47

34 0 0
                                    

47


********Numfasawa tayi tana kallan Noor da bacci ke san ɗaukar ta, kafin ta kalli interviewer ɗin ta saki ƙayattaccen murmushin da ya fito daga ƙasan zuciyar ta.

Da farko zamu zo mu ji sunan ki, da inda kika ta so, inda kika fara rayuwa makarantar ki da komai naki har inda kika haife ki"......

Tace, "Sunana Hafsah Uthman, an haife ni a garin Katsina, na fara rayuwa acan, daga baya muka dawo garin Kano. Lokacin ina da shekara biyar muka dawo, anan na yi makaranta kafin daga baya muka koma Abuja......

Ta basu ɗan tahirin su.

"Me ya dawo da ku Kano, bayan kince kin koma Abuja?

"Kamar yarda aiki ya ɗauke mu ya Baban mu aiki, to wannan aikin ne ya sake dawo damu garin Kano".

"Kamar ya kenan?

"Idan mutum yayi retire ba gida yake dawowa ba?

Sai tayi murmushi, itama Hafsah murmushin tayi.

"Ance A. Madaki, ɗan uwan ku, a shekarun baya videos sun yi ta trending, har ama akace shine ya kori Mahaifin ku daga aiki haka ne?

"Ehh kawun mu, amma batun kora a aiki, bansani ba, Videos ɗin ma da yayi ya trending ɗin bamma gan shi ba. Balle naga me ya faru".

Jinjina kai tayi interviewer ɗin cike da gamsuwa. Haka ta ringa tambayoyi tana bata amsa, amma ko da wasa bata ɓata A. Madaki a inda duniya ba, domin tasan idan mutane duka suna kan ta, da zaran tace wani abu shikenan ya zauna. Haka aka yi mata tambayoyi yarda suka fara kasuwancin nasu da nasarar da suka samu da kuma irin ƙalubalen da suke fuskanta da kuma wanda suka fuskanta.

"A dawo maganar Zaharaddeen, kuna da alaƙa da shi?

Girgiza kan ta tayi.

Tace, "Ko kusa, bamu da alaƙa da su, hasalima ba su san mu bamu san su ba".

"Aurene ya haɗa ku?

Sake girgiza kan ta tayi kafin tace.

"Farko maƙwabtaka ce ta fara haɗa mu da su, da Abban sa da Baban mu. Daga nan sai abota. Wannan abotar da kuma makwabtakar ita ce ta haɗa mu ta kawo wannan matakin.  A sanda iyayen su suka rasu mahaifin mu shine ya kula da su, muma kuma a sanda muka rasa komai na mu shine ya kula da mu".

"Shi wa kenan?

Hararan ta tayi tana basarwa, itama daman ta faɗa ne da wasa wanda kowa ɗan darawa a wajen, domin kowa yasan mijin ta take nufi.

"Abota da maƙwabtaka wasu abubuwa ne da suke da alaƙa, wanda tunda can sanda muna yara bakowa ne yake iya riƙe wannan hakki da kuma amanar ba. Ko yanzu da muke ciki, wani abokin ya fi wani ɗan uwa, nesa ba kusa ba. Ɗan uwan ka, kan iya mutuwa ka rasa shi, ko ya ji wani ciwo, amma ba zaka ji zafi sosai ba. Ba zaka kuma kake tunawa dashi ba, muddin ba wani abu ne ya faru, amma abokin dake kusa da kai zaka tuna shi a kullum, a kuma ko da yaushe. Mahaifin su, mutumin kirki ne, baya da faɗa, baya da hayaniya be da tashin hankali komai ka ce masa zai ce eh. Harta musu baya yi. Yana da gaskiya halin sa ne ya haɗu da Baban mu shiyasa abotar su take har yau. Batare da tayi targarɗa ba".

Kowa shiru yayi, domin kuwa maganar ta baƙaramin tasiri tayiwa da yawa daga cikin su, aka ringa mamakin irin wannan abun, shi kan sa Ɗalhat jin wai abota ce tsakanin wannan mutanen guda biyu abin baƙaramin girgiza shi yayi ba domin be taɓa sani ba, haka ma Mu'azzam idan har abota ce ta kasancen suka riƙe amana suka zama abu ɗaya wanda a yanzu duk wanda ya kalle su yasan ba iya abota ce sun zama ahali guda ma'ana sun zama abu guda ɗaya tal. Da baza'a iya rabawa ba. Muddin kace zaka raba to kai ne wanda zaka rabe. Yayin da gefe ɗaya na zuciyarsa ke hasko masa A. Madaki, wanda ya cuci mutane da yawa, ya kuma cuci abotar dake tsakanin sa da Daada, ina zai kai wannan hakkin? Ji yayi wani irin ruwan hawayen na zubo masa yayi sauri ya sa hannu goge, yayin da Ameerah ta kalle shi tasan me yake yiwa kuka, har yau har gobe yana son Daad ɗin sa domin shine ya tashi ya buɗe ido a gaban sa, wannan soyayyar ya mahaifi yake masa, baya taba masa fatan ya salwanta a kullum addu'ar sa Allah yasa Daa ya gane hanyar gaskiya.

Tissue ta miƙa masa ya karɓa ya kalle ta sai yayi murmushi hawayen na zubo masa, ita ce ta goge masa tana girgiza masa kai alamar a'a.

"Auren soyayya kuka yi tare da shi?

Bata san ya akayi ba sai ji tayi ta saki wani ƙayattaccen murmushi lokaci guda kuma ƙwalla na cika mata ido, domin duk maganar da aka ambaci sunan sa sai ta ji gaban ta ya faɗi. Kasa riƙewa tayi kawai hawaye ya zubo mata.


********  Turkmenistan: Ashgabat

Yana zaune a gaban TVn tun sanda suka sauko daga mota, aka fara nuna su dake Taufiq ne ya fara ɗauka sai da suka shiga sannan ya sami waje ya zauna. Idan sa akan komai har abinda Ameer da Zarah ke yi duk ya ga ni, da sanda aka nuno masa ƴar sa na gudu da kuma aka hasko kowa dake ahalin sa akan idan sa hakan ta faru. Banda murmushi babu abinda yake yi shi kaɗai kamar wani sabon kamu. Ƙasan ran sa kuma wani irin kewar su ke addabar sa, lokacin ya kwasa ya yi, lokacin da da ya kamata ya kammala duk wasu abubuwan sa yayi.

Tsawon shekaru huɗun nan yayi nesa da su ne saboda ya muddin yana tare da su ba zai samu ya cimma abinda ake so, idan har ana ganin sa. Amma da babu shi, su kan su sun fi tsayawa su yi aiki da kyau. Duk kan shekarun nan yayi ne yana bibiyar duk wani shafin Taufiq dake ɗaura duk hotunan su scene baya scene. Yana jin irin taru ficen da suka yi a Nigeria da kuma ƙasashe dake maƙwabataka da Nigeria.

Tambayar da aka yi mata ne yasa shi sake gyara zaman sa yana kafe mata da idan sa yana jin wani irin a ran sa wanda ba zai iya fisulta meye yake ji ɗin ba. Murmushi ya sake saki ganin har yanzu bata amsa musu tambayar tana ta ƙoƙarin mayar da ƙwallar idan ta, amma kuma hawayen ya zubo.

"Babana ne ya bashi ni".

Ya ji ta faɗa, be san sanda ya saki ƙaramar dariya ba, wannan matar ko. Har yau ba zata sauya hali ba.

"Meye ba zaki manta da shi ba?

"Abu biyu".

"Wanne da wanne?

Sosai wannan karon hawaye ya zubo a idan ta.

Tace, "Na farko be ce irin cin amanar da aka yi mana ba, sai de ta hakan wani Alkhairi ne ya tunkaro mu, domin da ba'a ci amanar mu da bamu kawo irin wannan matakin da muke ciki ba, cin amanar da ta sa mahaifin mu a wani hali".

"Na biyun fa?

"Sirri ne".

Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi domin ta gaji da amsa irin wannan tambayar. Tana gaf da sakin kuka. Ganin haka yasa interviewern cewa.

"Me ya ake kiran ki da Hafsah Bala".

Cak ta tsaya hawayen nata ma tsayawa yayi tare da barin ƙoƙarin ɗaukar Noor da tayi bacci. Sai kuma wani murmushin ya ƙwace mata na ba zata.

"Meyasa kuma bayan kince mana sunan ki Hafsah Uthman?

Dariya dariya tayi.

Tace, "Kina so na shaidawa Duniya saboda ina da ni masifaffiya ce yasa ake kira na da Hafsah Bala'i? S

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now