56

49 2 0
                                    

56

******Koda safe da ta tashi babu wanda tayiwa magana ta je ta ɗebo ruwan ta a waje ta cika randar da sai idan wanki za suyi ne za su ɗebo ruwa. Ta cika ta dam ta share gidan, duk da be sharu ba amma yayi ɗan rage ƙurar. Ta wanke toilet ɗin su da ruwa sannan ta shiga tayi wanka ta je ta shirya, samun kan ta tayi da saka kayan da Hafsah ta bata, sai take tuna sanda ta je gidan su suna azabtar da Ameerah sai shi yau ƴar maƙiyan su da Dad ke kira ita ce ta taimake ta, ta kuma sanar da ita abin da uwar ta bata taɓa zama ta sanar da ita ba, shi yasa su suka ci gaba a rayuwarsu domin sun sa Allah a ran su. A nasihar da ta mata harda riƙo da addini sallah akan lokaci kaɗai wata falala ce da Allah yayiwa bayin sa, sai ta ji ita fa har gwara ita tana sallahr ma, Musaddiq fa?

Kallan kanta tayi a madubin powdern ta sai taga ta fi kullum yin kyau, wannan shine karon ta na farko da ta sa ka Hijabi a tsayin rayuwar ta.Sanda ta fito dukan su sun tashi, an samu koko an siyo de da sauran canjin da suka aro. Da mamakin irin shigar da tayi suke kallan ta. Ta zauna aka zuba mata nata.

Musaddiq yace, "Wannan kayan fa?

Uffan bata ce masa ba, ta sha kokon da babu sugar a cikin su, domin ta yarda zata amshi rayuwar ta a duk halin da ta zo mata. Haka ta fita neman abinda zata rufawa kan ta asiri domin abinda ta ɗauke shi sana'ar ta ne, ta tabbatar ba Alkhairi ne akan ta ba. Tana tafe tana goge hawayen ta tare da tunanin rayuwar ta ta baya, da kuma ta yanzu inda ta lura akwai banbanci mai tazara, ko shigar da tayi da dane an ringa nuna ta ana yi da ita, wani ma yace kamar Christan, amma yau ko kallan inda take babu wanda yayi. Tana tafe wannan nazarin rayuwar ta ta, bata ankara ba sai ga ta a supermarket ɗin Zarah da Ummu.

Ummu ce a supermarket ɗin ta fara zuwa daman tana riga Zarah zuwa, tunda yanzu Zarah ba kullum take zuwa ba, ita kuma ba makaranta ba shi yasa kullum take shagon na su. Ta gama clearing ɗin komai zata koma office ɗin ta kenan, Safiyya ta shigo tana kallan wajen, yaushe rabon da ta shiga irin wannan wajen?

"Lafiya?

Cewar wata mai aikin su, dan duk wajen mata ne, masu gadi ne kawai maza.

Ɗan goge ƙwallar ta tayi tana ɗan sakin murmushi bakin nan duk ya bushe.

Tace,"A'a dan Allah idan da wani aiki a bani. Aiki nake nema da zan ringa yi ana ɗan biya ne ko ya yake".

"Kinga dalla Malama fita".

Ummu tace, "Clarity meye hakan?

Ta faɗa tana matsowa kusa da su, dan ita kam har ga Allah bata san Safiyya ba ko tace ta manta ta, itama Safiyyan ba sanin Ummun tayi ba. Wani irin tausayi ta bawa Ummun..

Tace, "Kinga muna da masu aiki, amma tunda Hassana tayi aure, kafin ta dawo bakin aikin ta ta kama aikin da take yi, idan ta dawo sai su ci gaba a tare".

"Amma Madam Ummu..."

Taufiq da shigowar sa kenan yace, "Har jayayya kuke samun damar yi tsakanin ku da masu aikin ku?

Cewar sa yana zuba mata ido, dan shi kuma haka kawai Allah ya zuba masa rashin san Clarity dan bata da hali matar, ita de indai wani zai samu ba ita ba to sai hassada, kuma daga Ummun har Zarah ba wani faɗa ne su ba na ku zo mu gani, daman shi da Ameer ke takawa shegiya burki kamar ba Allah da Annabi tayi ba aka ɗauke ta aikin..

"Kayi haƙuri sir".

Tsaki yaja yana yin hanyar office ɗin Ummun.

Ummu tace, "Ki bata aikin, ki nuna mata idan kun gama ki min magana da ita ina neman ta".

"To Madam".

Tana barin wajen.

Tace, "Sai muje waya sani ma ko mayyace amma ki sani sai na kore ki a wajen nan".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now