33

19 1 0
                                    

      33

******Yana kwance akan gado dan wata irin gajiya yayi  dan duka be samu wani cikakkiyar lokaci ba na kan sa, daga jiya zuwa yau ɗin na ranar asabar, duk yarda ya so tunanin abinda yarinyar can tayi masa kar ya dame shi amma a banza, dan wani irin takaici yake jin kan sa a ciki. Ace yarinya ƙarama, yarinyar ƴar cikin sa ke sanar da shi irin wannan abun? Ke faɗa masa magana? Abinda ya kasa ganewa shine, inda suke da zama. Yanzu yana korar a aiki za'a ke masa kallon mutumin banza, amma har ransa baya san zaman ta a wurin da yake, baya so ace zata yi wani abu da zai tabbatar da cewar ya zalunce ta ɗin tunda ya lura babu wanda ya gaskata shi zai iya yin haka.

Tashi zaune yayi yana tunanin abinda ta faɗa masa cewar Fodiyo yayi magana. Taya ma za'a ce Fodiyo yayi magana? Da wane bakin? Karya kenan likitan yake masa ko me? Ya sake faɗa yana ƙara kwantawa. Likitan da ya tabbatar masa da cewar mutumin ya riga da ya shanye duka jikin sa, ba wai iya stroke na ɓari ɗaya ba, na duka jikin ne saboda abn daga duka ƙwaƙwalwar sa ya taɓa? Amma yake magana? Kenana cutar sa yayi ko me?

Ga tunanin kuma Deeni da aka bashi labarin irin tarin lashe nasarar da yake yi, nasara yake baya faɗuwa kamar de Fodiyo, yayin da yake so a ya gano waye shi ɗin? Abu ɗaya ya sani cewar shine wanda ya cinye su a sanda suka je Anadyr shi da Hashim. Idan haka ne kuwa yana da buƙatar sa a kusa da shi. Zai sa a masa bincike a gano waye shi?

Shigowar ƙarar message yasa shi duba wayar sa yana kallon abinda Hashim ya turo masa. Da wani irin sauri ya zubara tashi ganin abinda ya faɗa masa, zuciyarsa ba wani irin dagargajewa. Me hakan yake nufi? Ina Hashim ya san da wannan zancen? Waye ya sanar da shi? Kode Hashim ya haɗu da Mahaifiyar sa ne?

"Alhaji lafiya?

CewE Hajiya da shigowar ta kenan taga wata uwar zufa da ya haɗa, kamar wani sakarai ya tsaya yana kallan ta kafin ya nuna mata message ɗin.

"Daad na san da cewar ba kai ne ka haifeni ba, nida Ɗalhat da kuma Maryam. Abinda nake so da kai shine ka sani cewar dukiyar dake wurina tawa ce, ta ni ɗaya, haka ma dukiyar da ke wajen Ɗalhat nasa ne, sai kuma ta Maryam da baka bata ba. Bana jin ni da Ɗalhat ka cuce mu kamar yarda ka cuce Maryam. Dad mafita ɗaya nake nema. Ko da nemo min inda ƴan uwana suke ko kuma duniya tasan waye Mamman Nasir Alhaji Madaki. Na baka nan da 24hrs ka nemo min su idan ba haka ba kuma zan yi ɗaya daga cikin biyu. Zan kwashe duk wata dukiya dake cikin asusun mu. Da zarar na ga baka fito min da ƴan uwana ba kuma na faɗawa duniya waye kai".

Ita kan ta Hajiyar rawa jikin ta ya fara yi kafin ta samu waje ta zauna, tana dafe da ƙirji shi kuwa A. Madaki tashin hankali kawai yake ganowa zai fara tozali da shi. Duk tsarin sa, duk tsare tsaren  be taɓa tunanin hakan zata faru da shi ba. Dafe goshin sa yayi kafin ya karɓi wayar sa yana ficewa daga ɗakin yayi wajen balcony yana dannawa Hashim kira.

*****Yayin da Hashim ke kwance wani irin zazzafan zazzaɓi ya lulluɓe shi, amma ko nemon taimakon magani be yi ba. Su da ko kan su ke ciwo sai an kira likita, amma shine yau a zube a kan gado. Daƙyar yake tashi yayi sallah ya koma ya kwanta, baya da dauriyar zuciya shi kam a rayuwar sa. Duk yarda ya so kada ya yadda da abinda Deeni ya faɗa masa amma abin ya ci tura, ya kasa yadda da hakan, ya kasa amincewa da cewar  wai ba ba Dad ne ya haife shi ba. Ya yadda da Deeni kamar da can ya san shi, dan lokaci guda ya ji ya amince da shi, lokacin guda ya ji ya yadda da shi, yadda da be taɓa yi da kowa ba. Saboda ba kowacce magana ce ake ƙaryatawa ba, kamar yadda ba kowa ne zai zo ya faɗa maka ba.

Yasan waye Dad ɗin sa, ya sani, baya jin akwai wanda ya fishi sanin Dad. Amma abu ɗaya Hashim ya sani cewar ba zai taɓa cin amanar wani ba, ba zai taɓa kwasar abinda ba na s ba, baya da wannan hassadar a zuciyar sa. Fitowa ne kawai be yi ya faɗa ba, abinda yayi wa su Baba abin ya masa zafi, ashe ma ba sau daya ya ci zalun sa ba. To shi kuwa Baba wanne irin mutum ne? Da zai sake ɗaukan ƴar sa ya bashi a karo na biyu ba tare da ya duba da irin abinda ya faru ba a baya? Shin a duniyar nan akwai irin Baba kuwa?

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now