58

53 4 1
                                    

58

********Sanda ta zo Hafiz ya dawo gida, ya ji duk abinda ya faru, da sauri ya kira waya aka bada cigiyar zoben batare da sun sani ba, sosai take kukan abinda A. Madaki yayi mata.

"Dan Allah ku barni anan, bana so na koma gida ya same ni da wannan tambayoyin".

Sai ta sake fashe musu da kuka, sosai suka tausaya mata yayin da suka ji wanj irin shakkar A. Madaki.

Saima tace, "Amma anyi azzalumin mutumi, nifa ban taɓa san wannan mutumin ba tunda can da ake ta wani A. Madaki. A. Madaki na tsane shi wallahi shege azzalumin banza kawai".

"Ke kuma da zagi, ƙanin Baba ne fa".

Zarah ta faɗa mata. Saurin rufe bakin ta tayi tana kalle-kalle.

Cikin raɗa-raɗa tace, "Dan Allah ƙanin Baba ne?

"Wallahi, ita kuma Baban ta ne".

Ƙwalalo ido tayi ta alamar jin kunya sai kuma ta tashi sadaf ta sauya waje ta koma wajen su Taufiq dake saurarensu. Sadiq yana shigowa ma ta tashi daga gaba ɗaya daga parlourn ta  koma ɗakin su Ummu.

Dawowa Hafiz yayi yana kallan ta cike da tausayi yarda take kukan kaɗai abin dubawa ne. Daƙyar suka samu tayi shiru.

"Kana ganin Dad ba zai cutar da ku ba?

Murmushi Ɗalhat yayi yace, "Kema kin san zance ne, a yanzu zuciyarsa ta ƙeƙyashe fansa kawai yake so ya nema, ta abinda aka masa. Ba wai iya dukiyar sa yake son dawowa da ita ba  har kimar sa da bartabar sa da ta zube a idan Al'umma. Amma sai de yana mantawa da cewar har a yanzu yana ƙarƙashin hukuma ne, laifi biyu ne akan sa, muddin yayi wani abun to fa dole sai an kama shi, gidan yarin da be so sai ya shiga".

Kowa shiru yayi babu wanda ya tanka yayin da Ɗalhat yace a kawo yaran ya maida su asibiti wurin iyayen su. Haka aka yi kuwa suka tafi har Hafiz dan yana san ganawa da Deeni.

A zaune suka same su, sun zubawa Noor ido, suna jiran tashin ta, tana jingine a jikin sa ta ɗaura kan ta a kafaɗar sa ba abinda take yi sai aiki zubar da hawaye. Yayi shiru ba abinda ke cikin zuciyarsa sai kaiwa da komawa, irin bugu take masa na tsoron rasa Noor ɗin sa. Jin ana sallama da knocking yasa shi amsawa ƙasa-ƙasa. Suka tura suka shigo, kallo ɗaya yayi musu ya gane akwai damuwa a tattare da Ɗalhat har ma da Hafiz ɗin, kawai ta Ɗalhat ta danne ta Hafiz ne. Miƙa musu yaran suka yi da suka yi baccin wahala, ƙurawa yaran ido yayi yana kallan su, jiyan nan suka zo duniya amma har sun fara shan wahalar duniyar daga zuwan su ko sararawa ba suyi ba. Sun fara gwagwarmaya suma batare da sun san me Duniyar take ciki ba. Kafin su girma suma aga wacce kalar ƙaddarar ce ta su? Shin ya rayuwar su zata kasance, irin tasa? Ko kuma irin ta mahaifiyar su? Baya fata su tashi irin tasa rayuwar gwara ace sun yi rayuwa irin ta mahaifiyar su, su ɗauko duk wani zafin rai da faɗa irin nata, domin ba kowa ne zai iya jure abinda ya jure ba. Tun yana yaro be iya faɗa ba, ko magana aka faɗa masa sai dai ya kalli mutum kawai, amma sam baya da hayaniyar faɗan yara. Be shiga sabgar kowa bare a shiga ta sa. Duk wanda ya shiga kuwa shine zai ji haushi ba de Deeni ba. Amma ita kuwa fa? Baka taɓa bama tayi inaga ka ga taɓa ta? Mutum ce mai faɗa da masifa uwa uba jarabar da ke cin ta. Ga basarwa kamar bata yi ba, ko kamar bata san mutum ba da ita yake.

Wani guntun murmushi yayi yana ɗaura ɗaya a kafaɗar sa, yana jijjaga shi alamar yayi shiru ita kuma ta fara shayar da ɗayan. Yayin da Hafiz da Ɗalhat suka ba su waje domin san cigaba da kadaicewa da su biyun. Sai da yaran suka koma bacci suka kwantar da su a gaban Noor suna kallan su cike da burgewa. Murmushi ne ya ƙwace mata haɗe da guntun hawayen ganin Noor na motsi zata farka. Babu wanda yayi attempting riƙe ta ko kiran sunan ta har ta buɗe idan ta tar akan yaran, wani irin washe baki Noor ɗin tayi zata tashi da sauri sai kuma ta saki ihu ta koma ta kwanta hakan yasa su tashi suka yi kan ta suna kiran sunan ta.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now