51

28 1 0
                                    

51

******Deeni da Hafiz sun kasance suna aikin SS tare da abokin su Eliot wanda suka yi makaranta a Benin tare, su uku ne a ɗakin su. Shi Eliot ya kasance Christan sannan yana aikin SS, irin kula irin ta Deeni da Hafiz musamman Deeni da duk wani abu da akayi indai yana nan to yana sane da komai, hakan yasa Eliot janyo su suka shiga wannan harkar tare, sune suka bashi gudunwan yin abinda ya zo yi a makarantar ta su, daga nan suka ɗauke su aiki ta hanyar gwada su ta wuri daban-daban. Kafin suyi aikin sai da aka kai ruwa rana Sannan suka yarda, aikin SS ba abu ne mai sauƙi ba, wani irin sirri da ko matar sai gumu tayi gumu ake sani bare kuma family. Da wannan suka kammala makarantar su, sai de ba su tafi ba daga garin suna nan har sai da result ɗin su ya fito saboda aikin na su da suka tsayi. A aikin ne aka tura su Cambodia yin wani bincike akan wasu ƙwaya da ake shigowa da su Nigeria, ashe A. Madaki ke wannan safarar batare da sanin kowa ba, riƙe kayan da kama kayan da aka yi ne, sune suka sa A. Madaki zuwa har aka kama shi. Yayin da ya haɗa wa shugaban su tuggu cewar tare suke. Sannan kuma shine zai sa shi ya fita, wannan furucin da yayi ne ya janyo hankalin manya mutane da ke wakilta case ɗin, yayin da a ranar da daddare aka tashi bomb a prison ɗin A. Madaki ya gudu. Sanda ya zo guduwa Deeni ne ya kama shi shi da Hafiz suka kulle shi. Yayin da Deeni ya gana masa azaba iri iri da iri har sai da ya faɗi komai nasa. Ranar da zai shaidar a ranar A. Madaki ya sake guduwa bayan ya ajjewa Deeni note ɗin cewar duk inda yake zai kamo shi kuma sai sa yayi kuka da idan sa, ya rubuta ya ajje ba'a ja da shi. A lokacin Deeni murmushi kawai yayi. Sai yaga babu amfanin cigaba da bibiyar sa ko akai sheda dan yasan da sa hannun manyan su, aikin su aiki ne na sirri amma fa akwai ƴan cuwa cuwa a cikin sa, ba'a Nigerian ta mu ba, ba'a ƙasasashen ƙetaren ba, ko ina akwai macuta kuma manyan ne masu goyawa masu laifi baya. Be bada shaidar ba har aka kulle wannan mutumin dake shugabantar case ɗin A. Madaki a lokacin. Tunda ya baro Cambodia ya dena harka da can. Duk da yayi nasara dan shi kiraran sa shine nasara ta sace, baya faɗuwa baya asara nasara gaba ya bata ba baya ba.

Sanda ya Deeni ya kammala service ɗin sa, a ranar Ummi ta rasu, sai da ya nutsu sannan aka bashi duk wani report na accident ɗin da inda tayi da komai da muka motar da aka killa ce ta, da kuma wayar ta da komai nata. Tsayawa yayi,yayi bincike dan sosai maganar A. Madaki ta dawo masa a lokacin da yaga motar Ummi. Da ya tsananta bincike kuwa sai gashi  zargin sa ya zo ɗaya. Shi yasa har yau yake a tsaye ganin cewar ko A. Madaki be rasa wani abu nasa ba, to tabbas A. Madaki sai ya ruguza ta kowacce hanya. Domin yana tinƙaho da cewar yana da nasara, nasara tasa ce, shiyasa yayi amfani da su Ameerah ganin ya kawo ƙarshen sa, yayi amfanin da nasarar da yake tinƙaho da ita ya raba shi da half and quarter na dukiyar sa. Ya kuma ragargar duk wani harkar sa ta kasuwanci, duk wani kuɗin da ake damfarar sa ba kowa ba ne sai Deeni, yayin da ya rabarwa da dukkan dukiyar ga marayu domin dukiyar ba tasa ba ce ba, ya kuma sa a Foundation ɗin Ɗalhat.Sai de duk wannan abubuwan be san waye Deeni ke yi ba, ba su taɓa haɗuwa ba tun daga wannan ranar, yayin da shi kuma A. Madaki be taɓa sanin cewar a Nigeria ma Deeni yake ba, duk a tunanin sa Uwar sa a Nigeria ashe ba haka ne ba, Shima Deenin a Nigeria yake......

Duk wannan tunanin Deeni yayi su ne cikin seconds ɗin da ba su fi goma ba, idan sa ƙem a kan madaki yana sakar masa wani irin lallausan murmushi tare da miƙa masa wani flash mai azabar kyau golden sai sheƙi yake.

"Nasan hakan zata iya faruwa shi yasa na taho da wannan. Idan ka je gida ka sa ka gani zamuyi magana da kai".

Daga haka Deeni ya koma ya zauna yana harɗe hannun sa tare da kulle idan sa.

"Me kake nufi da ni?

"Wai kai, kai waye ne?

Murmushi Deeni yayi yana tasowa.

"Ka manta ni waye?

Baƙin ciki da takaici A. Madaki yake ji, ji yake kamar ya shaƙo Deeni tsabar haushi.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now