53

17 1 0
                                    

53

*******"Kin haƙura?

Ya faɗa yana sake rungumo ta tsam a jikin sa. Rufe idan ta tayi tana ɗaga masa kai alamar eh. Murmushi yayi mata yana shafa kan ta, itama murmushin tayi tana sake shigewa jikin sa.

"Kin san Yusrah?

Ɗagowa tayi ta kalle shi, ta girgiza kan ta alamar a'a.

"Baki san ta ba?

Ta sake ɗaga masa kai. Rungume ta yayi tana mayar da da ita yarda take, ya cigaba da shafa mata kan.

Yace, "Yusrah Yayar ki ce, daga Hafiz sai ita. Yusrah?

Sai ta tashi daga ɗaya daga jikin sa tana zama da kyau tana kallan sa. Ganin irin kallan da take masa yace.

"Nima fa bansan komai ba, sai da na tafi can gidan su Baba Kebbi anan nake jin komai".

"Ya akayi ka san gidan?

"Sanda Hajja ke bada labari, tayi kwatancen unguwar da layin da kuma gidan, kawai daga nan sai na wuce can. Anan naga Baban su Baba".

"Be mutu ba?

Murmushi yayi mata yace, "Ya rasu, amma ita tana nan, Babar su A. Madakin".

"Wanna shegiyar muguwar matar. Allah ya isa wallahi abinda ta ringa min, shegiya kalar iyyamurai".

Dariya ta bashi shima ya tashi zaune yana yaye bargon da suka rufa, yayowa tana masa kallan ya haka?

"Ni ba abinda zan gani, ni da bana leƙe idan leƙawa zan yi na leƙa ta bargo mana".

Ya faɗa ya sake janye bargon, riƙe bargon tayi gam tana masa kalar tausayi.

"Idan kika sake zagi?

Ya faɗa yana saka idan sa cikin ta, marairace fuska tayi alamar ka yi haƙuri.

"Zaki sake?

Sai da ta kumbura fuska sannan ta girgiza masa kai.

"So kike mu koma ruwa ko?

Ware ido tayi tana girgiza kan ta da sauri irin innocent girl ɗin nan.

"Koma ki kwanta".

Ba musu ta koma ta kwanta ta juya masa baya murmushi yayi shima yana kwantawar a kusa da ita, yana kallan sama.

"Yusrah tun tana shekara biyu A. Madaki ya fara treating Baba akan ta, saboda wani irin so da kowa ke yi mata, kasancer ita ce mace ta fari da aka fara haifa a familyn su a lokacin. Wannan yasa har kukan ku ma yake san ta, tsakanin ta da Hafiz shekara ɗaya ce. A haka yake cimma burin sa a kan Baba, har ya raba shi da komai nasa sannan ya ɗauke yarinyar ya kai ta dangin mahaifiyar sa dake ƙauyen Kebbi. Da zai zo dawo kuma yace sun yi hatsari ta mutu motar ta ƙone, dagaske sun yi hatsarin kuma motar ta ƙone shiyasa ma aka yadda da shi ganin kurjewar da ya yi sosai. Daga nan kuma ganin Baba ya samu aiki yana yin kasuwancin sa dai-dai gwargwado ya fara tara abin duniya sai yayi masa sharri a lokacin Baba ya auri Yaya Bilki. Ke kuma kina ƴar ƙarama. Sharrin da yasa Baban Baba korar sa daga gidan sa, yace masa ko ya ji labarin ya mutu kada ya zo kan gawar sa. Babu wanda ya san da cewar A. Madaki ne yayi masa wannan sharrin sai Baba da Mahaifiyar A. Madaki. Sune kawai suka san da wannan zancen. Daga lokacin Baba ya dawo Kano da zama. Sai de A. Madaki yaga Baba a wani taron da yake ɗaya daga cikin company na Nigeria masu ci. Wato FD company sai ya san yarda zai yi ya sake rushe Baba a komai domin baya san wani abu da zai sa Baba ya cigaba a rayuwar sa. Wannan dalilin ne yasa shi haɗa aure da Ɗalhat sai gashi Alhamdulillah auren ya ja silar da ya wargaza A. Madaki duk bamu so akayi auren ba, amma kuma ƙaddara ta riga fata".

ZARAHADDEEN Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum