40

54 3 2
                                    

40

*******Shigowar da Hajiya tayi ne yasa shi kallan ta.

"Ka zo kayi sallama da yaran nan za su tafi".

Wani shegen kallo ya wurga mata..

"Banda kuɗin da suka kwashe min har wani sallama zan sake yi da su?

"Nawa suka ɗauka ne? Kuma kuɗin nan da shi ake ɗauka ake yin cefane, yaushe rabon da ka ji na tamabaye ka kuɗi? Amfanin ajiyar kuɗin kenan".

Rasa abin cewa yayi ma kawai ya fita ya shiga closet ya barta a wurin, duk yarda zai mata bayani bazata gane ba.

"Na tura musu 5-5m daga account ɗin ka".

Ba shiri ya fito.

Yace, "Me naji kin ce kin tura musu? Kamar miliyan biyar biyar?

"Ashe ka ji".

Ta faɗa zata wuce, tsaki ya ja ya rigata fita, sai de basa nan har sun tafi.

"Ni Saratu kina da hankali kuwa? Kina ji yarda kuɗi yanzu baya shigo min amma shine zaki ɗauki har 10m ki bawa yaran nan?

"Amma ai kasan da tafiyar ko? Kuma ba su kai ɗai za su tafi ba, ita Safiyya ta ce min acan zatayi birthdayn ta, shi yasa suka tafi da ƙawayen ta da abokan ta".

"Nace duka ƙawayen na su a kuɗin wa aka biya musu kuɗin jirgin da na dawowa?

Duk da yasan amsar da za'a bashi amma ya dake yayi tambayar, gaban sa har wani faɗi yake. Ba dole kuɗin da su ƙare ba, an kwashi shegun ƴan iska an tafi da su wani waje. Anya sun san halin da yake ciki kuwa?

"Wai Alhaji lafiyar ka kuwa?

"Uhm duk yarda zan maki magana da bayani ba zaki gane ba, dan haka ki rabu dani".

Ya faɗa yana komawa closet ɗin sa. Yau kam shi ba'a sa ba ya tashi. Wani be taɓa zuwa companyn sa ya zuba wannan uwar hannun jarin ba sai de shi ya zuba, to yau ga wanda ya fishi san samun riba. Kenan fa ribar idan aka samu tasa sai ta ta kowa yawa,tunda shi ne yake ɗaukan rabi da kwatar kuɗin.

Shiryawa yayi ya ci abinci kaɗan, sannan ya sake fita, yana zuwa office ɗin sa ya tarar hau ɗin da ya fi na Kano da Kaduna. Dan wannan gaba hannun jarin wanda suka zuba kuɗin su, ya nin ka musu sau biyar, amma sai de shi wannan wani daban wai shi D investment da be san da shi ba shima. Tashin hankali ba'a sa masa rana. Yanzu shine yake jagorantar companyn a kowanne lokaci companyn zai iya zama na sa, shifa yanzu 5% ne nasa, duka 95% ɗin na D ne. me ya ci me ya bawa ma'aikatansa, be taɓa tunanin jakai ya tara a ma'aikatan ba sai a wannan karon, dan harta wanda ya kwaso daga Kanon Directorn da ƙananan ma'aikatan ba su da amfani.

"Da ace Dr. Usman yana na da duk haka bata ta so ba, yana da ƙoƙarin yin aiki. Bamu taba samun matsala ba dashi".

Cewar wani ma'aikaci wanda yake ɗaya daga cikin manyan manyan managers ɗin companyn ya faɗa.

"Wannan haka yake, ni na fara tantama anya ba magauta ba ne suka sanya hannu a wurin korar sa?

Wani ya sake faɗa, haushi ne ya turnuƙe A. Madaki.

Yace, "Ga zancen da muke ga wani zancen da kuke yi mana".

Hakuri suka bashi.

Yace, "Waye D investment?

"Sakeenah ce tayi wakilce shi".

"Waye ce Sakeenah?

"Ansn companyn take aiki".

"A kira min ita".

A take a wurin aka dokawa table ɗin ta waya, ba'a ɗau lokaci ba sai gata nan ta shigo.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now