu zaki raina ma wayau?? tun jiya da kika yi mana bayanin mun sani sarai qarya kike yi.."

Ya nuna MK ya cigaba da fadin "kin ga wannan?? Dan uwanki ne wanda yake son ki tsakani da Allah.. nayi imani da Allah bazai taba cutar da ke ba.. da kike fadin ya saki matar shi ke meyasa bazai sake ki ba? wannan rashin mutuncin naki ya isa haka nan.. wallahi idan kika cigaba da wannan iskancin zan raba auren ku.. Gidan shi kuma idan kin ga dama kar ki koma, ki cigaba da zama a nan din. Daga ni har Mummyn ki bazamu qara sa bakin mu a al'amarin ki ba.."

UMMI | ✔Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin