2

44 2 0
                                    

✨ *ZAHARADDEEN* ✨

   
                        2.

                       

A kusan tare suka fito shi da ita, suka nufo table ɗin da suke cin abinci, kujera yaja ya zauna itama ta ja ta zauna kusa dashi, rasa abinda zai ci yayi shi, baya san cin wasu abubuwan dan besan da me aka yi ba. Sorrel soup wanda aka yi da, sorrel leaves, potatoes, carrots, parsley da ƙwai ya zuba ya fara sha a hankali. Ita kuma ta zuba Ukha da aka yi da kifi daban daban, saura ƙiris yayi mata magana sai kuma yayi shiru tuna wacece ita ɗin. Sai dai wani da yake ta kallan ta tun shigar su meeting lura da hakan da tayi ne yasa ta haɗe fuska ta fara gunguni, kallan ta yayi yaga yarda tayi wani haɗe rai tana cune baki. Shi wallahi dariya take bashi idan tana masifar nan ta ta,  baya idan ta haɗe fuska tana cune baki. Haɗa idan da suka yi ne yasa ta galla masa harara tana kau da kan ta, shima janye idan nasa yayi batare da ya ce komai ba daman ba ya da abin faɗa.

******Koda aka koma meeting ɗin komai ya tafi yarda ake so, shine ya wakilci Companyn su ita kuma ta wakilci Baban ta a ƙarƙashin Company ɗin. Kasancewar ita da shi duk Company ɗaya ne kuma abu ɗaya suka zo nema hakan yasa  aka basu aiki tare su biyu meeting ɗin da za'ayi ranar ƙarshe, ɗaya daga cikin su zai gabatar da presentation haka aka yi aka gama.

Duk da tasan da cewar ƙasa ɗaya suka fito sam bata san da cewar baya jin Hausa ba, a ganin ta idan wani ne ai zai yi mata magana yace yana jin ta, shiyasa ko ta kan sa bata bi ba ana tashi kawai fitowa tayi, toilet ta koma domin ta manta agogon ta da tayi alwala tana duba wayar ta dake cikin jaka da ta ji vibration, sam bata lura da mutum ba ta buge shi, da sauri ta ɗago ta kalle shi wannan mutumin de da ya addabeta da kallo. Dogo ne gashi fari yana ji da kyan sa da kuma samartakar sa, gashi yana ji da kuɗin sa.

"Nigeria ko?

Ya faɗa yana wani mata murmushin sa iyakar gaskiyar sa, irin kin fa burge ni ɗin nan. Sai da ta kuma haɗe rai fuska ta mau.

"Sorry".

Kawai tace tana raɓa shi ta wuce  lokacin ta ɗauko wayar da ta katse, babu zato babu tsammani ta ji y ruƙo hannun ta yana dawo da ita gaban sa, kamar walƙiya shi kuma yaji wani irin abu mai shegen zafi da zugi ya ratsa fuskar sa ya zauna. Kulle ido kawai yayi tsabar yarda yake jin kan sa na wani iri juyawa, be gama ba daga wannan marin da ta masa yaji.

Tace, "Allah yasa yanzu zaka gane mutane daban daban ne a duniya ko?

Daga haka ta wuce shi ta barshi tana jan tsaki. Har taje ta dauko abinda zata ɗauko yana tsaye. Tunda yake a rayuwar sa babu wanda ya taɓa hannu ya wanka masa mari koda kuwa iyayen sa ne, abinda kuma ya ga damar yi shi yake yi, wacece ita da zata ɗauki hannu ta mare shi? Ta kuwa san waye shi? Tasan matsayin sa kuwa? Shi da yake da kuɗin da yake ganin zai iya siye Nigeria da abinda ke cikin ta? Wacece ita ? tambayar da ya yi wa kan sa kenan yana shafa wajen da ta mare shi, a lokacin kuma ta zo zata wuce shi yasa hannu ya ficiko Hijabin ta saura ƙiris ta faɗo masa ya ɗaga hannu zai zabge ta da mari, karaf yaji an riƙe hannun, ita kuwa idan ta ƙuri akan sa taga yau wanenen zai mare ta ya taɓowa kan sa bala'i da masifa.

"Kayi haƙuri. Su mata rauni ne da su be dace ace ka mare ta ba".

"Kai kuma waye? Yayan ta ne? Ko kuma shishshigi?

"Ni waye bashi ne mai muhimmanci ba, muhammacin shine kayi haƙuri kada ka mare ta".

'ya ilahi' ta ji ta faɗa a zuciyar ta, tunda take a rayuwar ta wannan shine karon farko da ta taɓa jin kunya a rayuwar ta, zata ita iya cewa bata taɓa shiga yanayin na jin kunya ba sai yau, ashe duk abinda take masa yana ji. Shi kuwa wannan waye? Ga shi muryar sa mai taushi da daɗi gami da wata irin nutsuwa da tafiya da ruhi harda imanin mutun ma tsaf zata iya tafiya ( ace warta 😂) da  da yake presenting ta ɗauka iyaye ni be kuma burge ta ba kamar a yanzu da yayi yaren sa mai cike da tafiya da imani, lumshe idan ta tayi ta buɗe akan sa. Kafin ta wani ƙara ɗinke fuska tana shan mur.  Kallan ta yayi.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now