54

21 1 0
                                    

          ✨✨ZAHARADDEEN ✨✨        



          54

ASSALAMUALAIKUM WARAHAMATULLAH: FATAN MUN YI IBADA LAFIYA MUN YI SALLAH LAFIYA. UBANGIJI ALLAH YA AMSA MANA. ALLAH YA KARƁI IBADUNMU. YA YAFE MANA. ƳAN UWAN MU DA SUKA RASU ALLAH YA JIKANSU ALLAH YA GAFARTA MUSU YASA ƘARSHEN WAHALAR KENAN.  IDAN TA MU TA ZO ALLAH YASA MU CIKA DA KYAU DA IMANI. AMEEEN. 🙏.






********Suna zaune Major Kabir ya kira waya yace be samu Ameer ba su zo su ɗauki ƴar su ba zata hana su bacci yarinya ace sai an rungume ta zata yi bacci. yana kashewa kuwa suka fara mita. Deeeni ne yace su zauna zai je ya ɗauko ta.

Taufiq yace, "Yaya Deeni zaka gane hanya kuma?

Murmushi ya masa yace, "Ban yarda da driving ɗin ka ba, ɗazu kawai shahada nayi na shiga. Kar ka je ka zubar min da yarinya ta".

Sakar baki Taufiq yayi yana kallan Deeni.

Sadiq yace, "Yaya ba kara haka?

"Bansan ta ba".

Shiru duk suka masa sannan aka bashi key ɗin mota. Ya je ya ɗauko ƴar sa ya rungume ta a haka tayi baccin kafin su zo, ya tsaya ya siyo musu kayan ƙwalam dan yasan ba suyi bacci ba yaran nan. Ga rashin bacci da wuri ga tashi da wuri haka suke. Suna nan a zaune kuwa Hafiz ya gani a balcony yana zaune shi kaɗai da'alama Deenin yake jira.

"Hafiz lafiya?

"Zauna".

Ba musu Deeni ya zauna yana nazarin sa. Shi kuma ya kalli yarinyar hannun sa.

Yace, "Gaba ɗaya tabi ta shagwaɓa yarinya, daga ita san Zarah ke iyawa da wannan halin nata".

Murmushi Deeni yayi yana sake shafa kan ƴar sa da yake jin wata irin soyayyar ta a yarda yake ji baya ji ko tasa ya haifa zai so ta haka, ita ɗin kasance kyauta ce aka masa sannan ta fito daga tsatson ahalin Baba wanda yake jin zai iya sadaukar da komai ganin cewar sun samu rayuwar su tayi kyau.

"Ka san Umar Babandi?

Murmushi yayi yana ya ɗaga kan sa alamar wani abu ya faru kenan..

"A. Madaki ya gudu fa, bayan tafiyar aka yi gaggawar sanarwa".

"Tun yamma ya gudu, sun nemi shi ba rasa ba shi yasa suka ce a yanzu ya gudu kada a ga laifin su".

Taɓe baki Hafiz yayi alamar shi ya sano.

"Me yayi Umar ɗin?

"Mai gadin gidan nan shi yake yiwa aiki".

Da mamaki akan fuskar Deeni yace, "Shi kuma?

"Shifa, kuma yace shi kuma be san wanda yake yiwa aikin ba, wannan kawai ya sani".

Girgiza kan sa Deeni yayi yace, "Kenana shi yana aiki a tare da A. Madaki kenan?

"Kasan aikin da na koma Turkmenistan na gano shi a ɗaya daga cikin manyan ƴan tawagar da suke shigo da miyagun kaya?

"To me muke jira?

"Evidences".

"Babu?

Hafiz wani irin murmushi yayi na takaici yace, "Wannan aikin fita zan yi da shi Deeni, na gaji da yiwa mutane aiki ana samun matsala, ace duk wata shaida idan muka samu sai min ga na sama da mu sun yi ƙoƙari sun kawo mana cikas a cikin ta? Haka ake yi? To ni gaji".

Shiru Deeni yayi yana kallam Hafiz.

Yace, "Ba fita zamuyi ba, haɗa tawagar mu zamuyi yarda babu wani mahaluƙin da zai kawo mana cikas, ba za su san muna wannan aikin ba, amma idan muka ce zamu fita kasan wannan shima wani case ne na daban ko?

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now