FIVE

3.3K 295 113
                                    

Indeed, Allah is my Lord and your Lord, so worship Him. That is the straight path | Surah Ali 'Imran 3:51

♧♧♧♧♧♧♧♧

ALIYU SODANGI RESIDENCE

Wuraren qarfe biyu na dare tana zaune a bisa katifar da ta kasance ta dakin su a matsayin su na ma'aikata.

Kuka take ta yi babu sassautawa. Ummi dai ta kasa bacci a yau. Da ta kwanta ta rufe idanuwan ta sai ta dinga ganin fuskar shi. Sossai take jin shi a ranta.. ji take yi kamar ta gano wani abinda ta rasa a rayuwarta tun da dadewa.

Inno wadda suke zama dakin tare ce ta ji sautin kukan ta a cikin bacci. Ko da ta bude idanuwa ganinta tayi zaune ta kifa kanta bisa gwiwarta.

Da sauri Inno ta tashi zaune ta janyo ta tace "Ummi lafiya kike ta kuka??? ba dai akan marin da Hajiya qarama tayi miki bane??"

Girgiza kai tayi alamar ba wannan bane.

Cikin kuka tace "Dada ni fa wallahi ba laifi na bane. Kin ga shine ya taba ni kuma sai na ji kamar wuta ta ja ni... Dada na shiga uku.. ya hana ni bacci. Ni bana so ina ganin shi a bacci na... zuciyata tana yi mun wani iri.. don Allah ki taimaka mun..."

Inno wadda duk ta bi ta rude tana shafa kanta tace "ki daina kuka Ummi.. na tabbatar saboda kin sa abin a ranki ne shiyasa kika damu.. Itama hajiya qarama kiyi qoqari ki qara bata haquri gobe kin ji"

Ummi tana share hawayen ta tace "toh Dada.. nagode"

Inno tayi murmushi tace "babu komai Ummi, ni na dauke ki a matsayin 'ya wadda na haifa da ciki na. Tunda kika zo gidan nan na kula da lallai kina da hankali da natsuwa. Ki cigaba da haquri Ummi, ni ina ji a jiki na cewar rayuwar ki zata yi haske nan gaba, Allah bazai barki haka ba Bi'iznillahi ta'aalaa"

Ummi tace "gettaɗɗo Dada"

Inno ta harare ta tace "kin fara fulatancin naki kenan ko?? ni kam ban san abinda kika ce ba.."

Murmushi Ummi tayi sannan tace "Haba Dada... sau nawa zan koya miki wannan?? kawai fa ina nufin nagode ne"

A haka dai Inno ta lallaba ta suka koma bacci dukda dai ita Ummi bata koma ba domin kuwa ta kasa. Fuskar MK kawai ke dawo mata da zarar ta rufe idanuwa...

Why??

♧♧♧♧♧♧♧

Washegari wuraren qarfe goma sha daya na safe tana kwance a kan makeken gadon dakinta yayinda Jameela take zaune a gefen ta.

Jameela ce tace "yanzu jibi Layla Hayat din zata iso??"

"yes Jay, Mummy tace jiya sunyi waya da ita tace jibi zata baro Egypt"

"gaskiya matar ta iya aiki, na tabbatar she will do wonders on you.."

Maleeka ta turo baki tace "ni duk ba wannan ba Jay, takura ni da za'a yi ne bana so. Mummy fa tace idan aka fara gyaran jikin nan bazan qara fita ba... ai wannan punishment ne"

Jameela ta Harare ta tace "meye punishment anan?? hutawa fa zakiyi Leek besides bikin ki ya matso so you need to reduce all these your to and fro movements"

"wallahi Jay don dai bani da anything to take care of a fanin business dina but I swear har ranar auren zan iya tafiya.."

Kafin ta qarasa maganar ta kuwa Jameela tace "what?? is your business more important than your wedding da kike fadin haka?? duk shirin da kika yi??"

"No Jay, My wedding is more important but the business is equally important.. aure na da Honey can take place even if we are not present amma kuma business dina can't survive without me.."

UMMI | ✔Où les histoires vivent. Découvrez maintenant