13

26 1 0
                                    


✨ *ZAHARADDEEN* ✨

          
                   By

       *Hijjartabdoul*

           13.





*****sun fito da su fita, shi kuma Ɗalhat ya sake dawowa domin ɗaukan abinda ya mata, daman mantuwa yayi ya dawo kuma ya manta be ɗauki abin ba ya sake fita, da zai fita yaga shigowar motar ta layin su, itama ta gan shi yanzu kuma dake ran ta a ɓace yake gudu kurum zankaɗawa ganin sa da tayi sai kawai ta ƙara speed ɗin gudun, ba dan shi ya rage nasa ba da sai de Allah ya kiyaye hakan ma sai da ta buge shi da gangan tayi gaba. Tsayawa yayi yana kallan ta, dan tabbas jikin sa ya bashi akwai wani abu dake faruwa ko kuma faru. Ita kuwa gida ta wuce da Ameerah suna gida babu kowa a gidan sai tayi amfani da mukullin ta, ta buɗe suka shiga, tunda suka taho kuma take faman yi mata har suka zo, ko da suka iso Ameerah tayi kuka ta gode Allah, babu yarda ta iya kawai kulle idan ta tayi ta kwanta a kan gado.

"Dake kin mai da ni ƴar iska ko? Ina magana kin kwanta ki rufe ido, irin ki gaji ki bari ko?

Tashi zaune tayi, ta jingina da gadon, bata ce komai ba.

"Dan uwar ki ba zaki bani labarin abinda ake maki ba? Ke wai mene yake damun ki ne?

"Ni fa Anty ba abinda suke min, kawai fa dan ta taɓa ni ne shine ya mare ta kuma anjima da marin shine yanzu tace yau sai ta rama".

"Waye ya mare ta din?

"Shi mana".

Ta faɗa tana sake zamewa ta kwanta, dan amai take ji, wannan tashin hankali da ta gani kawai ya wargu tsa ta mata lissafi.

"Waye shi?

Ta faɗa tana  fara cire kayan ta.

"Kai Anty".

"Dan kar uwar ki sunan mijin naki ne ba zaki iya cewa Tsalha ne ba, ga abinda ya faru ga abinda ya faru har yayi mata haka?

"Ke wai dan gidan ku meye yake damun ki Ameerah? Meye yake damun ki? Me ya ke samun ƙwaƙwalwar ki ne? Ki buɗe baki kiyi magana ba zaki iya ba?

Shiru tayi, ita kam, dan bata san me zata ce mata ba.

"Ki ci gaba da abinda kike, babu inda zaki koma".

"Na'am?

Ta faɗa tana raurau da ido tana kallan ta, juyowa tayi ta kalle ta.

Tace, "Eh lalle Ameerah faɗa min kin kamu da san mijin ki. Ko ki ce min Anty ina san mijina. Ni kuma ba zai hana ni cewa ko mutuwa zaki yi ba zaki koma wannan gidan ba. Dan uwar sa ko shi be fimu san ki ba....

Ganin ta tashi ta nufi toilet da gudu ya sata binta da ido, sai kakin amai ta ji, sakar baki tayi tana bin toilet ƙofar toilet ɗin da ido, da kayan da ta cire a hannu bata cigaba da naɗewa ba, jin shiru de yasa ta bin ta ganin tana wanke wajen ga shi ta galaibata, sai kawai ta kamota ta fito da ita waje.

"Ameerah ciki kika yi?

Ta faɗa calmly, kamar ba ita ce ta gama masifa fa yanzu.

"Ciki kuma Anty?

"Da naga kin yi amai ai. Kuma de gaki nan ga ki nan".

"Dan na yi amai sai ace ciki ne?

"Ai nima tambayar ki nayi, idan ciki ne a san yadda za'a yi da shi dan wallahi Ameerah ba zaki koma wannan gidan ba".

Shiru Ameerah tayi tana ƙara kwanciya a kan gadon, dan ba ƙaramin jin daɗin kamshin Antyn na su take yi ba. Tana yi luf da ita daga nan bacci ya ɗauke ta. Ita kuma bayin ta wuce ta gyara tayi wanka sannan ta fito, kallan ta kai wurin ta, kafin ta tako tana ƙare mata kallo ga hannun ta raɗau ya fito akan fuskar ta, hannun ta tasa ta shafi wajen sai tayi motsi hakan yasa ta kallan ƙafar ta da ta kumbura yanzu haka tayi targaɗe ma.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now