23

49 2 0
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                   23.

******Kawai a office zaman shiru yayi yana tunani babu abinda ya tsinana tunda ya shigo office ɗin a zaune yake ya kasa taɓuka komai, ji yake ƙwaƙwalwar sa bindiga kawai zatayi ta tarwatse. Tashi zaune yayi ya je wajen windown dake office ɗin sa ya tsaya ya zura dukkan hannun sa a aljihun sa. Yana kallan harabar companyn da kowa ke shige da fice abin sa. Amma a zahiri kam tunani yake yi fal kan sa, tunanin dake so ya addabi rayuwar sa.

"Wai tun ɗazu nake maka magana tunanin me kake?

Jin muryar Hafsah a saman kan sa yasa shi juyowa ya zuba mata ido, ita ma yana tunanin akan ta.

"Ni yunwa nake ji kuma ba zan sha cornflakes. Na ce ko zaka fita ka samu min wani abu da zanci. Ka ga ban ci komai ba".

Ta ƙarashe da kalar tausayi, shi kawai kallan ta yayi, shi be ce komai ba, amma sai de baƙaramar dariya ta bashi. A zancen da tayi ita ba umarni ba, ita ba pleading ba, ita ba statement ba, gashi nan de. Hakan ne ya bashi dariya. Kawai ya ɗan kalle ta ya wuce wajen kujerun sa ya zauna.

"Meye haka? Ina maka magana?

Yanzun ma shiru yayi mata, tayi ƙwafa ta dawo kusa dashi. Zata fara ya tashi ya bar mata wajen ya koma kan kujera.

"Wai meye hakan kake min?

Lapton ya janyo ya kunna kawai ya zuba mata ido. Sai ya shafi kan sa ya ɗago ya kalle ta, calmly yace.

"Ɗan fita daga waje".

"Ni kake kora?

"Ban kore ki ba, haka kawai nace ki fita daga waje".

"Korar kenan ai....

"Hajiya kina ihun ki na samin ciwon kai can you....."

"Please excuse me?

Ta ƙarasa masa tana ƙwaikwayon muryan sa. Shi kuma ya jinjina mata kai yana nuna mata, sai da ta ɓalla masa harara.

Tace, "Ba laifi ka ne ba, laifi na ne dana kawo kai na".

"Da sanki ne abin ma da daɗi to matsalar ba san ki nake ba".

"Nima bance a so ni ba".

Ta faɗa tana banka masa harara ta fice masa a office. Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina da kujerar sa, kafin ya fita daga companyn be dawo ba sai da aka kira Sallahn azahar.  Yana dawowa ya iske yayi baƙi a office ɗin sa. Kuma bana company ba. Abin ya bashi mamaki amma be nuna ba ya shiga office ɗin na sa. Ganin mutane manya yasa shi suka gaisa cike da mutunci.

"Nide sunana Hamisu  Alƙasim. Mahaifi kuma ga wanda yake son ƙauwar ka Zarah Jalal. Wannan ƙanina ne sunan sa Galadima, dukan mu aikin gwamnati muke yi a ministry".

Ɗan murmushi kawai Deeni yayi yana girgiza jinjina musu kai alamar eh na gane be je ga yin magana ba.

"Sanda ya zo mana da labarin mun yi bincike akan ka da kuma yarinyar, a unguwar ku duk labari ɗaya ne ake bamu cewar ku yaran karuwa ne. Sai de kuma inda kuka tashi daga unguwar ta ku labarin ya sha banban da wanda ake bamu a yanzu. Shin mene gaskiyar maganar? Yaro na wajena yana san ta sosai hakan yasa har yanzu da kake ja masa rai be haƙura da ita ba".

Wanda aka ce sunan sa Galadima yace, "Gaskiya ne, shi aure yana da wannan abun, idan aka tashi neman sa dole zaka ji magana daban daban daga wurare da dama. Shiyasa ba'a yin sa kai tsaye batare da bincike ba. Kuma ku kan ku aibata kuke a idan duniya. Shi yasa nace da ɗan uwa na mu ta so mu ji ya batun yake? Mun je gida an ce mana baka nan, mu zo nan".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now