15

25 1 0
                                    

*****Shima kasa riƙe kan sa yayi sai da ya rungume ta gam, yana mai rarrashin ta, a haka suka ƙaraso suka same su a wurin, Hafiz shima hawayen yake sharewa, yayin da kowa yayi jugum batare da sun ce musu komai ba akan stroke ɗin Baba. To me za su ce musu? Ganin kuka da Ameerah ke yi bana ƙarewa ba ne sai kawai ya ja ta suka fita wajen asibitin suka zauna yana riƙe da ita, kafin ya ɗago ya kalle ta ya share mata hawayen yana mai haɗe goashin su waje cike da tausayin ta.

"Addu'a zaki masa ba kuka ba".

Ya faɗa da wata irin muryan mai sawa mutum nutsuwa, girgiza kan ta tayi tana mai riƙe hannun sa da riƙe fuskar ta, ta sauke ƙasa ta riƙe hannun gam.

"Yaya Deeni ka barni nayi kuka ko na ji sauƙin abinda nake ji a rai na".

"Kina so Babyn mu da be san komai ba ya cutu?

Sai ta tsaya tana kallan shi kamar yarda shima yake kallan ta, lumshe mata ido yayi alamar eh.

"Cuta ba mutuwa ba ce ba Ameerah, komai yayi farko yana da ƙarshe. Abu mai muhimmanci anan shine dukan mu mun san Baba ba zai taɓa aikata abinda aka ce yayi ba. Baba mutum ne da yake ƙaunar mu, yake san mu, yake kuma alfahari da mu kasancewar sa ƴaƴan sa. Idan kika duba rayuwar mu, dukan mu babu na  banza a cikin mu Alhamdulillah kowa ya mallaki hankalin sa da Baba yake da yaƙinin ba zamu sauya ba da izinin Allah. Bayan haka mene Baba be mana ba? Komai ya mana, ya nuna gata tun baya da shi har Allah ya hore masa".

Share mata hawayen fuskar ta, yana ƙara riƙe hannun ta. Yace, "Ko mutuwa Baba yayi a yanzu babu abinda zamu saka masa da shi sai addu'a da sadaka, sune kawai gatan da zamu masa muma muna masa irin wannan soyayyar da ya nuna mata. Mu godewa Allah be mutu ba, kuma in sha Allah lokacin sa be yi ba. Mu masa addu'a ba dare ba rana. Mu tsaya da ƙafar mu mu taimake shi".

Ƙwallae da ta zubo mata ta saka hannu ta share yana mai jan majina, a yanzu kawai ta ji tana san ta fitar da duk wata damuwa dake ran ta, da kuma Deeni kawai ta ji tana san yin maganar ba kowa ba.

"Faɗa min me kike san faɗa min".

Sai ta kalle shi, ya jinjina mata kai tare da lumshe idon sa cike da kwantar da hankali da kuma nutsuwar da ko baka san faɗa a lokacin sai ka ji zaka faɗa.

"Tunda naje gidan nan Yaya Deeni, bansamu kwanciyar hankali ba dai-dai da kwana ɗaya, wannan mutanen ba sa san Baba, ba san duk wani cigaban da Baba ya samu da kuma wanda zai samu. Dalilin da yasa suka nace lalle sai ni saboda sun san na iya duk wani kalar rubutu, sun san da cewar muddin naga wani abu to zan yi exactly irin shi ba za kuma a taba ganewa ba. Hakan yasa shi Daddyn yake kawo min takardu na yi signing ɗin Baba sometimes harda ta Yaya".

Sai ta kalle shi tana share hawayen dake zubo mata.

Tace, "Be tsaya anan ba, har sai da ya sani nake zuwa office ɗin Baba domin ɗauko musu documents ɗin project ɗin kuɗi. Da kuma ire-iren advertisement da jingles of advertisement, nake kawo musu. Abubuwan da na aikata Yaya Deeni ba zai faɗu ba wa Baba. Na cuci Baba na zalunce mu duka".

Sai ta sake fashewa da wani sabon kukan, kwantar da ita yayi s kafaɗar sa yana rarrashin ta sai da ta yi shiru, tsaf ya goge mata hawayen.

"Waye ya san wannan zancen?

"Ba kowa".

"Kar ki sanar da kowa kinji?

"Ba wanda zaka faɗawa? Ko Yaya ma?

Wani sihirtaccen murmushi ya sakar mata yana ɗan bubbaga kumatun ta tare da lumshe mata ido. Haka kawai ta tsinci kan ta itama da murmushin.

"Kina san shi ko?

Sai ta kalle shi jin abinda ya ce mata, sai tayi saurin girgiza kan ta alamar ehh sai kuma tayi saurin girgiza kai alamar a'a, sai abin ya ba su dariya dukan su sai murmushi ita kuma ta ɗan yi dariya tana rufe bakin ta dan sosai yarda tayi ɗin ya bata dariya.

ZARAHADDEEN Où les histoires vivent. Découvrez maintenant