7

19 1 0
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                7.





****Sai da ta fito ga tafiyar ba su kaɗai ba ne ba harda Ɗalhat da Abban su da Musaddiq. Mota uku suka yi Alhaji da Hajiyar sa, Maryam ta da Musaddiq sai Ɗalhat shi kaɗai Hashim baya nan.

"Ina zamu je?

Musaddiq ya tambayi Maryam.

"Nima bansani ba".

Har suka je babu wanda ya kuma cewa uffan a cikin su. Kowa na danna wayar sa a hankali kwance.

"Wannan gidan fa?

Cewar Musaddiq yana wani ya mutse fuskar sa, kallan gidan tayi da za su shiga, gidan mai kyau dai-dai na mutanen dake cikin sa a wadace a komai kuma upstairs ne.

"Me yayi?

Tambaye shi dan ji me zai ce.

"Haba kinga fa, sai de a ƙauye".

Drivern na dai-dai ta parking.

Tace, "Wasu mutanen ba su sami wannan ɗin ba. Ginin duniya ba wurin zaman ba ne ba".

"Ai ke daman haka kike ba daman ayi ɗan zance dake sai ki fama yiwa mutane waye waye".

Murmushi tayi masa tace, "Shikenan Musaddiq amma ka sani wata rana zana mutu ko? Idan ka mutu kuma sai a kai ka da ginin da ya fi na Baban ka kyau".

Daga haka ta fice ta barshi a cikin motar, shiru yayi yana nazarin maganar ta ashe wata rana zai mutu ko? Idan ya mutu kuma a ƙasan ƙasa za'a burne shi. Jiki a sanyaye ya samu de ya fito yana kawar da tunanin da ta dasa masa. Suma acan motar Alhaji da Hajiys mita take masa ita wannan auren da za'a yi kawai cutar mata da ɗa zai yi, yaran da ba wani arziki ne da su ba, je bi fa gidan da suke ciki kamar na almajirai sai da ta lallaɓata sannan suka fito. Suna shiga wani irin  ƙamshin turaren wuta ya daki hancin su mai daɗin gaske ga kuma sanyin ac da ƙamshin freshners masu daɗi da sa nutsuwa, fes fes parlourn yake, Maryam ce a gaba dan tasan ba sallama za suyi ba, ita ce tayi Sallamar tana shigowa sannan suka biyo bayan ta, an samu Alhajin yayi sallama.

Duka amsa musu suka yi suna mai tashi zaune, dukan su suna parlour har Baba da Umma amma banda Hafiz da Hafsat. Cike da farin ciki Ba yake musu sannu da sannu zuwa, sai da suka ƙare musu kallo a fakaice duka matan doguwar riga ce a cikin su iri ɗaya sai ƙaramin mayafin da suka ya fa abin su. Yayin da mazan suka sha dinkin su na kufta sun yi kyau suma. Umma lace ɗin ta tasha mai kyau da tsada hannun ta cike da gwal din ta sai mayafi da ta yafa. Batare da Hajiya ta nuna musu komai ba ta karɓe su da murmushi tana ɗan murmusawa kamar gaske. Yaran suka gaida ta, yayin da Maryam ta gaida kowa haka ma Musaddiq.

"An zo lafiya? Sai muka ji tafiya babu shiri kuma".

"Wallahi kuwa ba".

Cewar Baba.

"Ina Hajja kuwa?

"Hajja na ciki bata jin daɗi ne shiyasa".

"Ayyah, ko ƙafar ce?

Dake ya san tana da ciwon ƙafa tun da can da suke tare. Baba ya amsa da eh. Kasancewar Musaddiq sa'an Taufiq ne yasa  Taufiq miƙa masa hannu da'alamar su fita waje haka, ba'a san ran sa ba ya bashi hannun sa suka fita waje shide duk wani iri yake jin sa. Ameerah da Ummu kuma suka shiga da Maryam ɗakin su domin bawa iyayen na su waje su gana.

"Ina wuni".

Cewar Maryan ganin Hafsat a zaune a tsakiyar gado tana aiki. Ɗagowa tayi ta amsa da lafiya ta cigaba da abinda take.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now