25

27 1 0
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

By

*Hijjartabdoul*

25.

*****Kewayen su aka kai shi yagani, kawai murmushi yake yana tuna rayuwar da suka yi anan ɗin. Babu wanda ya shiga wajen yana nan yarda suka tafi suka barshi sai ginin ƙasar da ake sake yiwa shafe duk shekara gudun lalacewa, duk da cewar sun nuna ba sa sun Abba amma kuma sun tsare masa kewayan sa da jiran cewar wata rana zai dawo, kuma ba su bar shi haka ba suke gyara shi. Koda aka buɗe masa kawai ganin ɗakunan yayi, yarda suka tafi haka ya zo ya tarar da su, sai masifar ƙura da kayan suka yi. Ga samirun da kumbo nan na Ummi dan ita Mama bata da wannan gatan da za'a ce an yi mata kayan ɗakin irin na Ummi a wancan lokacin. Yana nan tsaye aka kira yara sai gani yayi ana fitar da kayan ɗakunan waje yace su bari kar aje maciji yana nan yayiwa mutun illah. Suka ce masa ina ai ba abinda zai sare su ko ya cije su sun sha maganin tauri da tsari. Shi de fita yayi ma ya bar su wajen. Suka share suka gyara komai aka kaɗe aka goge komai yayi tas aka wanke na wankewa kamar ba shine aka shekara da shekaru ba. Shide tun da ya fita be dawo ba sai da aka kusa magriba dan canza Kawu Bala da Kawu Isubu suka yi suke kaishi gidan ƴan uwa, har mamaki yayi da yaga makaranta a ƙauyen na su, be mantawa shi da Sadiq sai sun share tafiya mai tsayi kafin su je makaranta sannan su dawo.

Mamaki ne ya kama shi ganin yarda aka gyara kewayen yayi kyau da shi kamar wanda ake rayuwa a cikin sa, ɗaki ya buɗe yaga an kwashe komai an sa masa babbar katifa na gyara shi, ɗayan kuma an shirga kaya a cikin sa, girgiza kai kawai yayi yana janyowa. Tare da su ya sha ruwa gaba ɗaya sai tambayar sa ya gida suke yi, yayi aure? Ina ɗan uwan sa, nawa ne yaran Kabir yanzu shide kawai nasa murmushi ne be ce komai ba banda wannan murmushin da yake faman yi musu.

Koda ya je kwanciya wayar sa ya ɗauko ya kira Hafiz da Sadiq, sannan ya rufe idan sa yana mai sakin ajiyar zuciya ba karamin gajiya yayi ba yau ɗin nan ba. Duk da haka be hana shi yin tunanin sa ba da ya saba yi a kullum. Kafin ya gangaro kan Hafsah yana tunanin ko yanzu me take? Sai ya samu kan sa da murmushi kawai ya janyo wayar sa ya danna mata kira.

*****A bakin Ameer take jin cewar yayi tafiya, amma shine ko ya faɗa mata, sai a bakin wasu zata ji, abin ba ƙaramin ƙular da ita yayi ba, ya bata haushi har bata san ma'aunin da zata saka yarda take ji ba. A ranar ta shiga ƙuncin da bata san dalili ba. Gani take ko waye de kuna kwana ku tashi tare ɗaki ɗaya ai ya ci ace an sanarwa da mutum tafiya ko addu'a mutum yayi ai ba laifi ba ne ba. Amma shine ya tashi ya yi tafiyar sa ya rabu da ita.

Yanzun ma yana kwance a kan gado, ita de bata san mene ya faru ba, kawai taga ta kwanta a ɓarin da yake kwanciya tana shaƙar turaren sa mai sanyin ƙamshi, luf tayi tana tunanin haɗuwar su kawo yanzu da yake gasa mata aya a hannu. Tashi tayi zaune tayi tagumi tana mai janyo wayar ta. Ita da bata da numbern sa me zata ce masa? Ko tana da shi ba zata kira ba tunda be sanar da ita tafiyar ba. Komawa tayi ta kwanta ta sake tashi ta juya haka ya ringa yi, Kafin ta samu ta kwanta.

"Ko me yake? Ko yana ina? Ko ina ya tafi? Me ya ci? Me ya sha ? Yayi bacci?

Haka ya ringa jerawa kan ta tambayar da bata san su ba. Bata jin ma shi ya damu da ita kamar yarda ta damu da shi. Janyo wayar ta tayi ta duba lokaci, taga goma da rabi.

"Yayi bacci?

Ta sake tambayar kan ta. Sai kuma ta ja tsaki ta dungurar da wayar, ta fara jin haushin kan ta da kan ta. Jin wayar na ƙara yasa ta ɗagawa. Be yi magana ba kamar yarda itama batayi ba, jin shirun ya yi yawa sata kashe wayar tana jan tsaki.

Daga can ɓangaren ƙaramar dariya Deeni yayi yasan yanzu ya kunna ta. Ƙara kira yayi bece komai ba. Yayin d ita kuma cike da masifar da ta zame mata jiki.

Tace, "Idan ba za'ayi magana ba kar a sake kira ni. Bana ciki da kut**".

Ta kashe wayar ta gaba ɗaya tana dungurar da ita, tare da shafa kan ta,bata san meke damun ta ba.

ZARAHADDEEN Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz