*****Yayin da Major Kabir yana can a asibiti ya kasa zaune ya kasa tsaye, banda zirya babu abinda yake yi, tsabar yarda hankalin sa ya tashi ma ko tambayar ba'a sin yarda abinda ya faru be yi ba. Tunanin yarinyar sa yake, wacce ya shafe shekaru da dama yana jiran haihuwar ta, ya ɗauki dukkan wani irin so da ƙauna ta zuba mata, kowanne mahaifi yana son ɗan sa, amma shi nasa soyayyar kan ƴar sa daman ne, ba zaka misultu ba. Idan ta mutu me zai kama? Ya zai yi da rayuwar sa? Be san wani ikon Allahn ba amma a yarda yake ji yasan shima mutuwar zai yi.

Ɗaya daga cikin sojojin nasa ne ya motso yana bashi ƙwarin gwuiwa, ganin tunda suka zo ya goya hannu a baya yake safa da marwa, ajima ya leƙa ya tafi ya sake leƙawa. Ga kuma wasu daga cikin malaman makarantar nan sun yi zugum, su Headmistress kamar ta saki fitsari akai. Kun san iyyamurai da tsurewa musamman akan yara, gashi kuma ita ce shugaba a primary section. Ket kawai ake jira ta zubara ga wannan sojoji da suke ciki da wajen asibitin.

Likitan ne shida nurses suka fito yana ganin su ya nufo shi yana tamabayar sa ba'a sin me ya faru.

"Ana da buƙatar ayiwa, yaron aiki akai, a hassashen mu nan da kwana uku ko biyu zai iya rasa ran sa ko kuma ya haukace muddin ba'a masa aiki ba".

"Innalillah wa'inna ilaihirraji'un".

Ya fara ambata a ran sa yana nan natawa, yayin da abin ya tsaya masa a rai ya kasa wucewa, ya kasa tambayar ita yarinyar fa.

"Ita yarinyar kuma, alhamdulillah mun samu nasarar yi mata ɗinki a inda ta samu tsautsayin. Akan ta kenan, kuma bata bugu ba kamar shi yaron. Dan shi kamar wani abu aka sa aka buga masa".

Runtse idan sa yayi zuciyar sa na wani irin bugun da be taɓa jin irin sa ba.

"Yaushe kake ganin za'a yi aikin?

"Sai de gobe zuwa jibi, yanzu zamu rubuta report mu aika can Lagos, dan likitan ƙwaƙwalwa ne zai yi aikin, sai mun ga yarda yace da kuma uzurin sa".

Jinjina masa kai yayi, yayin da ya musu bayanin a yanzu zai iya yin magana amma ba kowanne abinci zai ci.

"Akwai buƙatar iyayen sa gaskiya su sani da wuri domin ayi aikin".

Daga haka ya wuce, ya bar shi, yayin da Headmistress ɗin ta ɗaura hannu akai ta saki wani uban ihu tana kiran Allahn su. Haka yace su bashi numbern Baban yaron. A take suka yi waya makarantar aka turo masa.

"Sir! Ka kwantar da hankalin ka tunda Najma bata samu rauni ba...

Wani shegen kallo da yayi masa ya sa shi saurin haɗe maganar sa yana sara masa tare da ƙamewa da kuma furta sorry sir, yana shiga taitayin sa. Ƙwafa yayi mai masifar ƙara wacce ke nuna ran sa ya kai ƙololuwa a wajen ɓaci. Kawai dan yarinyar sa nata be yi worst ba sai ace kada ya damu a kana yaran wasu. Shi soyayyar ƴar sa kawai ya sani da kuma yarda yake mata, amma be san soyayyar ta su ba akan ɗan su.

"Assalamualaikum".

Ya ji kamilalliyar muryan Deeni ta cikin wayar, mai tafiya da dukkan wani imani da ruhin mutum tare da saukarwa mutum da nutsuwar daya samu lokaci guda, batare da yasan ta ina ne nutsuwar ta zo masa ba. Har sai da ya kasa riƙe kan sa ya samu waje ya zauna  yana dafe zuciyar sa da ya ji bugun ta ya sauya daga marar nutsuwa zuwa mai natsuwa.

"Assalamualaikum".

Deeni ya sake faɗa, jin anyi shiru. Yayin da Hafsah tayi ƙwafa tana zabga masa harara a fakaice tare da gunguni cewa"idan ba'a magana mana a kashe ai ba dole ne ba".

"Walaikumussalam".

Cak shima ya tsaya, Allah yasa lokacin suma sun zo ƙofar gidan su Ɗalhat. Da Ɗalha ne ya taho da su sanda ya zo inda aka kwantanta masa. Ji yayi kamar muryan Abban sa ke masa gizo.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now