41

22 1 0
                                    

41



******Washegari ta kasance ranar juma'a ce, hakan yasa su daga wajen aiki suka wuce sallah, daga sallahr juma'a kuma sai suka dawo gida abin su, suma su Zarah gidan suka dawo domin samun wadataccen hutu, gashi kuma da safe da za su fita Deeni ke sanar da ita cewar Hashim zai zo. Hakan yasa Ameerah ta tursasata suka koma gida da wuri dake suna hutun makaranta.

Ameerah ce ta shigo ɗakin Hafsah da sallama ta shigo, ganin ta da tayi a kwance akan abin sallah yasa ta saurin nufar ta tana taɓata.

"Anty ko jikin ne?

Tashi zaune tayi ta jingina tana girgiza mata kai.

"Har kun dawo? Ina Noor?

"Tana wajen Zarah".

Cewar Ameerah da mamaki a kan fuskar ta ganin irin sauyin da Antyn na su ta samu, maganar da take mata cikin hankali da kwantar da murya, babu wannan ɗacin ran dake tattare da ita. Ko bata da lafiya idan ka mata magana to amsar da zata baka ma aiki ce idan ba'a zage ka bama ka ci sa'a.

"Anty sannu".

Ta sake faɗa tana ɗan dafa ta, da mamakin ta murmushi taga tayi mata.

"Karki damu na warke. Fita ma nake so nayi na gaji da kwanciyar nan".

Ta faɗa tana tashi, taimaka mata tayi ta tashi. Cire hijabin nata tayi tace ta ɗauko mata ƙaramin mayafi, suka fito tare.

"Ina zamu je?

Cewar Ameerah, Zarah ce ta ta so tana mata sannu ita da Ummu, murmushi kawai tayi musu ta fita ta ƙofar baya ta barsu su suna sakin baki.

"Anya Anty ce kuwa?

Cewar Ummu tana ɗan leƙa ta window tare da komawa ta zauna a cikin parlour.

Zarah tace, "Ba ruwana nikam".

Ameerah komawa itama tayi ta zauna  tana cewa, "Anty gaba ɗaya ta sauya, anya ba Yaya Deeni ne ya sauya ta ba?

Zarah tace, "Wanne Yaya Deenin? Bade Yaaaa ɗina ba ko?

"Da wani ne bayan shi ?

"A'a baki san waye Yaya Deeni ba Shiyasa, shi fa ba komai yake magana akai ba, amma duk abinda yake faruwa yana sane da shi, kawai kallan kowa yake yi".

Ummu tace, "Yaya Deenin?

"Uhm".

Kawai tace bata ce musu komai ba.

Ameerah tace, "Me za'a haɗawa Yaya Hashim ɗin?

Shiru Zarah tayi bata ce komai ba.

Ummu tace, "Eh kiyi mana magana me zamu haɗa masa?

Banza ta sake yi da su.

Ameerah tace, "Wai ke haka ake yi ne?

"Wai dan Allah Ameerah me kike so nace maki ne?

"Ki ce yana son abu ka za da ka za mana".

Tsaki tayi bata ce musu komai ba.

"Ni kwa Zarah kin iya zance ma kuwà?

Cewar Ummu.

"A'a ban iya ba sai Ummu".

Ameerah tace, "Bari na koya maki yarda ake yi toh, tunda ke sabon shiga ce".

Kallan su kawai take yi, bata jin daga Ummu har Ameerahn sun waye ce ita a wurin tara samari, da har suke ce mata wai za su koya mata wani abun, ita dariya ma taji suna bata, to da iya Ameerhan me ta sani ma?

Ameer ne ya shigo da gudu ya hauro ta kan kujerar da Zarah ke.

"Mun dawo".

Cewar sa yana ƙoƙarin cire babbar rigar da suka saka yau su shida Taufiq ta ɗaurin auren Deeni. Zarah ce ta taimaka masa suka cire.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now