THIRTY NINE

3.9K 352 213
                                    

(All) praise is due to Allah (SWT), whose is what is in the Heavens and what is in the Earth, and to Him is due (all) praise in the hereafter; and He is the wise, the aware | Surah Saba (34:1)

♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Abu dai kamar wasa Ummi ta qi yarda MK ya matso kusa da ita tun jiya da daddare..

Tun da jiri ya kwasheta ta fadi a jikin shi ya dauke ta ya kai ta dakin ta ta kore shi.

Ya so ya san yadda take ji idan da akwai taimakon da zai iya yi mata amma sam ta qi sauraron shi.. Kukan da take ta yi shine ya tada mishi hankali matuqa... haka nan ba don ya so ba ya qyale ta tunda abinda take so kenan.

A yau da safe ma da ya shiga dakin nata qin sauraron shi tayi... dukda bata bari ya matsa kusa da ita ba ya fahimci cewar akwai zazzabi a jikinta don haka ne ya kira Dr. Zeenat.

Da qyar Ummi ta amince Dr. Zeenat ta duba jikinta.. sossai likitar tayi mamaki domin kuwa babu wata matsala mai tsanani, ta fahimci rashin natsuwa da tayi shi ya janyo take jin pains sannan ta kula Ummi tana da raki sai kuma shagwaba sannan kuma qila harda yarinta...

Da qyar ta lallabata ta sake gasa jikinta a ruwan zafi sannan ta sha magani da fresh milk.

Likitar dai ta tabbatar ma MK cewar babu wata matsala don haka ya kwantar da hankalin shi. A haka tayi mishi sallama ta tafi.

MK ne ya bude qofar dakinta ya shigo..

Gani nayi ya tsaya cak yayinda ya zaro idanuwa cike da mamaki.

Ummi ce a tsaye ta shirya tsab alamar zata fita.

toh fa..

Da sauri ya qarasa wurinta ya kamo hannunta yace "Baby meye haka?? ina zaki je??"

Fizge hannun ta tayi ba tare da ta kalle shi ba tace "gidan Goggo zan tafi.. zan roqe ta mu koma Rugange.."

Ni kuwa nace Kamar fa ta san hanyar gidan Goggon..🤣

Wannan maganar ta so ta bashi dariya amma ya matse..

Hannunta ya qara riqowa ya janyo ta suka zauna kan gadonta sannan yace "Haba Baby.. kiyi haquri mana.. Hamma bazai qara ba, kin ga fa ba laifi na bane.. ai ke ce kika nemi mu cigaba kuma fa da amincewar ki.."

"toh ni ban san cewar abinda zaka yi mun ba kenan... yanzu ka ji mun ciwo ka sa ina ta jin zafi.. shikenan ka lalata mun rayuwa..."

Wannan karon dai fashewa yayi da dariya yayinda ta danna mishi harara.

Da sauri ya natsu tare da fadin "don Allah kiyi haquri Baby.. nima ban so na baki wahala ba.. ke ce kika ruda ni gaba daya kuma da kin natsu, da kin ji dadin abinda nayi miki"

Ya qara matse hannunta a cikin nashi ya cigaba da fadin "...kin ga fa abinda muka yi jiya ba laifi bane.. ko manzon Allah yace.."

Fizge hannunta tayi ta miqe tare da fadin "toh ai bai ce kayi mun mai zafi ba.."

Janyo gyalenta tayi tace "ni tafiya zanyi.."

Da sauri ya miqe ya tare ta yace "don Allah kar ki tafi... wallahi Baby idan kika tafi zan mutu"

Jin haka kuma sai tayi saurin kallon shi cikin ido yayinda jikinta yayi mugun sanyi..

A wannan lokacin sai ta ji lallai bazata iya tafiya ba toh amma kuma abinda yayi mata fa??

Tana turo baki tace "idan na tsaya zakayi mun alqawari cewar bazaka qara matsowa kusa da ni ba.. ka amince??"

Zaro idanuwa yayi yace "what??"

UMMI | ✔Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ