34

25 1 0
                                    

     34.





*****A fusace yake yin komai ji yake kamar ya haukace musu ko ya huta, ya tayar musu da hankali ganin babu Hashim babu alamar sa. Wanda suka tabbatar masa da be wucewar be jima da fita ba duka ba za'a yi awa ɗaya ba zuwa awa ɗaya da rabi. Gaga ɗayan sa ji yake kamar ya zauce tsabar yarda yake ji a cikin ran sa, amma fa a zahiri babu abinda yake damun sa banda zallahar murmushin dake fita a ran sa, sai de kuma shi kaɗai yasan me yake binnewa tare da ajjewa. Ko cikkaken awa biyu beyi ba a garin ya koma inda ya fito dan wani irin haushi da takaicin dake cin sa ba zai iya tsayawa yana ɓata lokacin sa ba, yana abinda ya fi masa Hashim muhimmanci a gaban sa. Tunda be same shi anan ba, ya tabbatar ko ya je inda zai same shi ɗin ba samun sa zai yi muddin dan shi yake gudun. Haka ya sake yin awannin a jirgi yana kwasar tunanin gami da takaici. Ga kuma asarar lokaci da yayi, ba shi ne ya zo Nigeria ba sai asuba, gashi yau Litinin yana da meeting mai amfani, yana shigowa yaga Musaddiq a lokacin yake dawowa.

"Kai daga gidan uban wa kake?

Sheƙeƙe Musaddiq ya tsaya yana kallan sa.

Yace, "Dad? Yau ka saba gani na nawa a wannan lokacin?

"Shi yasa yanzu na tamabaye ka".

"Daga masallaci nake".

Ya faɗa yana wucewa domin shiga part ɗin sa. Tsaki kawai A. Madaki yayi ya wuce ɗakin sa, a kan gado yaga Hajiya tana bacci da'alama bata san baccin yayi gaba da ita ba, duba ga irin kwanciyar da tayi, tsaki ya ja yana wuce ta. Da shiga toilet.

Shi kan sa be damu da cewar sun ɓata awowi ba a sarari saminiya batare da yaji Sallah ba a cikin jirgin, yanzun ma da lokutan sallahr suka shige be damu da ya rama ɗin ba, kawai wanka yayi shirya ya fice abinsa, bayan yace a sai masa ticket ɗin Kaduna za su yi meeting. A cikin jerin wanda za suyi meeting ɗin yaga sunan Hafsah me kuma zata je tayi anan?

Dan gaske a yanzu lamarin tsoro ya koma ba shi kuma, ga Hashim ga Ɗalhat baya nan, ga kuma Maryam, shi fa duk wani abu da zai taɓa shi ba so ba yake, ya fi so a ciki gaba da ganin sa da kima da daraja a cikin mutane. Shi kaɗai yasan ya yake ji a cikin ran sa idan ya ji ana yabon sa yana sa masa ana cewa ya gama da duniya lafiya, sai yake ganin cewar ai shikam duniyar sa tayi masa kyau, yarda tayi masa kyan nan da kuma addu'ar jama'a yana ganin acan ɗin ma zai dace. Bayan san abinda zai sa wannan yarinyar ya zubar masa da kima da mutunci, baya san take faɗar abinda ba'a sa ta ba, idan kuma ya cire ta nan ma mutane zasu fara yi da shi.

Cike da wannan tunanin ya zauna ya fara cin abincin sa, sannan ya wuce ya fita daga gidan dan zuwa office kafin su shiga meeting ɗin.

******Dake jiya ba wanda ya fita a cikin su yasa su yau dukan su fita musamman restaurant ɗin da aka buɗe, haka suka yi duk abinda ya dace suka fita dukan su gashi an koma school, sai suka bar Ameerah kawai da Umma dake kula da ita.

A murtuke fuskar nan ta shigo tare da neman wajen zama ta zauna. Ya kalle su dukan su, sannan ta kawar ganin yadda suke ƙus-ƙus. Musamman Aisha, taɓe baki kawai tayi, ta cigaba da abinda take yi. Har Mu'azzam ya zo.

"Kadunar zaki wuce?

"Eh".

Kawai tace masa. Ganin haka yasa shi jan bakin sa yayi shiru. Sai da suka tafiya kasancewar ba ita kaɗai ba ce zata je taga ita da Aisha ne za su tafi, kallan ta kawai tayi bata ce mata bakomai ba, yayin da Aisha ke mata wani irin kallan reni, irin matar saurayina ce fa.

Manya mutane ne ƴan kasuwa masu ji da kuɗi da kuma ilimi, yayin da Aisha take kallan tsirarun matan da basu da yawa, yawanci ma manya ne a wajen. Kowa shigar alfarma yayi banda Hafsah da ta ci hijabin ta da ya sha guga damma ƙasan ya ɗan squeezing saboda zaman mota. Duk kallan da ake mata ko a jikin ta,bama tasan suna yi ba itakam. Gefe guda kuwa A. Madaki ne a zaune shine babba a wajen saboda ya fi kowa kuɗi a wajen. Ko sau ɗaya Hafsah bata juya ta kalle shi ba, tunda ta fuskanci shine a wajen, duk abinda take tana ankare da duk abinda ake cewa. Har aka zo kan ta, tashin da tayi ne yasa dukan jama'ar dake wajen zuba mata ido, yayin da ta haɗe fuska tamau, camera ta fara aiki a akan ta, ana haska ta har ta zo kan stage ta tsaya a gaban dubban ƴan kasuwar dake wajen suna kallan ta. Dai-dai nan wayar ta dake kan table tayi ƙara, kasancewar wurin shiru ake yi yasa ta jin ƙarar wayar ta da ta tashi ta baro akan table ɗin.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now