"Kenan muna sai ka bamu company kenan ko?

Ya ji wani ya faɗa daga cikin masu hannun jari a companyn su Hashim, sai kuma hankalin sa ya dawo jikin sa ya ɗan yi murmushi tare da zuba musu shayi yana miƙa musu, kowanne su.

"Kuyi haƙuri, komai zai dai-dai ta".

"Yaushe kenan?

Cewar mai companyn Kaduna.

"Ko zuwa Monday".

Murmushi yayi masa. Yace, "Mr. Madaki ni ba irin mahaifina bane ba, ni da kake gani, babban ɗan duniya ne bani da mutunci da kirki, dan na gyara aka bani wannan aikin, Shiyasa nace a sakar min komai nayi aiki na, idan ka saɓa alƙawari komai zai iya faruwa da ni da kai. Babu ruwana".

Daga haka ya shanye shayin nasa tas sannan ya tashi ya fice, da mamaki A. Madaki yake kallan sa, har ya fice kafin ya dawo da kallan sa ga sauran mutum huɗun da a yanzu suka yarda suka amince suma har sai Monday ɗin.

Murmushi yayi kawai yana ɗaga shayin sa, duk wanda ya sha wannan shayin baya taɓa iya masa musu, amma shi wancan ya ga ya sha sannan ya faɗa masa maganar karshe ya kuma sha, idan be da aljanu to kenan abinda ya sa a ciki baya masa tasiri? Shiru yayi na wani lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya, zai sake ji da shi, amma dole ya mallaki wannan companyn nasa na manshafawa. Abinci aka ce an shirya yace su barshi baƙin har sun tafi. Shima tasowa yayi ya fito ya zauna a kusa da Hajiya.

"Yanzu kuma ya naga ranka a ɓace yake?

"Hashim da Ɗalhat ni za su tozarta? Su bari wasu can su saka share ɗin su a companyna? Gashi nan na rufe companyn, banyi tunanin za su dawo ba gashin nan sun zo suna faɗa min magana".

"Aikuwa a sani na, basa aiwatar da komai batare da sun sanar da kai ba".

Shiru yayi, ko kuma de da sanin nasa? Basarwa yayi.

Yace, "Yanzu naga Hashim nasan inda yake".

Zabura tayi tace, "Dan Allah? Yana ina ? Me yake yi ?

Kallan ta yayi alamar meye haka?

Ɗan yaƙe tayi tace, "Ni wallahi tsoro nake ji, kada asirin mu ya tuno, kasan fa mun yi zalunci da yawa".

"Zalunci? Dan mun kwashi kuɗin mu shine zalunci? Taya su so muka yi, faɗa min meye a ciki? Munje kun kwashi wasu ne? Na mutane da muka sani muke ɗaukewa ba na wasu ba".

Ya faɗa yana maka mata harara tare da tashi ya wuce, ta sake ɓata masa rai, shi ga abinda yake damun ta, ita kuma ga banzan tunanin da take yi. Shekara da shekaru asirin nasa be tuno ba sai yanzu?

"Yarda asirina be tuno ba haka zai taba tunowa ba, ɗaukaka da samun nasara yanzu na fara, nasara tawa ce bata kowa ba. Ni ke da nasara ba kowa ba, nasara a jinin jikina take, dan haka gobe ma nine da ita".

Ya faɗa yana sakin murmushi sosai, tare da yin shirin kwanciya yana tunanin sa, sannan ya kwanta yin bacci, daman sallah ba damun sa tayi ba, India shi kadai ne mantawa yake da ita, sai de idan a cikin taro ne wannan kwa, har tsayawa yake yi yayi mai kyau kamar sune za su bashi ladan. Bacci yayi mai cike da kwanciyar hankali yayin da ya manta ya saka wasu a cikin rashin bacci kwanciyar hankalin.

******Daada ne sosai yake faɗa, ta inda yake shiga bata nan yake fita ba jin abinda A. Madaki yayi wannan mutanen. Babu wanda ya tanka masa har yayi shiru ya samu waje ya zauna, duk tsirko tsirko suka yi suka kasa zama.

"Yanzu ba zai bar su, su huta ba?

Ya sake faɗa cike da takaicin wannan mutumin.

Ɗalha yace, "To wai an tabbatar shine yayi ɗin?

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now