Safiyya tace, "Wannan shekarar sai na gama zagaye 7 wonders of the world".

"Yaushe zaki tafi?

"Ehh nan da kwana biyu haka".

Musaddiq yace, "Ni ba zan biki ba wannan shekarar, mun haɗa da friends ɗina zamu tafi Egypt".

"Me zaka je ka ɗauko a wannan ƙasar? Ka tuna last zuwan mu nan muka je?

"Wannan zuwan ma ita zan je, nida abokai na".

"Dad ka ƙaramin kuɗi wannan da ka bani ba za su ishe ni ba".

Hajiya tace, "Wai Musaddiq me kake yi da kuɗi ne haka? Kashe kuɗin ka fa yayi yawa".

A. Madaki yace, "Ke kike bashi? Ka sai duk abinda kake so, uban ka yana da kuɗi, kuma babu mai ja da shi, dan ku nake nema ba wani ba".

Yayin da suka ringa ihun murna, suna rungume Daad ɗin na su, ita de bata ce komai ba tayi shiru.


*******"Taya za'ayi ace yarinya sai ni kawai zan ne ɗaukar ki?

Ummu tace, "ke kaɗai take so".

Bata kula ta ba, ta wuce wurin Ameerah dake bacci hankali kwance.

Tace, "Tashi ungu ƴar ki".

Ta faɗa tana ɗaura mata ita a cinya, ita kuma ta fice, ita kam ba zata iya ba, bata haihu ba, ba kuma za'a kashe ta ba lokacin ta be yi ba. Tana bata suka fita sai aka ci sa'a batayi ba,tana karba bacci ta yi.

A wurin aiki kuwa, banda hararan Aisha ba abinda take yi, suna nan zaune Sadiq ya zo ya kawo mata takardar da ta manta. Da mamaki Aisha ke kallan sa.

"Sadiq?

Ta faɗa tana ƙara sowa inda yake sai ga su Zainab nan suma.

Yace, "Zee? Me kuke anan?

Hafsah tace, "Zaka bani ko hira da su zaka tsaya yi?

"Yi haƙuri gashi".

"Ɗan aiki ka koma? Ina jin kai da ƙwalisar take?

Cewar Aisha tana masa wani irin kallan renin wayo, ganin sa sanye da Kayan aikin sa da duk penti amma a wanke su tas, pentin da yake jiki ne za'a ga kamar kayan datti ne da su.

"To ya za'a yi? Haka rayuwar ta ke ai".

Khadijah tace, "Allah Sadiq har gobe ina san ka".

Kai tsaye Sadiq yace, "Allah Khadijah har gobe bana san ki".

Dariya Zainab da Aisha suka yi, dan wannan ce amsar da yake bata a kullum India tayi irin wannan maganar.

"Kai yanzu me kake yi?

"Aiki mana".

"Aiki wanne iri?

"Aikin katako zance maki ko carpentry?

"Kai Sadiq? Kawai ka zo muyi auren mu Babana zai baka gida da mota da komai na rayuwa".

Shiru yayi ya rabu da su kawai ya yake kallan su, idan ya kalli wannan sai ya juya ya kalli wannan, rayuwa kenan, wasu su sauya wasu kuma su sake sauya hali mai kyau ko marar kyau amma ga su wanna har yau ba su sauya ba".

"Mu'azzam ma anan yake"..

"Haba de? Ku ce duk anan kuka haɗe abin ku?

"Bamu san wanda ya ɗauke shi aiki ba, kasan ni ai Uncle ɗin na ne mai companyn".

Cewar Aisha tana wani fari da ido. Murmushi kawai Sadiq yayi yana mamakin su wai mai companyn nan batare da ta san ya san komai na companyn ba, shima ra'ayine baya yi. Ameer ne ya shigo ganin jiran yaƙi ƙarewa kuma ya kira shi be ɗaga ba yanzu haka a silent ya sa ta. Lokacin Aisha na bashi labarin Deeni.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now