21

18 1 0
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                     21.

******Da wani mamaki take kallan sa, gani kawai take kamar de an sauya mata mijin nata, ba wanda ta saba gani ne ba. Ɗan tashi tayi ita bata tashi zaune ba, ita kuma bata kwanta ba.

Tace, "Store fa?

"Kin ƙarfin ki koma store ɗin ne?

Samun kan ta tayi tashi zaune kawai ta zuba masa duka idan ta, tayi tagumi jugum da ita. Ta ma rasa me zata ce masa tsabar mamakin da ya kasa barin kan ta. Zuwa yayi ya kwanta a ɗayan side ɗin.

Yace, "Kinga Hajiya ko ki tashi ta sauƙi ko kuma nasa ƙafa na turo ki".

"Ni jikina ma ba zai iya taɓa naki ba gaskiya, dan tsantsani kike bani tashi dan Allah".

Ya faɗa yana juya mata baya. Iya ƙuluwa ta ƙulu kawai ta tashi tana ɗaukan pillow ta koma kan kujera zata a sukwane ya tashi yana mata magana irin da saurin nan da zan tsorata mutum.

"Kar ki zauna, kar ki zauna".

Cak ta tsaya tana kallan shi.

"Eh kar ki zauna, saboda kada ki ɓata min kujera ko ta ki ce?

Ya kuma haɗe rai kamar ba shi ba. Ya kwanta ya rufe ido.

Yace, "Idan baza ki kwanta ba, ki kashe min fitila ni bacci zan yi. Ki fita store ki je ki kwanta".

Haka ta juya jiki a sanyaye ta kashe wutar ta sami waje ta zauna a ƙasan tiles, kawai ta tagumi tana kallan sa.

"Anya shine kuwa?

"Ko kuma anya kece kuwa?

Sai ta girgiza kan ta kawai ta tashi cike da fushi ta matso inda yake shi kuwa har ya fara ɗan baccin sa.

"Malam tashi ba zai iyuwa ba wallahi ni ba bora ba kace na kwanta a ƙasa".

"Ni bance ki kwanta a ƙasa ba ko nace Hajiye kwanta a ƙasa?

"Ni ka dena cemin Hajiye bana san iyayi".

"To Hafsah".

"Ni sunan ne bansan ka kira".

Ta faɗa tana cune fuska, ji take kamar ta shaƙe shi kawai take ji.

"To kuma de meye ni bance ki kwanta a ƙasa ba. Dan haka ga hanya nan".

Ya faɗa yana nuna mata ƙofa. Hararar sa tayi.tace, "Kujerar ma ba hanani kwanciya kayi ba?

"Wannan kuma zaɓi ya rage naki. Amma kar ki hau min kujera. Tunda baccin dole ki shimfiɗa daddumar ki, ki kwanta akai, ki kin ɓata wannan taki ce. Amma ni kazanta ce bana so".

Rungume pilllown tayi, ta ƙara haɗe rai. Tace, "Wai ance maka haihuwa nayi ne ko tsiyaya nake ?

"To waya sani ne?

Ya faɗa yana juya mata baya, zatayi magana.

Yace, "Wallahi tallahi kada ki dame ni kada ki kuskura na faɗa maki. Kar na ɗauki mataki ki ce ban faɗa maki ba".

A harzuƙe tace, "Duka na zaka yi?

"Kusan hakan".

Hararan sa tayi ta jefa masa pillown ta bar masa ɗakin, da ido kwai ya bita yana murmushi ƙasan ran sa.

"Masifatu yanzu aka fara muga waye zai ci riba".

Ya faɗa yana rufe idan sa. Yayin da ita kuma ta fita, ta shiga Kitchen gaba ɗaya yayi wanke wanke, ya gyara gidan tas ko ina ƙalƙal. Ragowar abincin ta gani ya ajje ta haɗa shayi ta zauna ta ci abinta tas sannan ta dawo parlour ta zauna. Tana zama ta ji inji ya mutu ga bata jona wayar ta ba da system ɗin ta bata da tabbacin idan tablet ɗin tana da charge, dafe kai tayi cike da takaici kafin ta ɗan samu waje ta ɗan kwanta, zuwa ƙarfe bakwai. Ameer ya fito daga ɗaki yagan ta a kwance anan.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now