TWENTY SEVEN

3.5K 335 160
                                    

Do what is beautiful. Allah loves those who do what is beautiful | Surah Baqarah 2:195

♧♧♧♧♧♧♧♧

GIDAN GOGGO
RUGANGE VILLAGE

Bayan sallar azahar Goggo tana zaune a kan tabarma tana dama fura da nono.

Cikin sallama MK ya shigo gidan yayinda ya qarasa wurinta ya tsugunna har qasa ya gaishe ta.

Cikin fara'a ta amsa sannan ta nuna mishi tabarma a gefen ta tace "Ga wuri ka zauna Kabiru.. Ya kuka koma jiya??"

●●●●

MK dai a jiya ko da Goggo ta gama bashi labarin Ummi sossai ya tausaya ma yarinyar.. Sossai ya ji haushin Baffa da Daada..

Ya so dauko 'yan Human right su bi ma Ummi hakkin ta musamman a wurin Daada wadda ta nemi ta wulaqanta mata rayuwarta amma Goggo tace ya bar su kawai tunda dai abinda suka yi ma yarinyar bai tsinana musu komai ba..

Yayi ma Goggo alqawarin zai kula da Ummi matuqar yana raye kuma bazai taba barin mummunan abu ya same ta ba haka kuma bazai taba bari ta wulaqanta ba.

MK ya sanar da Goggo cewar washegari zai zo ya tafi da Ummi saboda aikinshi da ya baro a Abuja...

Sun tattauna akan abubuwa da dama sannan ya tafi...

abubuwan da zaku jiyo daga baya don haka ku bi ni bashi..!!!

●●●●

"lafiya lau Goggo.."

"bisimillah ga fura.. dukda na tabbatar da Ummi tana kusa da ta hana ka sha tunda bata so.."

Shi kam jin tace Ummi bata son Fura da Nono sai ya ji shima har ga Allah baya so.

Kai tsaye yace "Alhamdulillah Goggo"

"au.. kai ma baka sha kenan"

Murmushi yayi ba tare da yace komai ba.

Tana ta dama furar ta ne tace "ai dazu da safe Bashir ya kawo likita ta duba ta... sannan Kabiru wadannan kaya da ka aiko ai sunyi yawa.. wa ya fadi maka mu 'yan qauye muna ciye-ciye haka?"

Yana dariya yace "kiyi haquri Goggo, me likitar tace?? na manta ban kirata ba... dayake akwai wasu 'yan abubuwa da na tsaya yi"

"eh toh babu wata matsala.. kawai ciwon da yake bisa goshinta ne wanda shima tace zai warke"

"bata yi mata allura ba dai ko??"

Goggo tana dariya tace "ai ta fadi mun wai kace kar ayi mata allura.. Ummi kam ai bata son allura ko alama... da dambe fa aka dinga yi mata alluran da nake kai ta chemist..."

MK shima yana dariya yayinda ta cigaba da fadin "...Likitar dai ta bata magunguna, ka ga lokacin shan na ranan ma yayi bata sha ba.. bata yi sallah ba sannan abincin nata yana nan ajiye a dakin bata ci ba"

"tana ina ne??"

"tana cikin daki tana bacci tun dazu.."

Miqewa yayi yace "bari in duba ta.."

Goggo ita ma ta miqe ta dauki furar ta tace "Nima bari in shiga duba Mairo a nan makwabta ta haihu ban je barka ba.. Yau din zaku tafi ko??" yayinda ta nufi wurin tsohon qaramin fridge dinta ta sanya shi a ciki.

"In sha Allah Goggo"

"toh madallah.. ni sai na dawo"

******************

Kwance take a kan katifar dakin yayinda take bacci. Gaba daya ta dunqule a cikin hijabinta kamar wadda take tsoro..

MK wanda ya shiga dakin zama yayi a gefen katifar yayinda ya sanya mata idanuwa.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now