22

45 1 0
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

       
                      22.

******

"Zaka je kam".

Cewar Hafsah tana shan mur, ƙarfe huɗun ma bata cika ba, tayi saurin tashi ta fita wajen motar sa ta shiga gidan baya ta yi luf a ƙasan kujerar dake saiti da shi ta yarda ko juyowa yayi ba zai ganta ba, shi kuwa sai da aka yi sallah dashi sannan ya zo ya tafi. Kwata kwata be san da mutum a motar ba sai da ɗau hanya sannan tayi wuf ta fito tana zama a ɗayan side ɗin da ba kowa, ita kan ta ta bawa kan ta dariya bare kuma shi da aka yi ɓoyen dan shi kuma be sani dan sosai ta bashi tsoro da farko amma yarda ta wani sha mur ne ya ba shi dariya. Banza yayi da ita kamar be san da ita ba. Gani tayi sun nufi wani wajen daban ba hanya ba, ya tsaya yayi siye siye sannan suka tafi gida.

"Yau me zaka ci?

Banza yayi da ita kamar ba dashi take magana ba.

"Magana fa nake ma".

Nan ma yayi banza da ita, sai Tafseer ɗin dake tashi a motar tasa hannu ta kashe, ya kunna.

Yace, "Yanzu zaki fitar min a mota tunda ba gado".

"Wallahi ina da gado idan ka mutu".

Ta faɗa tana hararan sa. Banza yayi da ita har suka shigo gida ganin gate a buɗe ya basu tabbacin yanzu Hafiz ya dawo dake yana riga su Sadiq dawowa. Sai da ya dai-dai ta parking ɗin sannan ya dube ta cike da kulawa.

Yace, "Kina da gado ne kawai idan ina san ki, amma babu gado ga macen da mijin ta baya so".

"Wannan karatun fa?

"Baki zo wurin ba".

"Malam kar ka rena min hankali mana".

"Kin san nayi ƙarya ai tunda maƙaryaci kike aure".

Shiru tayi ta kasa fita daga mota, ita de tasan abinda yake faɗa ba haka ne ba, amma kuma ko dagaske karatun nata be zo nan ɗin ba? Shi kuwa ficewa yayi ya kwashi kayan su Umma ya kai mata daga nan ya wuce part ɗin su, har zai shiga ɗaki sai ya zauna ya na lissafin, tana zuwa zata kwanta tace ta gaji. Ko gama zancen be yi ba kuwa ta bankaɗo ƙofa ta shigo. Zata kwanta.

Yace, "Kayan dake motar ni zan kwaso maki?

"Ban gane ba?

"Kina so duk abinda kike yi naje na sanarwa da Baba da kuma Umma ko kuma na sanar da Hafiz kin san zan iya ko?

Shiru ta tsaya tana yi tare da zuba mata idan ta.

Yace, "Zaɓi ya rage naki, kiyi ta sani magana biyu ki gani toh".

Daga haka ya ajje key ɗin mota a gefe ya tashi ya wuce ɗaki, harara ta banka masa.

"Dan da me iyayi kawai".

Ta faɗa tana turo baki gaba. Ta wuce ta kwaso kayan ta kawo Kitchen tana buɗewa yogurt ɗaya ta gani a kayan na su, hakan yasa ta ɗaukan Yoghurt ɗin ta nufi ɗaki.

"Nace wannan Yoghurt ɗin ɗaya na gani ina nawa?

"Kin yi azumi ne?

"Amma kuma ko ban yi azumi ba ina da haƙƙu da a bani nawa kamar yarda aka bawa kowa nasa".

"Kece haƙƙun ɗin ai".

Ya faɗa yana fara cire kayan sa a gaban ta.

"Meye hakan?

ZARAHADDEEN Donde viven las historias. Descúbrelo ahora