4

29 1 0
                                    

          ✨ *ZAHARADDEEN* ✨

   

                          4.

*****Bashi ne ya dawo ba sai yamma lis duk da cewar an bashi hutu ya huta sai Monday ya fito kasancewar tafiya da yayi amma be yi ba gani yake hutun me zai yi kuma bayan aikin dake gaban sa, ko da ya dawo be tarar da su Sadiq ba sai Zarah da ya tarar zata fita, kallan ta kawai yake yi tana saƙala takalmin ta ba wata shiga kwalliya tayi ba amma tayi kyau sosai, cikin ankon ta na ƙawar su da za'a fara aurarwa a ƴan ajin su kowa na ji da bikin duk da ba wani ƙawance suke ba sosai ba, amma kasancewar ita ce ta fari shiyasa kowa ke cewa zai je. Medium mayafi ta yafa akan kayanta da suka yi matuƙar yi mata kyau.  Dagowa tayi daga saka takalmin jin sallamar sa. Cike da murmushi da fara'a.

Tace, "Yaya sannu da dawowa".

Ƙarasowa yayi yana zama a kusa da ita yayin da ita kuma ta tashi ta kawo masa ruwa da lemu, tana komawa ta zauna inda ta tashi.

"Nagode".

Ya faɗa yana ɗaukon ruwan da ajje masa.

"Ina zaki je?

Ya jefa mata tambayar yana kallan ta.

"Yaaa nan bayan layin mu ne, bikin ƙawar mu ɗin nan da ka bani nayi anko? Kuma jiya shine nayi ƙunshi".

Ta faɗa tana ware masa hannun ta wai dan ya ƙara gani bayan ganin da yayi na jiya anyi mata. Bin ta kawai yayi da kallo bece komai ba, ita kuma ganin kamar zai hana ta yasa ta tace,

"Yaaa fa jiya ma fa anyi wani event ɗin amma nasan ba zaka bar ni ba haka zaka ce fitar tayi yawa shiyasa na haƙura banje ba, Yaa yau kawai zanje gobe ba sai naje ba ɗaurin aure tunda gobe Juma'a da wuri kake dawowa kuma ka ce min za mu fita tare da kai dan Allah Yaya".

Kallan ta kawai yake yi har ta gama zancen ta bece uffan ba, sai ma kallan sa da ya mayar kan TVn da take a kashe bece komai ba.

"Gwoggo ta dawo?

Ya tambaye ta amsar da ba ita take tsammani ba.

"Ehh amma taje gida ta dawo".

Ta bashi amsa idan ta na cikowa da ruwan hawayen.

"Kin san zaki fita me yasa ba ki fita da wuri ba?

Ya tambaye ta, batare da ya jira amsar ta ba.

Yace, "Idan kika fita sai yaushe zaki dawo? Bana san wannan shashancin bikin? Kinji ko baki ji ba?

"Naji".

"Kar ki jima".

Kawai yace yana tashi, ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfe tana goge hawayen ta, kuɗi ya ajje mata wanda yasan zai ishe ta sosai, sannan ya tashi, godiya tayi masa ta fita da sauri kafin ya zo ya sauya ra'ayinsa yace ba zata je ba, tasan da cewar Yayan ta zai iya sauyawa ba ruwan sa, gashi de shine yayi mata ankon kuma ta sha faɗa masa cewar za suyi biki amma bece ba za ta ba dan haka ba ruwan sa zai iya sauyawa a koda yaushe yanzun yace ba zata ba. Shi haka yake, gashi de a fuskar sa ba zai nuna ba ko da wasa kuwa. Bata mantawa sanda yake yawan kamata da samari tana hira yau da wannan gobe da wannan jibi da wannan, yayi maganar amma bata ji ba, ranar da ya kamata kuwa da ya zabga mata wani mari ya haɗa da duka ita ce har asibiti Sadiq da Gwaggo ne ƴan zaman jinyar amma shi ko dubiya be je ba a lokacin ta gane Allah ɗaya ne tun daga nan ko sha'awar ace ana san ta ma bata yi, daƙyar ta samu ya haƙura sannan kuma yake mata nasiha. Ajiyar  zuciya ta sauke tuna irin abin da taɓa aikawa ta Yayan na su.

****** Tara yaran nasa yayi a parlour yana kallan su ɗaya bayan ɗaya idan ya kalli wannan sai ya kalli wannan dukan su babu wanda ya san dalilin kira sai Hashim, hakan yasa sunkuyar da kan sa ƙasa batare da ya ɗago ba. Yayin da A. Madaki ya tashi tsaye yana sake ƙare musu kallo tsaf, so yake ya gano inda matsalar take a jikin su amma kuma ya kasa. Hakan yasa shi komawa ya zauna yana haɗe ƙafa tare da ɗaukan shayin da aka kawo musu ya zuba ya bawa kowannen su.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now