50

21 0 0
                                    

50

*******"Na rasa ina zan sa rayuwa ta, kai fushi da ni, Hafsah ma fushi, me kake so nayi Hafiz?

Sai hawaye ya zubo masa, be damu da ya share ba .

Yace, "So kuke na mutu? Ko kuwa so kuke na kamu da wani ciwon? Ita tace na sake ta, akan me? Tasan yadda nake san ta da tattalin ta Hafiz? Kasan ita Waccen nake so? Yaushe zata bari zuciyata ta samu sarari ne Hafiz? Sannan kai....

Sai hawaye ya zubo masa.

"Nasan zaka yi fushi da ni, amma bansan zaka yi har haka ba Hafiz. Saboda wannan mutumin ya rabu da ku kuka yi rayuwar ku, har kuka kawo wannan matakin batare da ya san cewar ina existing a jikin ku ba. Duk wata gudunwa ta D investment nike baku, sanin cewar be san waye D investment ba yasa shi rabuwa da ni, har Anadyr ya je domin sanin waye D, amma be samu ba, saboda ba'a bada information akan komai na kowa haka ya haƙura ya koma. Na haɗa wannan kasuwancin ne da tarin kuɗin da na samu nida da Hafsah, da kuma wani abokin mu dake Albuquerque....

"Eloit?

Jinjina masa kai yayi, yana share hawayen sa.

"A lokacin na buɗe komai na haɗa hannu da mutane da yawa, dake suna san aikin namu yasa cikin lokaci ƙanƙani Allah ya sawa abun Albarka. Da wannan na tura Sakeenah ta siye wannan companyn da ke hannun mu a yanzu wanda kake riƙewa. Da kuma wanda Hafsah ke riƙewa. Companyn mu supermarket ɗin su Ummu da restaurant ɗin Hajja wanda da za'a yi mata ƙwacen shi amma be iyuwa ba, domin A. Madaki ke turo da duk wasu mutane akan cewar lalle sai sun haɗa hannu sun yi aiki da ku".

"Sanda na fito daga cell, Ɗalhat ya kai ni gidan sa, nine wanda na ɗaura wannan abun na turawa duka gidajen Tv amma A. Madaki yayi ruwa yayi tsaki aka share maganar, sannan kuma ya tura aka kashe Hashim. Saboda ya harbe shi a ƙafa ya kwashe dukkan wata kadara ta sa. Bayan mun rabu da Hashim a Airport, naji hankali na be kwanta da shi ba, jirgin mu kuma aka ce ba a yanzu zai tashi ba, sai na fito kawai na nemi shatar mota muka bishi a baya. Amma bamu haɗu ba sai da muka zo Zaria sannan na ganshi, shima inaga dan ya tsaya ne da ba zamu haɗu ba, muna daf da shan gaban sa kenan, wannan motar ta zo ta kwashe shi, drivern mu kuma ya bi wannan mutumin ashe ba driver ne ba SS ne. Bayan ya ajje ni na taimaki Hashim shi kuma ya kamo shi mun kai shi asibiti ashe har ya kamo shi yasa shi a Boot ɗin sa. Zai ajje ni nace ina san magana da shi. Anan yake sanar da ni cewar ya baza dukkan wasu jami'an tsaro akan duk inda nake a nemo ni wanda yace na koma nace masa ba zan koma ba, akwai inda zan je. Babu yadda be yi da ni ba akan nasar da shi nace masa a'a. Zuwa na nan ƙasar na ba zo ba ne dan haka kawai na zo ne domin yin wani aiki. Banda kai babu wanda ya sani, amma baka min uzuri ba shine kake fushi da ni ko?

Sai yaja ajiyar zuciya ya ajje. Yana cigaba da kallan Hashim.

"Duk wannan shekarun da kaga nayi bana nan, muddin naje sai A. Madaki ya zo yace a kamani idan kuma kana kokanto a kai na a yau mu tafi ido na ganin ido, zaka tabbatar da abinda nake faɗa maka, rayuwar ku da zaman hankalin ku Hafiz ya fi komai ba, nesa da yasa kun zama jajurtaccu a cikin al'umma, a yanzu da ku ake dubawa, domin kun zama madubi da kowa kan iya kalla ya kalli kan shi da shi, ko Taufiq da ka duba da baya san aiki, amma a yanzu fa? Kai ne zaka faɗa, idan ka duba kowa fa zaka ga ya sauya, har ta Ameer ɗin da kuke masa kallan wani Shashasha, Ameer na da basirar da bamu da shi, shi yasa ban takura masa ba akan sai yayi karatu amma nasan Zarah zata sa shi yayi".

"Kasan yana san Zarah ne?

Sai Deeni yayi dariya har haƙuran sa suna fitowa tare da goge sauran hawayen dake zubo masa.

Yace, "Tun farkon zuwan Ameer nasan da haka, kawai de yana jin tsoron bayyanawa gani yake kamar ba zan bashi ba, ganin be bayyana ba ni kuma..."

"Kai kuma yasa kake ta san sai ka haɗa ta da Hashim ko?

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now