Hannu yasa ya share mata ƙwallar idan nata.

Yace,"Duk hali na, amma kike kuka akai na?

Hannu tasa ta buge shi cike da sakalci.

Tace, "Kai ko".

Sai ya rungume ta, yana jin tsantsan farin ciki na ratsa shi. Kafin suka shigar cikin gida tana maƙale da shi. Gaisawa suka yi da su Baba sannan aka kaishi ɗakin su Hafiz ganin magriba ta kusa.

"Meye haka?

"Me fa?

"Janyo ni fa kamar wani raƙuma".

"Ni da kike janyo ni raƙumi ne?

Ya bata amsa yana mata kallan tsakar ido, harara ta zuba masa, tana zama akan kujera.

"To ni bana san haka".

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ta.

"Sabir".

Sai kuma yayi shiru bece da ita komai ba, ita zai fara faɗawa ko kuma Umma? Ko Baba? Ko Hafiz? Wa ya kamata ace ya fara sanarwa? Me za'a yi?

Sumar kan sa ya shafa, cike da wannan tunanin dake ran sa. Ya rasa yarda zai yi da rayuwar sa. Ƙwaƙwalwar sa toshewa take nema tayi. Wanne irin abu ne haka? Me yasa zai yi musu haka? Why Sabir? Me Sabir yayi masa?

Haɗe kan sa yayi da jikin kujera, yan furzar da iska mai zafi, yayin da Hafsah ta zuba masa ido kawai tana kallan sa. Gaba ɗaya jijiyar kan sa ta fito raɗau da ita, idan sa yayi ja. Shiru kawai tayi masa tana zuba masa ido batare da ce komai ba, daga ƙarshe ma tashi tayi ta wuce ɗaki ta barshu a wurin. Da ido kawai ya bita yana rufe idan sa. Hafiz ne ya shigo ya same shi a haka.

"Deeni lafiyar ka kuwa?

Girgiza kan sa yayi cike da alhinin abinda zai sanar da shi, ya gyara zaman sa.

Yace, "Ina Hashim ɗin? Sai yanzu suka sauka?

"Wallahi, jirgin na su ne ya samu matsala shiyasa suka jima ba su zo ba".

Jinjina kai kawai yayi.

Yace, "Sun haɗu da Maryam?

Jinjina masa kai kawai yayi yana cigaba da kallan sa.

"Sabir wani abu ya faru da shi a makaranta".

Ya faɗa a hankali yana sauke a jiyar zuciya kafin ya koma ya kwanta a jimin kujerar yana rufe ido.

"Me ya faru da shi a school ɗin?

Wayar sa da tayi ƙara ne yasa shi yin shiru, ganin wayar Kawu Isubu je kira yasa shi saurin ɗagawa.

"Assalamualaikum Kawu".

*******Major Kabir kuwa da tambaya da komai ya isa ƙauyen, dan ya taba zuwa Gumel sun yi wani abu a garin, tun yana saurayi, hakan yasa shi be mance hanyar ba, sai de sauye sauyen da yaga an samu a garin. Hanyar ƙauyen ya tambaya aka nuna masa. Da tambaya da komai ya isa har ƙofar gidan, sai de abinda ya bashi mamaki ganin irin mayan motocin dake fita da shiga suna yi wani waje da ƴan machine dake ta fito da Z Yoghurt, abin ba ƙaramin mamaki ya bashi ba, kasa jurewa yayi ya tambaya ake sanar da shi ai companyn Yoghurt ne a wurin. Shi yasa yayi ta nema ashe a Jigawa yake, Jigawar ma ba ko ina ba sai wannan ƙaramin ƙauyen amma Meyasa?

Da wannan tunanin ya isa inda aka kwantanta masa. A ƙofar gida ya tsaya yana kallan gidan da aka masa kwatance, amma be tabbatar ba sai da ya fito ya sake tambayar aka sanar da shi. Ajiyar zuciya ya sauke ya zubawa ƙofar gidan ido, gini ne ginin ƙasa amma kuma ansake masa shafe sai yayi kamar sabo. Daga cikin gidan kuma yana iya hango yadda aka yiwa bangon siminti shima sabo. Yana nan a tsaye ya kafawa gidan ido, yana jin wani irin sabon al'amari game da wannan gidan. Wai nan shine asalin sa. Nan shine tsohen sa. Nan ne mafarkin rayuwar Yayan sa...

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now