52

25 1 0
                                    

52.

******Kowa kallan na kusa da shi yake suna mamakin wannan lamarin, yayin da A. Madaki gaban sa yake wani irin dukan ɗari ɗari, lokaci guda zufa ta keto masa, inda Mu'azzam da yace ba zai yafe dukiyar sa ba, da tasa da ta ɗan uwan sa sannan kuma da ta Mahaifiyar sa da ya haɗa dole sai an biya shi, dan ada be yi tunanin ya karɓa ba, amma a yanzu kam dole ne ya karɓa. Yayin da mutane suka fara ehh ya kamata a ba shi dukiyar sa. Sannan a kulle shi.

Sai da aka nutsa sannan Alƙali yace, "A bisa wannan kotun, da kuma jin ƙorafe ƙorafen mutane akan wanda ya shigar da ƙara wato Alhaji Mamman wanda aka fi sani da A. Madaki. A bisa bincike da hujjoji wannan bawan Allah zai bawa mutanen su kuɗin su, za'a zauna a ƙiyasta iya kuɗin su a lokacin da, da kuma a yanzu, zai ba su kudin duk wanda ya zalunta. Kotu ta yanke masa shekara biyar a gidan yari domin aikatawa miyagun laifukan da ya ringa yi yana zaluntar al'umma".

Nan fa aka fara cece ku ce a tsakanin mutane, yayin da aka fito da A. Madaki hannu bibbiyu da handcuff, ƴan jarida sun samu a abun yi sai nuno shi ake yi, be iya ɗaukan wannan abun ba, kawai ya yake jiki zai faɗi ƴan sanda nan suka taro shi. Aka wuce da shi asibiti akan gadon asibitin yana farfaɗowa aka ƙwace komai nasa batare da anji tausayin sa ba haka aka raba shi da duk wata kadarar sa. Aka raba yayin da kowa ya zuba a Foundation ɗin Ɗalhat, wani kuma aka bawa marayu. Ɗalhat yayi kuka sosai kamar ran sa zai fita, domin har yau har gobe Daad baban sa ne, yana kuma san sa a yadda yake, amma halin sa ne baya so, zalunci ne ya riga da yayi a asibitin kasa haɗa ido yayi da shi yana kallan sa daga bakin ƙofa suna magana da Daada da kuma Baba. Sai kawai ya fice ya bar wajen. Ya tafi can harabar asibitin yana zubar da kuka. Jin an zauna a kusa da shi ne yasa shi ɗagowa yana kallan Deeni.

Wani irin Murmushi Deeni yayi masa mai zallar kyau da annuri a cikin sa, mai saka zuciya ta sami natsuwa gami da jin salama a cikin ta. Murmushin da yake tafiya da dukkan wata damuwar da mutum yake tattare da ita. Hawaye ya goge masa cike da kulawa kamar wani ƙaramin yaro.

"Yara suyi kuka, muna manya muyi kuka? Kar ka manta mun girma fa".

Ya faɗa cike da lallashi. Murmushin takaici Ɗalhat yayi.

Yace, "Kasan yarda nake ji a rai na?

Sai yayi ɗan murmushi kaɗan.

Yace, "Yaya Deeni shekara ta Ashirin da takwas, shekara huɗu ne kawai ban yi tare da Daad ba. Wannan shekara ashirin da huɗun da nayi tare da shi, mahaifi na ɗauke shi. Ban taɓa masa kallan ba mahaifi ba har sanda na baro gida. Fata nake masa ya gyaru amma kwa fa?

Sai ya sake wani murmushin daga ƙirjin da hawaye na zubo masa.

Yace, "Mata nawa ya aura? Shin yana da yara a tare da shi ko a'a? Mata nawa ne wanda ya zalunta irin Umman Hashim da Antyn Sakeenah? Shin su biyu ne? Ko kuwa da wasu?

Murmushi mai kyau Deeni yayi masa yana kallan sa, tare da dafa.

Yace, "Ɗalhat kayi haƙuri, komai zai wuce Dad ɗin ka rayuwa zai gani ba komai ba. Ba zai zauna a asibitin nan ba, domin ba zai je gidan yari ba, kaga duk wannan tsaron, zai gudu ya tafi wani waje yayi rayuwa a ɓoye da shi da ahalin sa. Dole watan watarana zamu haɗu idan har ba mu mutu ba, ko shi be mutu ba. Idan bamu haɗu ba Ɗalhat zai zo wajen da kake ko muke. Domin neman afuwa, da gafarar mutane. Wanda ita kawai muke jira. Daga nan sai mu bayar masa da dukkan dukiyar sa, wacce zata dawo tsaftacciya halalliya mai kyau".

Murmushi Ɗalhat yayi wanda ya fito daga ƙasan zuciyarsa.

Yace, "Kana tunanin Anty zata bari ka bashi dukiya?

Sai ya sake wani murmushin.

Yace, "Kasan ba yarda ba'a yi da ita ba yau akan ta taho mu tafi? Baba da kan sa yaje yace an sayi ticket har ita ta fito mu tafi, amma tace ita idan taga A. Madaki zata iya marin sa tsabar yarda take jin haushin sa. Dan haka ita ba zata je ba. Wata irin tsana tayi masa da ko kallan sa muke sai kaga ta tashi ta kashe mana TVn ko tayi tsaki ta tashi ta wuce, ko dariya take da ka ambaci sunan Dad zata haɗe rai. Haka shima Ameer a cikin su banga wanda zai goya maka baya ba, banda Ameerah da Zarah bansani ba ko Sadiq".

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now