THIRTY THREE

3.7K 347 99
                                    

And do not let your dislike of a people lead you to be unjust | Surah Al-Ma-idah 5:8

♧♧♧♧♧♧♧

MK SODANGI RESIDENCE
ASOKORO

Tsaye take a gefen shi tana ta kallon shi yayinda yake gaban vanity mirror na dakin shi yana qarasa shirin zuwa ofis.

Ummi dai tun jiya da ta ji labarin cewar su Abba sun amince da auren su ne take cikin tsananin farin ciki. A yanzu haka sunyi da MK idan ya dawo daga ofis zasu je gidan.

MK wanda yake qoqarin zura agogo a hannun shi ne ya ga tayi saurin karba tare da fadin "bari in sa maka Hamma..."

Yana murmushi yace "toh Baby nagode.."

Yana ta kallonta har ta gama sa mishi.

Bayan ta gama ne tace "saura takalmin ka, mu je ka nuna mun wanda zaka sa.."

Janyo ta yayi da sauri ya rungume ta ba tare da yace komai ba.

Kusan tsawon mintuna biyar suna a wannan position din. Bugun zuciyar juna kawai suke ji yayinda qamshin junan su yake ratsa su.

Ummi wadda take manne a jikin shi ce ta saki ajiyar zuciya tace "Hamma zaka yi latti fa.."

Muryar shi qasa qasa yace "laifin ki ne ai.. "

"me nayi??"

"kin hana ni tafiya.. ban taba son kasancewa tare da wani abu ba kamar ke Ummi, meyasa kika shiga raina da yawa haka??"

"Hamma nima fa kana raina.. kullum fa ina cikin tunaninka. wallahi bana so ka fita kawai dai don aiki..."

Kafin ta qarasa magana ne yace "shirya mu tafi tare..."

Zaro idanuwa tayi tare da breaking hug din tace "dagaske Hamma??"

"eh.. ai dama baki taba zuwa ofis dina ba don haka ki zo mu je.. idan na gama meeting dina ma sai mu tafi gidan Abba daga can kawai"

Cike da murna tace "toh Hamma bari in je inyi wanka.."

A guje ta fita daga dakin yayinda ta barshi a nan tsaye yana murmushi.

With each second that passes qara son Ummi yake yi.. MK dai yayi ma kanshi alqawarin tarayya ta aure bazata shiga tsakanin shi da ita a yanzu ba domin he sees her as a small girl that is not ready for that.. Ya tsara akan sai nan gaba idan ta qara girma!!

Shin zai iya???

***********

Yana zaune a falon shi ta fito sanye cikin doguwar riga ta Jallabiya yayinda ta yafa gyalenta a kanta. Tunda ta fito MK ya sanya mata idanuwa.

Babu kwalliya a fuskarta amma tayi bala'in kyau. Ummi is a natural beauty.

Ta qaraso wurin shi sai zabga qamshi take yi. Tana murmushi tace "na shirya Hamma"

Ajiyar zuciya ya saki sannan ya miqe yace "kinyi kyau Baby.. Yanzu haka zamu fita mutane suyi ta kallon ki?"

Cikin rashin fahimta tace "Hamma baka so a kalle ni ne? meyasa??"

Ya girgiza kai yace "zan fadi miki watarana"

Tana riqe da jakar Macbook dinshi suka fita.

♧♧♧♧♧♧♧

MK-TECH SOFTWARE COMPANY

Tare suka shigo kamfanin.

Yana riqe da hannunta yayinda take riqe da jakar Macbook dinshi.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now