38

20 1 0
                                    

38


******Kallan sa kawai ta tsaya yi batare da ce komai ba, kallo ne na, iya wannan kalmar kawai? Amma ta ɗauke ni har tsawon wannan lokacin ban faɗa ba?

Zubowar da hawayen ta yayi ne yasa ta rufe ido, yayin da shi kuma ya sake matsowa kusa da ita ya share mata hawayen, ya kama duka kumatun nata ya riƙe da hannunsa tare da haɗe goshin su. Buɗe idan ta tayi tana kallan ta, shi kuma yana sakar mata wannan shegen murmushi nasa da take cewa na mugunta, ganin haka yasa ƙwace fuskar ta tana sakar mata duka. Dariya yayi yana gocewa.

"Me nayi kuma?

Ya tambaya yana riƙe hannun nata ganin zata sake dukan sa, majina ta sake ja taja neman ƙwace hannun ta, sakin ta yayi ya ɗauko mata tissue ya miƙa mata. Hararan sa tayi tana turo baki gaba, kawai ita kunyar kanta taji tana yi ma.

"Goge mana".

Ya faɗa yana sake zaman a kusa da ita.

"Hafsat ina so ki dawo mutum kamar kowa".

Kallan sa tayi tana turo baki.

"Ni aljana ce?

Murmushi yayi mata. Bece komai ba ya tashi zai tafi, da sauri ta riƙe hannun sa.

"Dan Allah kayi haƙuri ban sake wa".

Ba musu ya dawo ya zauna a kusa da ita. Suna kallan juna ita da shi, ya bata dukkanin hankalinsa kamar yarda itama ta bashi duka nata hankalin. Cikin wannan muryan nasa sake saka wa mutum nutsuwa gami da jin wani irin sanyi a rai da ruhi.

Yace, "Hafsat. Nasan kin aure ni badan kina so ba".

Da sauri ta ɗago ta kalle shi tare da ƙwalalo ido tana masa wani irin kallo, wani murmushin ya saki mai kyau. Ya riƙe hannun ta tare da jinjina mata kai.

Yace, "Nasan da wannan tun kafin ki furta".

Sai ya sake sakar mata murmushi.

"Baka bani amsa na ba".

"Ita zan baki yanzu".

Ya faɗa yana tashin ta suka koma gadon su, ya kwantar tare da yi mata pillow a cinyarsa ya zame ta hular dake kan ta suna kallon juna yana shafa mata sumar ta cike da kulawa.

Yace, "Abinda nake so yana da yawa, zaki iya bani duka?

Ƙura masa ido tayi tana kallon sa. Batare da tunanin komai ba ta ɗaga masa kai.

"Wannan halin da kika sake shi nake so, ki kasance a cikin sa. Ba faɗa, ba hayaniya, ba zagi, ba masifa, ba zafin rai. Ki zauna cikin ƴan uwa kuyi wasa kuyi dariya, ki ji matsalar su, ki ba su shawara. Ke ce ɗaya mace babba a cikin su, wani abun Ameer ba zai iya zuwa ya faɗawa Hafiz ba, amma sabon da kuka yi da shi zai iya zuwa ya faɗa maki. Dukan su suna da wata damuwar da suke ɗauke da ita batare da mun sani ba. Kuma so na suyi maganar da wani na so babba, amma ba sa samun fuskar yin haka".

"Hafsat, wanda yake da ƙannai, ba faɗa ne ya dace a gare su ba. Komai suka yi ba suyi dai-dai ba, komai suka yi kiyi banza ki rabu da su. Haka ba shine rayuwa ba. Ƙannan mu wani irin nauyi ne da Allah ya ɗaura mana suna da hakki akan mu. Idan yau aka ce Umma bata nan waye zai zamar musu uwa? Bamu da ƴan uwa irin sosai ɗin nan, ki duba rayuwar mu tun daga farko kiga ni, yarda muka ta so da wurin da muka so, da kuma mutanen da muka ta so a cikin su. ke kan ki  haka Umma ta maki a lokacin da ba kowa? Har Umma faɗa take maki akan wannan zafin rai naki".

Shiru yayi ya tsaya da shafa mata kan. Yayin da ita kuma ta zuba masa ido kawai tana kallon sa.

"Bansani ba, ko zaki gyara ko ba zaki gyara ba. Amma wannan shine abu na farko da nake so da ke a rayuwar mu".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now