"Innalillah wa'inna ilaihirraji'un".

Ya ji likitan ya faɗa yana share zufa da cire face mask, yayin da wani nurse ɗin ya rufe masa idon sa suna dafe kan su. Da ido kawai Ameer ke bin su, shima neman hawayen sa yayi yarasa.

"Wai shikenan ya samu lafiya?

Girgiza kansa Likitan yayi.

"Sai haƙuri mun rasa shi. Allah jikan sa".

Dum maganar ta zo ta wuce ta kunnen sa, haka daman ake mutuwar? Kafin ya ƙifta ido ace shikenan har ya mutu? Kode beje da kyau ba. Mutuwar da take da zafi da ƙuna? Kuma kasan ina adadin lokacin da ya ɗauka yana jin azabar a jikin sa? Wani sashi an zuciyar sa ya tunatar da shi. Share zufar dake goshin sa yayi ya saki hannun sa, ya fito kawai kallo ya bisu da shi babu buƙatar ya sanar da su, dan da'alama likitan ya sanar su komai. Report aka kawo musu na mutuwar tasa aka bawa ƴan sanda sannan aka basu gawar tasa suka tafi da ita.

    Suna komawa gida suka tarar da ƴan sanda suna jiran su sammaci tashin hankali da suka ganin acikin idanun su da kuma irin rashin da aka musu shi ya sanyaye ƴan sanda  suka kai report cewar babu Deeni ya gudu an nemi shi an rasa. Wannan abun ba ƙaramin haushi ya bawa A. Madaki ba. Be taɓa tunanin Hashim da Deeni suna da alaƙa ba shi yasa be kawo akai ba akan abinda aka sanar da shi. Shide burin da kada asirin sa ya tuno yasan kuma tunda ya kashe Hashim ai yayi mai wuyar shikenan. Bashi da sauran damuwar da zata rage masa sai ta Deeni. Wanda be san shi ba, kawai labarin sa yake ji, gashi a gadon asibiti baya da lafiya.

*****Sun haƙura bayan sun sha kukan sun godewa Allah, anyi zaman makoki dan mutane har daga Katsina dangin mahaifin su sai da suka zo, ana yin bakwai suka watse kowa yasan nayi. Suka koma harkar su sai de har yau walwalar su bata dawo dai-dai ba, sai d saka kwana ashirin sannan suka ware suka dawo normal, Major Kabir baƙaramin gudunmawa ya bawa Ɗalhat ba wurin ganin cewar ya cika masa burin sa na zama wani shugaba a ƙasar ta su wanda suke sa ran zai kawo ci gaban Al'umma amma ganin mutanen ba wani cigaban sa suke nema ba yasa shi cewa kawai ya fara bunƙasa unguwar da su Umma suke ciki tukunna dan ta fi unguwar da su Ɗalhat ɗin ke ciki neman agaji da taimako. Ya kafa Foundation ɗin taimakawa al'umma da kuɗin da Hashim ɗin ya kwaso a gidan Madaki. Kuɗin ne kawai aka gani dan komai ya tattara ya miƙawa Deeni kudin ne be karɓa ba yace ya kaiwa su Umma. Sun tashi daga wannan unguwar sun dawo kusa da su Deeni. Hafiz ya koma Abuja da aiki companyn de da ya bari yau shine a matsayin babba a companyn ɗin, shi ke kula da komai da lura da komai. Baya da shawara bare ma ya rubuta wasu su kwafa sai kawai de kawai aga ya aiwatar. Ga wani irin sauyi da yayi musu daga nan raha da dariya ya koma mai shiru shiru da ɗaure fuska ya dawo marar mutunci a cewar su. Tunda baya barin su su shaƙata. Idan kaga dariyar sa ko maganar sa to da Sakeenah ne da a yanzu yake ji ya kamata ya bata dukkan wata kulawa tunda yarinyar bata rasa komai ba. Gashi ta taimaka musu a sanda suke da buƙatar ta.

Haka itama Hafsah ta koma aiki, ita ce kuma shugaban a companyn na su, abunda take so shi ake yi, tana komawar ta sa aka mayarwa kowa albashin sa yayin da Mu'azzam ya dawo matsayin Deeni, duk inda za su je kuma da shi take zuwa. Har ta Kawun Aishs a ƙasan ta yake, duk sati take zuwa taga me ake yi, wanda irin kaya ake producing masu ya kuma ake kayan? Duka ma'aikatan da suke aiki su ke kuma san riƙe aikin su ta basu damar yin aikin nasu wanda ba su da dama kuma ta sauya musu aikin nasu daga babban matsayi zuwa ƙaramin matsayin office ɗin haɗaka. Mai sunan ta kuwa wacce suka je bikin ta itama ta sauya mata matsayi babba daga Mu'azzam sai ita ga wani irin mutunci da suke zubawa abin su. Sai de fa ta koma Hafsahn ta wannan amma idan ta dawo gida takan zauna suyi wasa da dariya da su. Ga Noor dake ƙara wayo abinta kullum sai an kawo ta dan kullum sai Ameerah ta zo gida indai bata je shago ba, idan suka ta so daga makaranta, sai ya biyo ya zo ya ɗauke ta. To ba wani babba a tare da su Hajja ce da Gwaggo sun yi faɗan a banza shi kuma Hafiz sam baya zama dan tunda yaje be samu kan sa ba.

ZARAHADDEEN Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz