EIGHT

3K 267 47
                                    

He knows what is within the heavens and earth and knows what you conceal and what you declare. And Allah (SWT) is Knowing of that within the breasts | At-Taghabun 64:4

♧♧♧♧♧♧♧♧

ALIYU SODANGI RESIDENCE

Zaune take a kan katifar dakin su wuraren qarfe daya na dare. Gaba daya bacci ya gudu daga idanuwanta.

Abinda ya faru tsakanin ta da MK take tunowa.

A yanzu dai Ummi ta gane sunan shi MK kamar yadda ta ji kowa yana kiran shi. Ita dai tun ranar da ta fara ganin shi take jin shi har cikin ranta. Sossai yake affecting rayuwarta.. tunanin shi ya mamaye Zuciyarta. Sossai take ji da tana da hali bazata taba bari wani mummunan abu ya same shi ba... Ji take yi kamar it is her duty to protect him a rayuwar nan... A yadda take jin shi kuwa zata iya sadaukar mishi da rayuwarta.

Ajiyar zuciya ta saki yayinda ta tuno abinda ta ji lokacin da Jameela ta ga emergency contraceptive pills a wurin Maleeka wanda yawanci da turanci suka yi magana.... dukda kuwa bata jin turanci ta dan tsinci hausar da suka yi.

●●●●●

"Leek yanzu kina nufin irin zaman da kika shirya yi a gidan Ya MK kenan?? ki hana kanki haihuwa??? toh wai tsaya ma... Baki son shi kenan ko me??"

"Jay ba haka bane... ni fa kawai bana son yara ne kuma fa kinga idan na haihu tun yanzu gaba daya jikina zai lalace.. I dont want to lose my shape for anything"

Jameela wadda take cike da mamaki tace "na shiga uku da ke Leek... Ya MK ne fa.. mutumin da yake son ki fiye da kowa a duniyar nan..mutumin da kullum burin shi bai wuce ya ga 'ya'yan da zaki Haifa mishi ba..."

Maleeka ta dakatar da ita tare da fadin "kar ki damu Jay, it's just for a while... nan gaba kadan idan na shirya haihuwa zan daina sha amma wallahi yanzu babu abinda zai hana ni shan wannan maganin idan dai har zai hana ni daukar ciki"

Jameela tace "toh shikenan Leek.. Allah ya baki sa'a"

●●●●●

Gani nayi Ummi ta runtse idanuwanta yayinda tace "Allah sarki Hamma.. Allah yasa ta canza ra'ayinta"

Gani nayi ta dan dafa kanta wanda yake yi mata ciwo yayinda ta miqe ta shiga bathroom tayi alwala.

Bayan ta fito ne ta sanya hijabinta dogo har qasa ta shimfida dadduma ta fara jero sallan nafila.

Bayan ta idar kuwa ta dinga jero addu'o'i wadanda yawanci duk na MK ne.

Haka kawai ta tsinci kanta da yi mishi addu'o'i na neman tsari daga sharrin masu sharri tare da yi mishi fatan alkhairi.

Bayan ta gama kuwa ta jingina da bango ta fara karanto haddar Al-qur'ani mai girma.

Sai wuraren qarfe uku na dare ne ta koma gefen Inno ta kwanta.

Babu laifi kuwa ciwon kan nata ya sauka.. Har sanyi ta ji a zuciyarta.

♧♧♧♧♧♧♧♧♧♧

SURFERS PARADISE YHA,
GOLD COAST, AUSTRALIA

Tsaye take gaban Vanity table yayinda take taje gashin kanta wanda ya sauka har gadon bayanta.

Sanye take cikin wata pink babydoll nightie wadda tayi revealing dukkan content na jikinta. Sai qamshi take zabgawa.

MK ne ya shigo dakin...

Asali dai ya je ofis din manager na hotel din don yayi signing wasu papers....

Gani nayi ya tsaya cak yayinda yake qare mata kallo cike da tsananin so da qauna.

UMMI | ✔Where stories live. Discover now