48

22 0 0
                                    

********"Wani shegen kallo yayi mata yana ɗauke kan sa, tare da sake shaƙe Musaddiq yana ɗaga shi da hannu ɗaya, ya zabga masa zafafan maruka masu shegen zafi.

"Bana marin da ka mata ba ne ba, ba hannun ka ya taɓa fuskar ta ne".

Ya faɗa yana haɗa hannun sa da nasa ya lanƙwasa,  Sannan ya wurga masa harara ya wuce ya bar shi. Yana zuwa ko kallan inda take be yi ba ya zauna ya tamke fuskar sa tamau. Haka ta ƙaraci kukan ta tayi shiru sai ta fara satar kallan sa, tana jin shakkar sa a ran ta. Har wani matse jikin ta take yi.

Shi kuwa Musaddiq banda ihun azaba babu abinda yake yi yana yarfe hannun nasa yake yi yana matse ruwan hawaye.

"Waye wannan ɗin?

Safiyya ta faɗa tana kallan taimakon sa. Sai da ya nutsu.

Yace, "Nima bansan shi ba, kawai wani jaka ce na mara ƴar ƙauye shine zai min wannan abun, to wallahi idan  muka sauko ni kaɗai nasan me zan yi mata idan ya so ya kashe ni".

"Aikuwa zai kashe ka".

Cewar Hajiya.

Tace, "Ehh zai kashe ka, muddin ka sake shiga gonar sa ka rabu da shi tunda kai ne ka fara masa laifi nasan da wannan".

"Amma...."

"Idan ka ji kenan".

Ta faɗa masa kallan baka da hankali, haka ya zauna ya cika yana batsawa har suka je inda za su je, be samu yayi bacci ba. Be gan shi ba ma da suka zo sauka, dan su ne kawai suka sauka, su ba'a nan za su sauka ba.

"Wai ba zaki dena kukan nan ba?

Ameer ya faɗa yana ɗan kallan ta, sai a yanzu ya ji zuciyarsa na ɗan bashi haƙuri. Ganin idan ta kalle shi sai ta sa kuka, duk da ya tsayar da kukan amma ana jimawa take sake matsar ƙwalla. Matsar da jikin ta tayi sosai jikin window, dan kada ma ya mata magana, kawai sai ya tsaya yana kallon ta tsabar mamaki wato tsoron sa ta fara ji ko me? Ajiyar yayi ya sassauto da murya can ƙasa ya fara lallashin ta, ita de bata ce masa komai ba sai de ta dena kukan. Sai dare suka zo, sun gaji kam iya gajiya.

"Ke kuma me ya samu fuskar ki?

Ummu ta tambaye ta.

"Wani ɗan iska ne ya mare ta....

Ameer ya faɗa sai kuma yayi sauri yace, "Tsaya, kamar Musaddiq ko?

Ya faɗa yana kallan Taufiq, fuskar sa kamar bata sauya ba, sun taba zuwa gida ko? Ka tuna?

"Wanne Musaddiq ɗin?

"A. Madaki mana".

Taufiq yace, "Gaskiya ba zan iya gane shi ba, wannan ɗan renin wayon?

Ummu tace, "Kamar na ganshi a jirgi fa".

"Ba kamar ba ne ba, to shine".

"Wannan yaron ai daga yanayin maganar sa zaka gane baya da tarbiyya shege mai kalar ifiritu".

Taufiq ya faɗa.

Sadiq yace, "Zaku taho ko kuma zaman zaku ci gaba da yi?

Hafiz yace, "Da ka rabu da su, mun tafi mun bar su".

Bin shi suka yi, suka yi taxi uku sannan suka tafi. Sai de suna zuwa Hafsah ta kalli ɗakin da ya sauka ita kuma ta kalli nata, murmushi tayi tunowa da abinda ta fara masa, waye zai yarda? Idan ba shi ba? Murmushi ta sake saki kafin ta shiga ɗakin. Ganin haka yasa suma su Zarah da Ummu shiga ɗakin.

"Uban me ye kuka zo?

"Babu exra rooms fa sai mai parlour kuma Baba yace mu haɗu anan".

Bata ce musu komai ba kawai ta shige toilet, tana fitowa ta nemi Noor ta rasa dake kan gado.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now