"Mu tafi ko?

Ta faɗa tana kallan Deeni, sai da ya gama kallan kowa har su Aisha dake zaune suna kallan ikon Allah, su ga zai tashi ko ba zai tashin ba, ba su gama tunani ba sai gani suka yi ya miƙe ya tattara file ɗin sa yayi gaba.

"Kai kuma fa?

Ta faɗa tana kallan Mu'azzam, shima tashin yayi ya bi bayan Deeni.

"Ya aka yi kika san wannan?

Cewar Kawun Aisha, juyowa tayi ta kalle shi.

Tace, "Bana jin idan mutane biyu suka yi magana suke tunanin babu wanda zai ji, ko ya ji wannan maganar. Bare kuma maganar da aka yi ta ba mutum ɗaya ba, ba mutum biyu ba, ba kuma uku ba. Ita magana wanda ake tunanin be ji ba, shine yaji ta. Kawai ana ji ne ayi kamar ba'a ji ba".

"Me kike nufi?

Murmushin takaici tayi, tana kafe shi da wannan idan ta nata Masha Allah da su.

Tace, "Abinda nake nufi, bango ma yana iya faɗar munafurci".

Tayi masa wani banza kallo ta wuce, baki a sake suke kallan ta, yayin suka sallami sauran da ba su tafi ba kowa ya kama gabansa.

Su Aisha kam da sauran ma'aikatan da ake gulma, waje suka samu suka zauna ake gulmar Hafsah da Deeni, duk a tunanin su bata jin su, ita kuwa sarai tana jin su, ko Mu'azzam dake gefe da ita shima yana iya jiyowa, ya na so ya mata magana amma tsoron ta yake ji, shiyasa ya zaɓi da yayi shiru kawai yayi abinda yake gaban sa.

Zainab ce tace da Aisha, "Kinga ki haƙura da shi, dan wallahi da'alama mijin tace ne. Kada ki kuskura kiyi wannan kuskuren shiga gidansa".

Khadijah tace, "Abinda nake jiye maki kenan, kiga de ranar ta je ta janyo shi kamar wani ɗan ta, shi kuma abin haushin zungui-zungui yana binta baya. Yanzu ma fa kiga sai abinda tace masa yake yi".

Shiru Aisha tayi tace, "Kin san kuma akwai sanda ya zo gidan mu, ba nace muku ya zo ba? To beci komai ba, wai Madam ta hana shi ci".

Ita Hafsah dake jin su sai tayi tunanin Madam Hafsah da yake faɗa, yayin da gefe ɗaya kuma na zuciyar ta na yiwa Aisha dariyar auren sa, dan ta tabbatar abinda yake mata sai ya fi wanda zai yiwa Aisha, ta wani wajen har gwara ita ma akan Aisha ba.

Tana nan zaune har lokacin tashin su yayi yayin da su kuma suke aikin na su na gulma daga wannan suyi wanna girgiza kan ta kawai tayi. Tana ratayaa jakar ta lokacin shima ya fito, tare suka fita su dukan har Mu'azzam da ya tura machine ɗin sa, suna kallan sa suka ya fita.

"Wai dan Allah me ke damun ka?

Shiru yayi mata bece da ita komai ba. Ƙara ƙulewa tayi.

Tace, "Amma kasan abinda kake babu kyau ko? Kasan wannan shirun naka baya da amfani ko? Ba kuma zai amfane ka da komai ba wallahi".

"Ni ban yarda da wannan maganar ba da ake cewa wai mahaƙurci mawada ci. Ta ina ne mai hakuri zai zama mai Wada ta? Ta wanne ɓangaren? Ta kowanne bangare cutar sa kawai ake yi. Sannan da ake cewa wani mai haƙuri kan dafa dutse har ya sha roman sa ta ina?

"Idan ba fadar bahaushe ba, da san mayar da mutum komawa ba, bana ganin zan iya yin wannan haƙurin, bangan ranar da za'a zalunce ni ba ace nayi haƙuri. Wallahi ba zan haƙura ba".

"Muslunci ma haka yace idan an mare ka inda ba za'a ka iya yin haƙuri ba, ka rama ko ?

Ta faɗa tana tambayar sa, duk da tasan hakan ne, tasan kuma ba zai yi mata magana ba, maybe yau baya jin maganar ko sai ta gama zubar ta ya gasa mata magana, amma bata damu ba.

"To ni de ba zan iya ba, ba kuma zan iya gani ana zaluntar wani ba namma nayi shiru. Babu abinda ya min fi".

"Kuma kai ma".

ZARAHADDEEN Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora