8

31 1 0
                                    

✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
     

             By

       *Hijjartabdoul*


                 8.



****kowa a cikin su jigun ya samu yayi ya zauna Kamar wanda aka ce musu mutuwa aka yi. Shigowar da Hafiz yayi ya gan su a haka sai suka bashi tausayi.

Yace, "Meye hakan? Ku fito Baba nasan magana da  ku. Ana jiran ki zaku tafi".

Ya ƙara she da kallan Maryam sannan ya fita. Haka suka fito jiki a sanyaye suka sauka yi  ƙasa. Yayin da Maryam ta kuma gaida Baba da Umma ta musu sallama ta fita, duk sai take jin ta babu daɗi itama ganin kamar ba san auren yayan ta amma kuma ya zatayi, wani gefe kuma na zuciyar ta yana bawa iyayen na su laifin rashin zumuncin su sai de ba zata ce ga dalilin ba tunda bata san mene ya faru ba. Cike da tunani iri-iri ta ƙarasa motar su suka tafi.

Yayin da Baba ya sa su a gaba da wata irin nasiha mai ratsa jinin jiki da ruhi, kowa shiru yayi jikin su na ƙara yin san yi, nasiha ce yake musu cike da hikima gami da sa zuciya salama, gefe guda kuma kamar wata wasiyya ce yake bar musu, su riƙe mutuncin su sannan kuma kada su yada zumuncin dake tsakanin su, akwai sanda za sh rabu kowa ya kama gaban sa, idan ina yi hakan kada yaji kada ya gani ace babu ziyarar juna. Yayin da Hafsat take kawai kallan Baba dan ita har ga Allah gani take kawai mutanen asiri suka yiwa Baba da kuma Hajja daman ita Umma bata ta, ta kawo ta dan ita sai abinda aka ce mata bata da wani abu da zatayiwa kan ta sai, kawai janta ake yi duk inda aka ga dama. Sosai hakan yake mata ciwo a zuciya, to su wanne irin mutane ne wai ? Kasa shiru tayi da bakin ta da Baba ya gama maganar sa.

"Baba wai ka manta irin abubuwan da mutanen suka yi maka? Kuma yanzu ka ɗauki ƴar ka, ka ba su?

Murmushi yayi mata mai kyau, ya sani da cewar kaf cikin su ta fi kowa riƙe abu, idan ta riƙe ka to har ka mutu ba zata manta ba, ba kuma da saurin yafiya a tsarin ta shiyasa ko me aka mata sai ta rama bata da haƙuri, ɗan ita da za'a bar ta ma sai sun rama irin cin mutuncin da suka yi wa iyayen ta.

"Hajiye, meyasa baki da yafiya?

"Baba ai ba su cancanta ace an yafe musu ba".

"Ko?

Jinjina masa kai tayi alamar eh, dan ita har zuciyar ta take faɗa.

"Ehh mana Baba. Kuma me yasa ba su ce ni ba? Suka ce Ameerah?

"To Hajiye ya zan yi? Yaron Ameerah yake so ba ke ba, kuma mahaifin yaron nan ya ta so ya tako ya ce yana so mu haɗa yaran mu. Mu manta abinda ya faru tsakanin mu, mu haɗa zumunci. Hajiye sai na ce a'a?

Sunkuyar da kan ta ƙasa kawai tayi, batare da tayi magana amma cikin zuciyar ta kawai uzuri take yiwa Baban na su da fatan Allah yasa ya gane gaskiyar kuskuren da ya aikata.

Taufiq yace, "Kuma Baba yaushe za'a kai ta? Ba zamuyi biki ba? Ba wanda zai zo?

Ummu tace, "Ehh Baba kaga wannan shine bikin farko".

Baba yace, "Zakuyi abinda kuke so idan za'a kai ta nan da wani satin, amma shi yaron baya san duk wannan abubuwan dan haka ba zai zo ba".

Ameerah tace, "Wani satin Baba?

Sai kuma tayi saurin saukar da kan ta ƙasa, jin tana shirin yin abun kunya, wani irin kuka na zuwar mata.

"Ko be miki ba?

Baba ya faɗa cike da kulawa, kasa magana tayi sai girgiza kan ta da tayi kawai, tana ɗan share hawayen ta, sai Baba ya ji ba daɗi shima.

Taufiq yace, "Yauwa Baban mu daman gwara ma kar mijin ya zo".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now