16

30 1 0
                                    

*****"Ka zo ka sani a gaba ka min shiru tun ɗazu kai baka yi magana ba kai baka tafi ba".

"Ina su Ameerah suka tafi?

Kawai kallan shi yake, kafin ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana shan ƙaddarar shayin sa.

Yace, "Wace Ameerah?

Da mamaki Ɗalhat ya ɗago yake kallan sa.

"Ameerahn da ka cuta ita da iyayen ta kake so ka ce baka sani ba?

"Ohh! Allah sarki. Ai wannan na manta da shafin su. Na so ace ma ba su biya kuɗin dana sa musu ba, sai gashi acikin kwana ɗaya tal wai sun biya abin da mamaki".

"Naje gidan su ake sanar da ni cewar ai sun tafi. Shine nake tamabayar ka ina suke?

"Nima bansani ba tunda na sami abinda nake so ina ni ina bibiyar su?

Tashi Ɗalhat yayi yana mai wani irin murmushin takaici ya ajje masa paper a gaban sa batare da yace komai ba ya juya ya fice, sai da yaje baƙin ƙofa ya ji muryan sa.

"Ta meye ka ajje?

Tsayawa yayi batare da ya juyo ba. Yace, "Zaka iya dubawa. Idan kuma ba zaka iya karantawa ba na dawo na karanta maka".

Daga haka ya wuce ya barshi a zaune yana zubawa ƙofa ido, wato baƙaramin kuskure yayi ba kenan ta haɗa wannan auren, amma koma meye de tunda mai faruwa ta faru kuma ya sami abinda ya ke so shikenan.

"Ɗalhat".

Cak ya tsaya jin kiran da Hajiya take masa, be juyo ba sai da ya ji ta a bayan sa.

"Yanzu akan wannan yarinyar kake min haka?

"Shine maganar da zaki min?

Be jira amsar ta ba yace, "Zan maki abinda ya fi haka muddin ke da ƴar ki baku fita hanya ta ba".

Daga haka ya wuce ya bar ta. Baƙaramin mamakin sa take ji ba. Yana zuwa kwashe kayan sa yayi ya fice ko minti ɗaya be ƙara yi ba a gidan, babu wanda ya ga fitar shi sai maigadi. Yana fita Alhaji ya fito daga ɗakin yana ƙwala masa kira dukan su fitowa suka yi suna kallan sa ganin tashin hankalin dake fuskarsa, ya wuce ya shiga parlourn sa baya nan ya shiga duka ɗakunan baya nan su Hajiya na biye da shi a bayan sa kowa da abinda yake tunanin mene ya faru kuma.

"lafiya?

Yana watsi da pillows ɗin parlourn yace, "Ina lafiya? Ni yaron nan zai ajjewa aiki? Ni ? Me yake nufi da hakan?

"Yana nufin wata banza mace ta fika muhimmanci...."

Tas! Ya wanke Hajiya da marin da bata taba tsammani ba a zaman su, ba Hajiya da ta dafe kunci ta sandarewa ba su kan su yaran ƙamewa suka yi cike da ɗimbin mamakin sa.

"Kada ki kuskura ki sake haɗa ni da yarinyar maƙiyi na, domin itama bana san ta".

"Kuskure na biyu da kika yi kuma shine da kika ce ta fini muhimmanci a wurin sa ".

"Ai naga shi ɗin ma ba san sa kake ba kuɗi ne kawai kake so ka cimma shima ka sallama shi...."

Wani marin tasha a fuskar ta, hakan yasa ta yace, "Wallahi ko zaka kashe ni bazan dena faɗar dukkan abinda na sani ba".

Daga haka ya juya ta fice tana kuka wiwi kamar ƙaramar yarinya, yayin da su Safiyya suka ja jikin su simi-simi suka fice daga parlourn, haka ma Hashim da yake jin abun kamar almara kamar mafarki de yake haka, kasa riƙewa yayi kawai ya wuce club ita kuma Safiyya party ta wuce haka ma Musaddiq duk suka fice dan gani suke ba hurumin su ba ne ba, tsakanin su ne za su gyara kan su. Yayin da shi kuma yasa duk inda yake a nemo masa shi cikin awa ɗaya.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now