49

27 0 0
                                    

49

*********Be ajje ta a ko ina ba sai a kan gado, yana ajje ta ta juya masa baya tare da rufe idan ta, duk wani kuka dake san ƙwace mata haka ta dake ta haɗiye shi ta shanye, abubuwan da bata shanye ba a lokacin da ya tafi sune suka ta so mata, kawai abinda take tamabayar kan ta shine me ye laifin ta? Son da take masa ko kuma nuna damuwar a kan ta? Wai haƙurin akan abinda yayi mata, abinda ya dame shi kenan.

Ya jima yana kallan ta, ya rasa ta ina zai fara bata haƙuri da baki amma yasan ba zata ji kiran ba a yanzu dan kowa waye sai ya ji haushi.

"Tashi ki yi wanka ki sauya kaya".

Uffan bata ce masa ba, da mamaki ya bita da kallo ganin ga shiga toilet, kafin ta fito ya fito mata da kayan bacci, da towel ta fito fuskar ta babu yabo ba fallasa, ko kallan inda yake de batayi ba, ta je gaban madubi ta shirya shi kuma ya fita ya haɗo mata abinci ya shiga wanka. Da kallo ta bishi tana jin wani irin ruwa ruwan hawaye na san zubo mata, da sauri ta mayar da shi tana hana kan ta yin kukan.  Sallah tayi sannan ta naɗe a kan gadon ta kwanta. Addu'a tayi tana tana hana kan ta tunanin sa, tana yin salati tana salati har bacci ya ɗauke ta ko da ya fito, ganin tayi bacci yasa shi zuwa saitin kan ta ya tsaya yana kallon ta, ita kaɗai tasan ya rashin sa yayi mata illah, kamar yadda shima shi kaɗai yasan me yake ji a game da ita. Bakin ta ya kalla yayi masa peck ɗan yatsine fuska tayi tana gyara kwanciyar ta. Tashi yayi ya je ya shirya ya zo ya kwanta a kusa da ita, tare da janyo ta, yana janyo ta ta buɗe ido ta zuba masa dukkan idan ta kafin ta tashi zaune ta ɗauki pillow da ta fice masa daga ɗakin gaba ɗaya ta koma parlour, da kallo ya bita shi be kwanta ba, shi be tashi zaune ba, har ta fice dafe goshin sa yayi da ya ji yana sara masa ba kaɗan ba. Kafin ya tabbatar da tayi bacci sannan ya ɗauki bargo ya fita, abinda ya gani baƙaramin mamaki ya bashi ba, a ƙasan dandaniyar tiles ta kwanta, kuma tayi baccin ta, duka hannun ta ta haɗe ta ɗaura akan pillown tana baccin ta hankali kwance.

Tsabar mamaki kawai tsayawa yayi yana ƙare mata kallo, kafin ya je ya ɗauke ta cimak ya ajje akan doguwar kujera, yana ajje ta ta tashi ta koma inda pillown ta yake ta kwanta tare da juya masa baya. Shi mamaki ma wannan rashin nauyin baccin nata, da ba haka take ba ai. Wata zuciyar tace ' shekarar ka nawa bakwa tare ' ajiyar zuciya ya sauke ya tafi da bargon ya rufa mata, yana rufa mata ta yaye shi, tare da tashi ta sauya waje ta kuma juya masa baya ta kwanta. Duk yarda ya maida kan kujera duk jiran da zai yi bacci y ɗauke ta, daga ya maida ta zata tashi ta koma, haka daga ya rufa mata bargo zata sake sauya waje. Gashi dare ya tsala suna abu ɗaya, hakan yasa shi barin ta kawai yana zuma akan carpet tare da jingina da kan sa a jikin kujerar, a haka bacci ya kwashe shi, be tashi ba sai da asuba.

Kawai kallan ta ya tsaya yi, tabbas ya ƙure haƙurin ta, wataƙila sai ta gan shi a gadon asibiti sannan zata haƙura ta sauko dan ba zai jure wannan fushin ba. Da wanne zai ji, da nata ko da na Hafiz? Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, ya tashi ya fita masallaci sai da ya dawo sannan ya tashe ta. Sallah kawai tayi ta sake kwanciya a kan tiles ɗin.

"Dan Allah ki hau gado ki kwanta".

Tashi tayi kawai ta fice masa a ɗakin, da mamaki ya bita da kallo, wayar ta ce ta fara ringing hakan yasa shi zuwa ya ɗauka ganin Ameer ne.

"Anty wallahi ga ƴar ki tun jiya ba muyi bacci ba, sai kuka take wai ita Mommy".

"Bari a turo a ɗauke ta".

"Yaaa ina kwana".

Yayi saurin faɗa, amsawa yayi cike da kulawa sannan suka kashe.

Zarah tace, "Yaya ne ya ɗaga?

Ɗaga mata kai yayi.

Tace, "Taab, har ta haƙura da wuri haka? Ta bada kai bori ya hau?

"Ke me kike nufi?

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now