"Meye haka?

Haɗe rai tayi, ta sake yunkurin tashi.

"Tamabaya nayi fa? Ko kuma kin..."

Sai ya ƙarasa faɗa mata yana a kunne, bata san sanda ta wuntsula shi ƙasa ba ta yi toilet da gudu tana rufe ƙofar, sosai abin ya bashi dariya, yana shafa kan sa, ta fito tayi kan abin sallah.

"Daga faɗar gaskiya sai a nemi a kayar dani?

Banza ta masa ta tada sallahr ta. Sanda ya idar duka idan sa
ya zuba mata yana kallan yadda ta ke figar kan ta, ba tayi a hankali, 'ita komai nata kamar yaƙi' ya faɗa a ran sa. Yayin da kawai ya fara tunanin yau idan ta je company ya zata kasance yake yi. Baya san wannan faɗan nata da maza suna faɗa tana faɗa, yasan kuma tabbas sai anyi haka waraka yau ta zamana ranar ta ta ƙarshe a companyn ɗin da shi da ita.

"A dena kallo na tunda ba matar so aka ajje ba".

Murmushi yayi mata.

Yace, "Kuma baki san ki zama matar so ɗin ko?

Itama murmushi tayi tace,"Bana cushi ba kwarjini".

"Aww haba?

"Aww dagaske".

Murmushi kawai yayi yana tashi tare da naɗe abin sallahr. Ya zo ya karɓi abin hannun nata ya zaunar da ita, tana kallon shi ta cikin madubi.

Yace, "Kina mace baki iya tajar kai ba, tsifar ma baki iya ba".

"Kaga bani abu na bance ka faɗa min magana ba".

"Allah ya baki haƙuri. Ni yau rabuwar lallami nake so muyi, ko na samu ɗan goodbye hug da safe journey kiss ko?

"Ni da ba matar so ba?

"Aww haka ne".

"Aww ka manta?

Daman ya faɗa ne dan ta ce ita da ba matar so ba?, tunda ya lura tun jiya ake sanar da shi, da ita aka masa welcome. Shi kadai ya san murmushin da yake, har ya taje mata kai tas, ya ƙulle mata shi sosai. Be firgito ɗin nan ba irin yarda take yi. Idan ta saka Hijabi aka ganin.

"Ba zaki ki ce kin gode ba?

Hararan sa ta yi.

Yace, "Kin ga banbanci ke da matar so ko? Shiyasa nake so nayi nayi, nayi auren nan, ko hankalina zai fi kwanciya, idan na tashi da safe a gaida ni, a haɗa min ruwan wanka, a fito min da kaya na, a shirya ni, a bani abinci a baki a kuma raka ni waje mota na tafi aiki, yayin da naje office ya kira ni aji na je office".

Sakar baki tayi tana wani irin abu da fuskar ta..

Tace, "Baka ji me bakin ka yace ba?

"Ke ma ai kina so na, tunda ke ce kika ce kina so da bakin ka b wani ya matsa maki ba".

"Tunda ba'a so na ai kaga ba zan yi ba ko?

Ta faɗa tana ficewa daga ɗakin, sosai maganar ke mata zafi amma ta ɓoye bata nuna masa, sai de ta makaro domin ba komai ake ɓoyewa Deeni ba, idan ma an ɓoye sai ya gane. Murmushi kawai yayi yana shigewa toilet.

********Kallan uban kayan da aka jibgo mata kawai suka tsaya yi, duk wata tsaraba da aka ba ta ƙauye wank abun ma bata san shi ba, Sabir ya kwashe ya bata, har ta teddyn Ummu mai masifar kyau da take ta ajje da ita, tace duk wanda ya yi aure ya haifi mace ita zata bawa, har ita ya haɗo mata da shi. Yayin da ita kuma take ta murna musamman teddyn ta, tana da ƴar tsana da teddy da yawa amma idan kaga murnar da take akan wannan teddyn da ko kuɗin ta ta ɗaya be yi ba sai ka yi mamaki, anan Abban ta ya lura, ita kyauta ba tsadar ta ce ke saka murna ba, a'a wanda ya baka ɗin ne ke saka nishaɗi. Ga kuma Yoghurt ɗin da aka haɗo ta da shi wajen cartoon uku su yi da shi? 

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now