THIRTY ONE

3.3K 337 169
                                    

Do not follow that of which you have no knowledge. Indeed! The hearing, the sight and the heart – about each of these you will be questioned | Al-Isra 17:36

♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Fatima ce zaune a main falon gidan.

Ummi ta shigo falon sanye cikin doguwar Jallabiya wadda ta bala'in yi mata kyau. Ta yafa gyalen jallabiyar a kanta yayinda jelar gashinta wanda ta kitsa ya sauka har bayanta. Fuskar ta fayau amma fa tayi kyau sossai tunda dai dama Ummin ku kyakyawa ce..

Fatima dai tunda ta shigo ta sanya mata idanuwa yayinda take mamakin wai wannan itace aka ce 'yar shekara Goma sha bakwai..

like how??? lallai fa Maleeka is in trouble!!

Cikin fara'a Ummi ta qaraso tace "Adda ina wuni"

"lafiya Babyn Hamma.. ya gida??"

"lafiya lau.. bari in kawo miki abun motsa baki.."

Da sauri Fatima tace "yi zamanki 'yar uwa..."

Bayan Ummi ta zauna ne Fatima tace "ya fadi miki cewar zamu fita ko??"

"eh Adda.. amma ina zamu je?"

"wurare dayawa..."

♧♧♧♧♧♧♧♧

Ummi dai tunda suka fita da Fatima shopping suka je suka yi na kayan sawa masu yawan gaske.. Kama daga dogayen riguna, English wears, night wears, inner wears da sauran su.

Dukda anyi rigima sossai da ita wurin zaben kayan, Fatima bata bi ta kanta ba. Haka ta dinga kwasar mata kaya masu zafin gaske yayinda ita Ummin ta dinga kumbure-kumbure.

Cosmetics ma ta zabar mata masu kyau da tsada, turarruka ma haka designers. Sossai suka kashe kudi.

Bayan sun gama siyayya ne suka nufi plush beauty lounge (salon and spa).

Ko da Ummi ta bude kanta gaba daya masu aikin salon din harda customers aka dinga mamaki ana yaba kyau da tsawon gashin ta..

Ma'aikatam wurin ma cewa suka yi basu taba ganin mai tsawon gashin Ummi ba.. Ganin ta fara sol suka dinga fadin ai da ganinta ma ba 'yar Nigeria ba ce.. 

Dayake dai yawanci da turanci suke magana ita bata ma san abinda suke fadi ba..

Fatima ce take ta sauraron su yayinda take ta kwasar dariya na rudewar da suka yi. Ummi kuwa ganin suna ta maganan ta ne ta tambayi Fatima abinda suke fadi and she told her...

Haka aka gyare mata gashinta yayi kyau sossai.. ga wasu mayyuka masu kyau, qamshi da tsada da aka sa mata. Dayake anyi mata stretching sai gashin ya qara tsawo. Ita kanta tayi mamakin ganin yadda gashinta yayi tsawo.. abin har tsoro ya dinga bata.

Masu wurin sun so suyi ma Ummi gyaran jiki domin kuwa sun iya sossai amma Fatima tace basu so. Sun dai yi mata pedicure da manicure.. Ummi dai nan da nan ta canza kamar ba ita ba.

Straight gidan Fatima suka wuce wanda yake Maitama.

A nan ne kuma Fatima ta fitar da wasu turarruka da mayyuka masu qamshin gaske kala-kala...

Ta tara ruwa a Jacuzzi bath ta sanya turarrukan wanka masu qamshin bala'i a cikin bath din sannan ta umurce Ummi akan ta shiga ta zauna a ciki na tsawon lokaci.

Gaba daya bathroom din da dakin sai qamshin turarukan suke yi.

Bayan ta fito ne ta hada ta da wasu mayyuka ta shafa a jikin ta tas. Ummi dai gaba dayan ta banda qamshi babu abinda take zabgawa.

UMMI | ✔Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora