TWENTY

2.8K 287 126
                                    

The good deed and the bad deed are not the same. Return evil with good | Surat Fussilat (41:34)

♧♧♧♧♧♧♧♧

Assalam my beautiful readers..

Thank you so much for your love❤
I appreciate you guys alot!!😘

The comments from the last chapter though🤣🤣
I sooo much enjoyed reading each and every one of them..!!

Maleeka dai ta ji jiki.. masu tsine mata suna yi sannan masu salati da rubutun larabci ma suna yi..🤣🤣

Well... Masoyan Ummi ina mai baku haquri akan abinda ya faru.. ku cigaba da salati sannan a duqufa wurin roqon Allah akan ya kawo mata sassauci!!

Keep Voting and commenting.. it's the only way ME and my STORY are gonna feel loved and blessed!!❤

♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Wuraren qarfe goma na dare ne security ya bude gate din gidan yayinda motar Fahad ta shigo.

Security din ya duqa har qasa alamar yana gaida su... MK wanda yake riqe da wayar shi cike da tsananin damuwa bai ma kalle shi ba.

Dayake glass din motar a dage suke horn kawai Fahad yayi mishi.

A lokacin da suka kai porch din gidan ne MK ya bude qofa zai fita.

Fahad ne yayi saurin riqo hannun shi yace "abokina ko in jira ka duba ta ne???"

"kar ka damu... just go home and rest. incase of anything I will call you"

"okay, take care"

Ko da MK ya fito qofar baya ya bude ya cire jakar shi.

Ma'aikatan gidan ne suke ta yi mishi barka da dawowa wanda gaba dayan su babu wanda ya kalla balle ya amsa.

Daya daga cikin su ma da zai karbi jakar hannushi dakatar da shi yayi sannan ya shige cikin gidan.

Fahad wanda yake kallon shi har ya shige cikin gida ne na ga ya girgiza kai sannan ya tada motarshi yace "it's time you realise cewar son yarinyar nan kake yi abokina.. wannan damuwar da ka shiga is not normal"

MK dai basu gama meeting dinsu ba sai gab da magrib.. bayan sun gama meeting din yayi ta kiran Ummi a waya amma a kashe.

Hankalinshi yayi masifar tashi domin kuwa bai taba neman wayarta ya ji ta a kashe ba. lokutta da dama sai dai ya kira har ta gama ringing bata amsa ba wanda kuwa hakan yana nuna cewar bata kusa ne...

but switched off?? why??

Aikuwa nan da nan suka shirya dawowa Abuja. Dayake dama da private jet din shi sukayi tafiyar babu wani bata lokaci suka kamo hanya.

Daga airport zuwa gida ne ma suka bata lokaci saboda 'yar tazara da keda akwai tsakanin airport din da gida. MK dai duk gudun da Fahad yake yi da motar Sam bai gani ba... gani yake yi kamar ma rarrafe yake yi. Sossai yake cikin damuwa. Sai addu'o'i yake yi akan Allah yasa Ummi tana nan lafiya.

***************

Tsaye take a jikin window na dakinta riqe da wayarta a kunnen ta yayinda ta hango shigowar su MK.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now