5

41 1 0
                                    

✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

                    5





*****"Tsakani da Allah waye ya shanye mana abinda muka yi? Mutum ɗaya de ba zai iya ɗaukan wannan abun ba shi kaɗai ko?

Faɗin Taufiq yana ɗauko bowl ɗin da suka zuba abin su.

Ameerah tace, "To nide bansan waye ya kai su Ɗalhat ba, amma Ɗalhat da ya sha yace na zuba masa ya tafi da ita haka aka yi".

Ummu tace, "Ko tantama bana yi Sabir ne".

Sabir yayi sauri yace, "Ni me nayi?

"Kai ne ka bada alawar mu mana, munafuki".

Ummu ta faɗa, Taufiq yace, "Munafuki kawai".

"Yaya Taufiq nine munafukin?

Ya faɗa looking so innocent and calm, kamar ba shi ɗin ne ya aikata ba.

"Da wani bayan kai?

Ya bashi amsa yana kallan sa kamar ya buge shi haka yake ji. Haka itama Ummu daman su ne suka yi abin su, irin abin nan na kayi timing abinka zaka sha yace ɗauke ni inda aka ajje.

"Nifa bani bane ba. Ina ruwana da abin ku kuma sai na faɗawa Anty".

Ya faɗa yana tashi zai wuce alamar sai fa ya faɗa ɗin nan.

"Ka jima baka faɗa ba".

Suka haɗa baki wajen faɗa san ya ƙular da su ba kaɗan.

"Kuma Yaya Ameerah kika juye masa duka?

"To kar yace na yi masa rowa shiyasa na zuba".

Hafiz ne ya kalle su ya girgiza kan sa, ya rasa yaushe yaran nan za su girma su dena shirme, mene dan an ɗauki Abu an bayar ba sai a sake wani ba?

"Taufiq kuyi hakuri kuje ku sake wani idan madarar ce babu aje a siyo mana".

"Yaya? A sake fa ka ce?

Ummu ta faɗa.

Ameerah tace, "Kasan da ya aka yi?

Taufiq yace, "To wallahi Yaya daƙyar muka yi kowa san jiki ya ishe shi".

"Uhm".

Kawai yace musu yana ɗaukan system ɗin sa ya shiga ɗaki dan ba zai iya da wannan hayaniyar ta su ba. Hajiya kuwa ko ƙala ba ta ce musu ba dan ta gaji hidimar biki suka je suka yi na wata maƙocin su tsohuwa irin ta ta gayyace ta wai bikin jikar ta. Sai da ta ji sun yi shiru kowa na muzurai.

Tace, "Ke kira min waccan yarinyar mai baƙin rai tsiya".

Ta faɗa tana kallan Ummu, tashi tayi ta wuce sama taje ta kira ta ta dawo.

"Kuma kije ki gyara mana gado da kuka je ku kayi sukuwa akai".

"Yau ba wanda ya shiga ɗakin ki fa".

"Shi yasa naga anyi sukuwar doki akan sa".

Haka ta kuma tashi ta shiga ɗakin nata dake ƙasa tasan kuma ba wanda zai yi sai Sabir bata san wanne irin reni Sabir yayi musu ba ita da Taufiq.

"Hajiya gani".

Hafsat ta faɗa tana tsayuwa.

"Kai na zaki hau, sai ki nuna min kin iso".

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallan Hajiya, kallan irin ba kula ki ba zan yi. Ta nemi waje ta zauna kusa da ita akan kujera daga wajen ƙafar, dake a doguwar kujera take sai ta kishingiɗa ta ɗaura hannun ta a hannun kujerar.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now