9

26 1 0
                                    

✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                      9.

*****Kamar de ko yaushe tana kwance a parlour, Abban su ya zo wajen ta, tashi tayi zaune tana gaida shi, cike da fara'a ya amsa yana zama a kusa da ita, tare da miƙa mata passport ɗin ta da komai nata.

"Ki shirya ƙarfe biyu zaki wuce".

Cike da wani irin tarin mamaki take kallan Abban na su wanda har sai ya nuna a fuskar ta.

Tace, "Daaad?

Ta faɗa da sigar tambaya, murmushi yayi mata mai kyau.

"Ki wuce kawai bana san wata magana".

"Amma Daddy ni bance ina san zuwa wani waje ba".

"Ni na ce kina san zuwa wani waje daman ba ke ba".

Tashi yayi yana gyara babbar rigar sa, kamar wanda ya je ɗaurin aure.

Yace, "Ki shirya kafin 2 ɗin tayi".

"Amma...."

"Bana san musu".

Ya faɗa ya zafafe, yana wucewa, rasa me zatayi daga ciki sai kawai ta fara kuka, hawaye ya fara zubar mata a ido ta sa hannu ta share, still wasu ruwan hawayen na sake zuba a cikin su.  Haka ta tashi jiki a sanyaye ta wuce ɗakin ta, littafan addinin ta kawai ta ɗauka da abinda tasan idan taje can ba zata samu ko zai mata wahalar samu su kawai ta ɗiba, ta fito tana share hawayen ta. Batare tayi sallama da kowa ba ta fito, tana fitowa harabar gidan ta ga yayun ta guda biyu, ko kallan inda suke batayi ba ta buɗe mota ta shiga drivern ta na karɓar kayan hannun ta ya sa a boot. Ya zo ya shiga ya zauna. Hannu tasa ta goge hawayen da ya zubo mata.

Tace, "Mu tafi mana".

Kallan ta ya juyo yayi, be taɓa ganin ta a wannan yana yin ba, sai ya danganta da  tafiyar da zatayi, daman aikin sa ita kawai yake yiwa aiki, kuma ance yau zata tafi idan ta tafi kuma shima an sallame shi, shi duk ba wannan ba, ya jima yana san ta amma be san taya zai ce yana san nata ba, idan ma ya faɗa besan me za'a yi masa duk da cewar ita ɗin babu ruwan ta, amma tsoron dake bugun zuciyar sa ya fi ƙarfin san da yake mata.

"Baka ji ba?

Ta kuma faɗa.

"Yi hakuri, Mai gida ne ya ce kar a tafi sai ya fito".

Haɗe rai tayi tamau ta kau da kan ta gefe, ƙwalla na cigaba da fito mata akai-akai tana sharewa, kawai tunanin sabuwar rayuwar da zata je tayi take yi.

"Hajiya kiyi haƙuri ki dena kukan nan".

Murmushi ta samu kan ta da yi, tana sake goge ƙwallar da ta taru a idan ta. Bata masa komai ba, ta madubi yake ƙare mata kallo, shikam Allah ya gani so be masa adalci ba, a rayuwar sa, ya rasa wacce zai so sai wannan? Zalelliyar yarinyar?

"Kamar ba tafiyar ce a gaban ki ba ko ? Me ke saki kuka?

Yayi jarumtar faɗa. Kallan sa tayi bata ce masa komai yanzun ma.

"Kiyi hakuri".

Ya kuma faɗa, ita kam ba abinda zata ce masa dan maganar da yake yi mata ma na so take ba. Zai kuma magana Abban su ya fito ya shiga tashi motar. Duk a cikin su kowa motar sa ya shiga drivern su ya ja su, ita ce a baya dan haka suna fitowa tace ya kai ta inda ya taɓa kai su kwanaki. Be ce komai ba ya jinjina mata kai.

Da sallama ta shiga parlourn na su dukan su suna zaune har an gamawa Ameerah Kitso ana yiwa Ummu an cire jan lalle an yi baƙi. Hafsat ta kwana tana bacci. Yayin da Umma da Gwaggo suke hira abin su.

ZARAHADDEEN حيث تعيش القصص. اكتشف الآن