Wani shegen murmushi tayi.

Tace, "Allah yasa duka duniyar ce ke. Abinda ya dame ni da na sani kawai shine ki tabbatar da kin sanar da ni meye ɗana yayi maki".

"Idan naƙi fa?

"Ki sha wani marin".

"To ba zan faɗa ba".

Cewar Antyn tana hararan Hafsah. Ɗaga hannu tayi zata ƙara marin ta, matar ta riƙe hannun ta tana bata haƙuri.

"Kiyi haƙuri, mu bi komai a sannu".

Yayin da shugabar makarantar ta ƙame ƙam a waje guda tana jin tsoron shiga al'amarin nan.

"Yaran ba sa karatu indai wannan na wajen ne, musamman Sabir da Najma. Ayi ta daura musu karatu ba sa iyawa, jiya suka yi bacci a aji. Na haɗa su duka ajin na zane. To ba zan iya ba ina dalili".

Gyaɗa kai kawai Hafsah take yi tana matsowa kusa da ita.

"Saboda wannan dalilin? Meye sunan ki? Ke ba malama bace? Baki san meye ya dace ba dake ?

Kiran da aka yi mata a waya ne yasa ta dakatawa batare da ta ce komai ba, kawai kallan ta take yi yarda take wayar da yaren su. Yayin da Hafsah take gyaɗa har ta gama.

"Zaki san kin yi da ni, yau sai kin yi kwanan cell".

"Nayi kwanan uban cell ba cell. Dan uwar ki ki sa a kulle ni ɗaurin rai da rai. Banza jaka".

Ware ido matar tayi cike da Mamakin wannan yarinyar tana ƙara kallan ta, ita bata da tsoro? Idan ita ce ai haƙuri zata bayar dan mijin ta sai da yace ba ruwan sa, Babar sa ce ta zuga ta tace taje shine ta zo, idan haka ta faru da ita ta tabbatar da ko kallan inda take ba zai yi ba.

"Kuyi haƙuri don Allah komai ya wuce, hakan ba zai sake faruwa ba".

"Nadiya please ki ba su haƙuri".

"Wa? Wallahi ba zan bayar ba, kuma zata san ta mare ni. Yaro kuma da take zancen sa indai Sabir ne, na wajen nan ko? Wallahi na ringa dukan sa kenan".

"Ashe kema zaki ringa dakuwa".

Cewar Hafsah tana ƙoƙarin cire hijabin ta. Caraf ta ji an riƙe hannun ta, ko bata ɗago ba ta kalle shi ba tasan tasan waye. Hakan yasa ta yi kicin-kicin da fuska. Tana haɗe rai. Kallan Antyn yayi.

Yace, "Dan Allah kiyi haƙuri".

"Haaa...me? Wai kana nufin abinda tayi wa Sabir be dame ka ba?

Juyowa ya kalli Headmistress ɗin.

Yace, "Kuyi haƙuri dan Allah, hakan ba zata sake faruwa ba in sha Allah".

"Bu***ba".

Ta ji ta faɗa tana ƙara sake kallan sa.

"Zamu haƙura amma sai an cire shi a makarantar tukunna, dan bama ɗaukan irin wannan renin hankali. Yara da zarar kun kawo su, sun tashi daga hannun ku sun dawo hannun mu".

Cewar Nadiya.

"Ehh ba damuwa zamu cire shi".

A zafafe ta ɗago ta maka masa harara tace, "Ai kuɗin shekara uku muka bayar, dan haka sai an biya mu kuɗin da ko term be yi ba. Shegiya dan gin matsiya ta".

Dafe goshin sa Deeni yayi yana kallan ta. Wannan yarinyar bade sa ciwon kai ba.

"Ba kuma iya shi za'a cire ba. Duka yaran mu zamu cire, kuma ko zaku mutu sai kun bamu kuɗin mu Allah kuwa".

Juyowa ya kalle ta. Yace, "Muje".

"Muje ina?

Ta faɗa har wani huci take yi na an hanata abinda take so. Hannun sa ya sa ya gyara mata hijabin ta da ya zame.

ZARAHADDEEN Where stories live. Discover now