59

28 1 0
                                    

59

*********Gaba ɗayan su sun yi zugum suna jiran tsammani, dan hankalin su ya tafi wajen Noor ba su ga abinda Hafiz yayi ba. Dan shi kan sa Deeeni ba su san yana da zafin zuciya irin na yau ba, ga shi wurin da aka yi masa dressing ya buɗe yana zubar da jini. Likitan da ta duba Deenin ce ta gan shi a haka ta fara faɗa ko kallan inda take be yi ba, haka ta zo ta sake gyara masa wajen ta na ta masa faɗa, shide nasa ido be tanka mata ba.

Likitan ne ya fito ya kalle su ɗaya bayan ɗaya, kafin yace, "Mun yi ƙoƙarin cetan ran ta, sai de kuma babu tabbacin ko zata iya magana ko ba zata iya magana ba, amma a gaskiyar magana ita ce, ba lalle ta iya magana ba. Kuyi haƙuri".

Daga haka ya wuce suka bishi da ido kawai. Deeni sai sake kwantar da shi aka yi san sosai jikin sa ya rikice ya kasa ɗaukar wannan abun da yake ji a ran sa.

Duka matan na zaune tun zuwan Safiyya ta sanar da su komai,  sosai hankalin su ya tashi sosai shi kan sa Baba hankalin sa ne ya tashi sosai sai da ya shiga ɗaki ya zubar da ƙwalla yana yi masa fatan shiriya. Ya kuma tabbatar da cewar ƙaddarar su ce ta zo a haka dole su riƙe hannu bibbiyu.

Ganin har dare ya tsala ba su dawo ba yasa suka fara kiran su, amma basa ɗagawa dan a silent suka sa wayar ta su saboda irin haka, Hafsah ce ta ɗaga musu hankali hakan yasa aka kai ta domin kuka ta ringa yi musu kan dole aka kai ta. Ɗakin da yake aka kai ta kafin aka haɗa su Noor ɗin da Baban ta a ɗaki ɗaya. Idan ta kalli wannan sai ta kalli wannan.

********Hafiz kam suna can aka kai shi wani irin waje, yayin da Major Kabir ya kalli A. Madaki.

"Yarinyar da ta haɗu da kai a yau, da safe har ta baka kuɗi ka amsa. Ba kowa bace sai ƴar da ka haifa".

Wani irin waro ido A. Madaki yayi cike da mamaki yana sake tuno fuskar yarinyar, tabbas anyi haka amma meyasa?

"Kai a tunanin ka kuma dan ka ce su baka sai su kwashi komai su baka? Ka manta da ko su ɗin su waye? Ka sace ƴar su ka ɓoye a inda suke da tabbacin hankalin su ba zai taɓa kawowa ba?

Sai Major Kabir yayi murmushi.

Yace, "So nake ka koyi rayuwa, domin idan na kulle ka komu jima, ko mu daɗe zaka fito, idan ka fito kuma banda tabbacin cewar zaka sauya halin ka. Amma kasan me Deeeni yace ?

Sai yayi murmushi ƙwalla na cika masa ido.

Yace, "A rabu da kai, ka je duk inda zaka je, ka cutar da duk wanda zaka cutar, burin sa da fatan sa be wuce wata rana ka zo ka ce Fodiyo kayi hakuri ba. Wannan ne kawai burin sa. Mamman bansan wanne irin hali da zuciya da kuma ɗabi'a ce kake da ita ba, wacce ka kasa sauyata ba a wannan takwas, amma Mamman ina so ka sani da cewar su mutane ba kowa ne zai baka damar da su Baba da Daada suka baka ba, Domin su ɗin suna san ka ne, shi yasa suka baka wannan damar har aka yi amfani da ita ka cimma nufin ka".

"Kamar de yarda yau ka fara mafarkin samun ingantacciyar rayuwa batare da ka yi tunanin hakan zata faru ba".

Sai Major Kabir yayi murmushi kawai yana kallan A. Madaki. Sannan ya tashi ya bashi waje. Yayin da A. Madaki yake jin wani irin wuta na ci da zuciyar sa, kwata kwata ji yayi ƙirjin sa ya toshe, tabbas kam, yayi tunanin cewar yaran nan dagaske suke masa, musamman da ya ji Deeni yace su basa cuta, kenan shine macuci? Basa yaudara? Shine mayaudarin kenan?

"Innalillah wa'inna ilaihirraji'un".

Ya faɗa yana kaɗa kan sa sama, tabbas yayi kuskure amma a yanzu idan ya gudu zai dawo gare su domin shifa sai ya sa ka a halin da suka jefa shi, suka jefa rayuwar ɗan sa cikin shaye shaye, dole ne sai sun yi nadamar abinda suka aika ta masa. Babu fashin wannan abun. Tashi yayi yana kallan inda Deeni ya caka masa wuƙar nan ta shige aka gyara masa wurin, da cirewa zai yi sai kuma ya rantse idan sa yana jin azabar zafi a wajen. Kafin ya gama zagaye inda yake tas ya nemo hanyar guduwa. Dan ɗakin wani waje ne, window ɗaya ne kawai shima acan sama, murmushi yayi yana saka table ɗin dake wajen yadda zai iya hawa da kyau ya gudu. Batare da yasan duk abinda yake yi ɗin ba suna kallan su, kawai murmushi A. Madaki yayi shi da Hafiz.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now