60

98 2 2
                                    

                           EPILOGUE:


                          EPILOGUE:

********Kowa ka kalla zaka ga zallar farin cikin dake tattare da shi. Musamman Baba da mutane suke ta haba haba da shi, murmushin fuskar sa ta ƙi ɗaukewa idan sa har wani ƙyallin ƙwallar farin ciki ce a cikin ta, ya bar garin bayan shekaru da yawa tun Hafiz yana da shekaru goma, amma a yau ya dawo Hafiz yana da shekaru talatin harda huɗu. Shin daman ba su manta da shi ba? Tambayar da yayiwa kan sa kenan. Yana sake kallan dubbin mutanen dake gaban sa. Idan ya kalli mutanen sai ya kalli Mahafiyar sa dake gaisawa da wanda suka san ta, itakam ta manta mutane da yawa sai an tuno mata su sai ta tuna, haka zai juya ya kalli matar sa itama dake cikin mutanen su mata suna gaisawa ana ta raha da dariya. 

Tunawa yayi da ranar da ya fita daga garin,kowa be san ganin fuskarsa, babu wanda ya yarda da shi sai abokin sa guda ɗaya wanda Allah ya yayiwa rasuwa shima. Shi kadai ne ya yarda da shi, har ta mahaifin sa da yake tsananin san sa be aminta da shi ba, shine ya yanke wannan hukuncin mafi muni a gare shi na raba shi da kowa da kowa, ya kuma tafi ba tare da ya nemo su ba. Duk da ya san inda suke, ya kuma saki mahaifiyar sa akan sa. Dukkan abin nan be taɓa masa zuciya ba irin sakin da ya yiwa Hajja saboda shi.  Wani irin ruwan hawaye ya ji yana cika masa ido sakamakon abinda ya tuna. Kafin ya maida kallan sa wajen Deeni shi da Hafiz ya ɗauki mai sunan sa shi kuma yana rike da Zaid. Sai murmushi suke yi suna zancen su. Shima murmushin yayi yana ɗan goge ƙwallar sa a kai kace.....

Ahmad ne ya katse masa tunani ta hanyar kiran sunan sa yana taɓa shi.

"Baba Noor ta fasawa wani kai, wai dan yace mata bebiya".

"Yana ina?

Jan hannun Baban yayi har wajen da mutane suka taru a wurin, wanda hakan yaja hankalin su Deeni suma suka yi wajen, suna zuwa suka ga abinda Noor tayi, ta haɗe rai tamau irin laifin nan aka yi mata. Wani babba a wurin yace.

"Amma duk yarda akay i wannan ƴar Hajiye ce ga kamar nan".

Wani yace, "Ƴar ta ce kam, dan itama haka ta sha fasawa yaran mu kai".

Deeni dafe goshi yayi kawai yaja ta suka fice daga wajen suka shiga gida. Hafiz ya bita zai zaneta.

Deeni yace, "A'a wallahi ba zaka dakar min ƴa ba".

"Kamar ya ba za'a dake ta ba? Kana ganin abinda tayi?

"Ba ruwan ka, ƴar ka ko ƴa ta?

"Haka kace? To ka rabu da ita, itama ta zama kamar uwar ta ta addabi ƴan unguwa".

Harara ya zabga mata yana wucewa ciki, ita kuma ta sake ɓoyewa a bayan baban ta tana ƙifta ido na marasa gaskiya. Fito da ita yayi ya tsugunna dai-dai tsayin ta.

Yace, "Me yasa kika yi haka?

Maganar kurame tayi masa kamar yadda suke magana.

Yace, "Kiyi haƙuri kinji? Ba zai sake ba uhm?

Ɗaga kai tayi alamar toj. Sai tayi masa alamar da to ya bata haƙuri.

"Uwar haƙuri zai baki ba haƙuri".

Ameer ya faɗa yana ƙarasowa. Cune baki tayi.

Yace, "Bayan abinda kika masa har sai ya baki haƙuri? Saboda yace maki bebiya?

Ƙara haɗe rai tayi.

Deeni yace, "Ya isa bana so muje ya baki haƙuri kinji?

Ya faɗa yana miƙawa Ameer Zaid. Yayin da Ameer da Taufiq suka baki suna kallan ikon Allah, kafin su kalli juna suka kalle su da ya wuce ya bar su a wajen.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now