44

24 1 0
                                    

44

*******"Wani iri kallo ne yake masa mai wuyar fassara, dan kuwa yasan soja da police ba wasa ba, shi al'umma yake yiwa aiki yayin da shi kuma soja ƙasa ce gaba ɗaya yake yiwa aiki, yana da iko da mutanen dake cikin ta idan har an bashi damar yin haka cikin kuwa harda shi, tunda kariya ce yake bawa ƙasar sa. Kuma duk a cikin gyara ƙasa ce ne idan aka gyara gurɓatattun ƴan sanda irin wannan mutumin dake tsaye a gaban Major Kabir.

"Muje ka ɗauko min yaro na".

Cewar sa yana yin gaba bayan ya bada umarnin a rufe motar su tafi. Jiki a sanyaye suka tafi sai de fa ya sa inda zasu je dole office ɗin na su aka je, aka gan shi alamar anyi gobara.

"Taya za'ayi ka kawo mu nan wajen?

"Anan muka ajje shi".

Jinjina kai kawai yayi bece da shi komai ba, suka sake shiga mota be zarce da shi ko ina ba sai militaryn su, tashin hankali ya fara shi tun ba'a je ko ina ba. Irin yarda ya ganawa Nadiya azaba shima haka ya gana masa sannan ya sanar da shi gaskiya.

Murmushi kawai Major Kabir yayi ya haɗa su y rufe sannan ya fito, yana fitowa ya wuce asibiti dukan su suna zaune suna kallan maimaicin labaran da ake akan wannan videon na A. Madaki da Hafsah, ana gamawa kuma aka sako na cewar "an kama wannan sabon ɗan kasuwar da ya fara yin tashe a kwanan, sannan gobara ta tashi a cikin station ɗin, an kasa cetan ran sa duk wanda yake ciki yayin da su kuma ƴan sanda suka ceci ran su babu wanda ya rasa ransa a cikin su, idan har bada manufa aka yi haka ba to waye? Ya jefa wannan iyalan wannan mutumin a cikin halin ko in kula yanzu haka matar sa tana asibiti saboda irin abinda ya aikata".

Kallan kallo suka fara yi a junan su wannan ya kalli wannan,wannan ya kalli wannan, yayin da Hafsah kawai hawaye ne yake zuba a idan ta, Noor dake kwance a kusa da ita kawai ta zubawa ido, haka kawai take ganin kamar ya tafi ya barta da yarinyar da bata san ta zata fara bata kulawa ita kaɗai ba. Gani take meyasa zai tafi ya barta a lokacin da ta fara sanin meye rayuwa? Me yasa zai yi mata haka? Yana ina? Ina ya tafi? Shin dagaske ya ƙone ɗin? Ko kuwa be ƙone ba?

"Yanzu Yaya Deeni Shikenan?

Ameer ya faɗa yana kallon Hafiz dake zaune har yanzu ya zubawa TV ido be ɗauke ba, sai yake ji kamar ba daidai kunnen sa ya ke jiye masa. Da waya ce ma su kunna labaran da wannan safen?

Babu wanda ya lura da Major Kabir sai da yayi magana, suka gaida shi yake tambayar su mai jiki.

"A'ina videon nan ya fito?

Major Kabir ya tambaya yana kallon Hafsah. Tashi zaune tayi tana goge hawayen ta,  girgiza kan ta yi alamar bata sani ba, wani hawayen na sake zubo mata tasa hannu ta share.

Ɗalhat ne ya zo don ya sanar da su abinda ke faruwa kada su je hankalin su ya tashi, yana zuwa kuwa yaga halin da suke ciki, daki-daki ya sanar da su duk abinda ya faru.

"Amma yanzu bansan inda yake ba, naje na kai masa abinci naga baya nan, ya ajje min note cewar A. Madaki zai zo neman sa, zai yi nesa da mu domin gudun jefa ku a wani hali, gwara ce shi yayi nesa da mu zai kawo karshen A. Madaki batare da kowa ya farga da hakan ba".

Ya faɗa yana miƙawa Major Kabir papern, shima Hafiz ya miƙawa shi kuma ya miƙawa Hafsah, kawai tsayawa tayi tana kallon papern da hannun nasa da yake miƙo mata, babu abinda ta ji sai wani irin malolon takaici da ya zo ya maƙale mata a wuya, da ya kasa tafiya. Ta nan  ta kwanta ciwo sabo da shi amma shine shi zai ɗauke ƙafa ya gudu ya barsu saboda wani ko? Yana so ya ce ya fi san su akan irin san da suke masa? Wai shi wanne iri mutum ne?

Wani irin siririn hawaye ne ya zubo mata, sai ta share tana sakar murmushin takaicin tare da sa hannu ta karɓa. Duk yarda take jin jikin ta haka ta sauko daga kan gadon ta ɗauki Noor ta goya sai suka zuba mata ido da mamaki suke kallan ta. Mayafin ta ne a jikin tun na shekaran jiyan nan da suka je wajen party.

ZARAHADDEEN Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin