"Dad?

Hashim ya faɗa cike da mamaki sai kuma yayi wani gajeran murmushi.

Ya kalli Hafsah yace, "Wanne meeting ɗin zakuyi?

"Nima bansani ba, sai naje".

Jinjina kan sa yayi.

Yace, "Idan meeting ne na haɗa kar company, ki kirani zan shiga".

Da sauri Ɗalhat yace, "Ka shiga kayi me?

"Na shiga nayi replacing companyn mu".

"Amma Hashim gaskiya baka da hankali".

"Ni kuwa nake da hankali Ɗalhat".

"Please ki kira ni".

"Uhm".

Kawai tace ta fita, sai da fita a ran ta tace 'to da me zan kira ka ɗin' hakan kuma be san ta koma ba. Sanda ta shiga reception ɗin da kallo kowa ya bita ganin irin shigar da kyan da tayi ga fuskar ta tayi wani irin fayau da ita, sai wani annurin da bata san yana fita a fuskar ta ba. Babu wanda tayi wa magana daman ba magana take da kowa ba har ta shigo office ɗin su, suma suka bita da kallo, musamman su Zee da suke mata kallan kucaka yau kam ba ƙaramin kyau tayi musu ba. Daman mutun idan yana shiga ɗaya ka saba ganin sa a cikin idan yasa wani kayan sai kaga ya fi dacewa da shi fiye da tunanin mai tunanin. Yayin da wani sashe na zuciyar Aisha yayi wani irin sanyi dashi ganin cewa zata ga Zaraddeen, da ta tabbatar da blocking ɗin ta yayi.

"Yau za ga Darling Deeni".

"Darling wahala de".

Cewar Zainab, zata yi magana Khadijah ta matso alamar gulma.

Tace, "Bana ji ana cewa an kore su ba?

Zainab tace, "Ke raba ni da wannan gulmar ta companyn nan, ƙaryar fa?

Aisha tace, "kunga ba haka ba ne ba".

"To meye?

"A'a bakomai".

Ta faɗa tana jan bakin ta. Tana sake kallan ƙofa ko zata ga Deeni, sai de be shigo ba, sai tayi ƙwafa a ran ta tana ɗan yaƙe.

Hafsah kuwa samun wajen Mu'azzam tayi ta zauna,  ganin yaje ya dawo baya nan, ɗaukar tablet ɗin sa tayi tana duba schedules ɗin da suke dashi a ranar.

"Yau kuma kune a companyn na mu?

Cewar Mu'azzam yana zama, ɗan murmushi tayi masa kaɗan.

Tace, "Ehh ba".

"Amma kun dawo  kenan ko?

"Ehh ba".

Murmushi yayi shima bece komai ba, kafin ta ɗago ta kalle shi.

Tace, "Ya faɗa maka zan haɗa ku da wani?

"Ni kuma? Deeni?

Jinjina kai tayi alamar eh.

"Be sanar dani ba".

Shiru kawai tayi bata ce komai ba, har ta gama duba abinda zata duba. Ganin suna da meeting shabiyu yasa ta cewa.

"Kana zuwa meeting ne?

"Ina zuwa, yanzu ma muna da meeting ɗin ai. Da A. Madaki".

"Wanne irin meeting ne? Na cikin company ne?

"A'a masu zuba share ne za su zo, har daga waje ma".

Jinjina kai tayi tare da cewa tana zuwa, bata jima ba kuwa sai gata ta zo da Hashim, tunda suka shigo Mu'azzam yake kallan sa, ko shine wanda za su haɗu ɗin? Yayin da su Zainab aka fara iyayi ga ɗan gidan A. Madaki sune daman ba su taɓa ganin sa ba, dan duk wayanci suna ganin sa kwanaki yana zuwa, ba su san me yake zuwa ba amma suna ganin sa. Haka suka ta so wai zan suyi hoto da shi, dariya ma shi suka bashi, babu kalar wanda be gani shikam, a mata sai de ya bada labari amma ba'a de a bashi ba. Hakan yasa ko kallan inda suke be yi ba, kawai da murmushi ya bi su yayi gaba.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now