18

25 1 0
                                    

*****Brazil : Belo Horizonte.

Yau babu inda ta je tana zaune a gida dan sosai damuwa ke damun ta rashin jin yayan ta da tayi, bare daman ita da abu kaɗan ne zai shigo sahun ta ya dagula mata lissafi.

"Maryam".

Faɗin Fa'iz dake zaman kusa da ita har suna gogar juna, ɗan matsawa tayi kaɗan.

Tace, "Na'am ina yini".

Murmushi yayi yana shan abun sha.

Yace, "Ke duk sanda za'a maki magana sai kin gaida mutum?

Ɗan murmushin yaƙe tayi tana ɗan ƙara matsawa.

"Gaisuwa bata ƙarewa ko?

"Uhm".

Ta faɗa tana ɗan janye jikin ta ganin da wayo wayo sai matsowa yake.

"Wai meye hakan? Ba kin amsa min soyayya ta ba, to koma meye muyi mana uhm?

Kallan shi tayi bata ce komai ba.

"Magana nake maki".

"Ni kake yiwa maganar?

Ta faɗa idan ta akan sa.

"Da wa ni ne bayan ke anan?

"Soyayyar dana amsa maka na amsa ne saboda ka dena bibiyata".

"Kamar yarda na furta na amsa, yanzu kuma na janye bana son ka".

"To waye wanda kike so ɗin?

Kallan shi tayi cike da mamaki, tace, "Ba damuwar ka ba ce".

Daga haka ta tashi zata wuce ya fincikota ta ta dawo jikin sa ya rungume ta tsam a jikin sa.

Yace, "Ba de wannan kike ma gudun ba? To zan yi maki mai gaba ɗaya ma naga iya gudun ruwan ki. Kuma duk sanda nake so nayi abinda na ga dama".

Tashin hankali, ƙarara ya hango a cikin idan ta, wannan bala'in har ina haka? Kokawa suka fara yi har ta samu nasarar guduwa ya sake kamo ta, ya yaga rigar dake jikin ta. Dai-dai nan Anty ta shigo.

"Fa'iz?

"Anty ita ce ta ja ni. Kin ga ma rigar ta da ta yaga dole sai da ta ci galaba akai na Anty ba laifi na ba ne".

"Maryam".

Kuka Maryam take yi sosai ta ƙudundune waje guda yana sharɓar kuka, wanne irin abu ne wannan? Idan tana da hankali ai kallo ɗaya zata mata ta gane abinda ke faruwa ko? Janyo rigar ta tayi ta yane jikin ta da ita tana cigaba da kuka mai cin rai.

"Kike so ki lalata min ɗa na?

Wani irin kuka da tashin hankali ne suka ziyarce ta, sosai take shashsheka kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu take ji tsabar yarda take jin zuciyar ta.

"Munafuka sumi sumi dake ashe ba haka kike ba ?

"Amma de wannan uwar ki tayi asarar haihuwa....".

Tashi tayi da gudu ta shige ɗaki, ba zata iya tsayawa a zagi Mom a gaban ta ba, uwa uwa ce duk lalacewar ta. Yarda ba'a sauyawa tuwo suna haka itama ba zata sauya Mom a matsayi mahaifiyar ta ba. A kan gado ta kwanta ta janyo wayar ta, tana duba time taga bakwai da rabi na dare a Nigeria yanzu shadaya da rabi na dare kenan. Wayar taga numbern Nigeria na kira da sauri ta ɗaga.

Ɗalhat ne ya kira ta, dan ya gaji da kewar ta, ga kewar Ameerah ga ta Maryam abin sai yayi masa yawa hakan yasa shi cewar Dalha ya siyo masa sim card, shine ya kira ta har ya kwanta ya kira ta.

"Maryam".

Zabuwara tayi jin shine sai kuma ta fashe masa da wani irin kuka mai cin rai da tsayawa a zuciyar da baza'a manta ba. Irin dokawa zuciyar sa tayi yana tashi zaune, be ce mata komai ba kawai yana sauraron kukan nata ya tabbatar da ita kukan ne kawai take yi amma shike zafi da raɗaɗin kukan nata. Sai da ya ji ta fara sararawa da kukan sannan.

ZARAHADDEEN Donde viven las historias. Descúbrelo ahora