"Auren ta za'a bani, Wallahi san ta nake Mommy".

Wani banzan kallo ta masa, tana mai da hankalin ta ga ƙauwar ta ta.

Tace, "Ina jin ki".

"Zuwa nayi ki taimaka min dan Allah. Wallahi ba zan iya zaman garin can ba".

"Me ya faru".

"Saraki ne yayi retire, kuma ta tattaro mu ya kawo ƙauyen su, sannan yayi aure bayan ya rabani da komai nawa, ya ɗauki ɗan sa da yake so ni kuma na barni nima da wanda nake so, suka tafi da amaryar sa, ni kuma na tattaro kayana na dawo wurin Umma dan ba zan iya zama a wancan ƙauyen ba, itama Umma tunda na dawo, gorin yau daban na rana daban na dare daban, duk akan abinda zamu ci, na siyar da komai nawa, ga sata da Fa'iz yake yiwa ƴan unguwa shine muka dawo nan da zama".

Jinjina kai kawai Hajiya take yi tunda ta fara tana kallan ta.

Musaddiq yace, "Taab! Wallahi Anty ba'a gidan nan, ba zamu zauna da ɓarawo a gida ba gwara tun wuri ki tabbatar da kin tattara tsommakaran kayan ki kin bar mana gida".

Safiyya tace, "Gaskiya nima abinda zan ce kenan, ba zamu iya haɗa inuwa ɗaya da ku ba".

Anty tace, "Ni kuke faɗawa haka?

"An faɗa ɗin ko da abinda zaki ce?

Cewar Musaddiq, girgiza kan ta kawai tayi cike da mamaki, yayin da Fa'iz ya tsaya yana kallan su. Yaran da suke haba haba da juna idan sun haɗu amma shine yau za su wulaƙan ta su.

Hajiya tace, "Yarana sun yi Magana, babu buƙatar yin magana, idan zaki koma gidan mijin ki, ki koma dan ya fi maki alheri kuma ba zai taba gudun ki ba".

Share ƙwallar ta tayi.

Tace, "Dan Allah ki taimaka min, ko dan wannan azumin dake bakin mu dan Allah".

Alhaji yace,"Gaskiya ba zamu iya ba, zaku iya komawa inda kuka fito".

Fa'iz yace, "Ko ba ku bamu mazauni ba, kun ci da mu dan Allah ku taimaka ku bamu kuɗin motar da muka zo. Wallahi bashi Maa ta ara da zummar za'a maida mata idan mun zo sai mu biya".

"Nawa ne bashin?

Cewar Alhaji. Hajiya tace, "Wai ba su zaka yi? Baka san wace Saratu ba yanzu haka cutar mu zatayi wallahi, ba wani bashi da ta ci".

Fa'iz yace, "Wallahi bashi muka ci".

Ya faɗa yana saukowa ƙasa. Yana su taimaka masa, yayin da Anty ke zaune kawai tayi jugum tana tunanin rayuwar su ta baya, komai suka samu Rahma, komai Umman su ta nemo ita, har gwara ita takan turowa da Umman kuɗi akai-akai amma ita wacce ke so ɗin Umman na faɗa mata bata taɓa turo mata ba, bare kuma ta tako ta zo inda take. Da sunan wai ta zo duba ta, idan tace ƴar ta ce ke auren A. Madaki ma ƙaryatawa ake yi har ta dena faɗa.

"Tashi mu tafi Fa'iz".

Cewar Anty. Yayin da Alhaji ya ɗauko bandir ɗin ƴan dubu-dubu, Fa'iz har ya fara murna koba komai za su biya bashin da suka aro kuma za su sa kayan abinci su dena zuwa karɓar sadakar da ake yi, amma sai gani yayi sun ya irgo dubu biyar ya bashi.

"Kwa biya bashin da kuka aro".

Hannunsa na rawa yasa zai karɓa Musaddiq ya warce yace, "Haba Daad gaskiya ba za'a ba su ba, ka sani ko ƙarya suke mana, ta Mom ce kawai su cutar da mu".

Sunkuyar da kan sa Fa'iz yayi. Sannan ya miƙe yana ɗaga Anty.

Yace, "Bari de a baku 200 kwayi kuɗin taxi".

Ya faɗa yana buɗe table ɗin dake kusa dashi ya ciro rafar ƴan ɗari biyu, ya ciri ƙwaya ɗaya tal ya cilla masa. Wani irin ruwan hawaye ya ji idan sa na cikowa da shi. Abin har abin mamaki, wai shi kamar sa ko ba komai ko ba su san shi ba yadda suke da kuɗin nan ai ya ci ance sun taimaka masa idan ya nemi taimako. Tabbas ya yarda da maganar da Mahaifinsa ke masa ta cewar ba mutane duka ne suka san darajar mutane ba, da kuma darajar taimako, su je su zauna ta wani lokaci za su gane hakan, sanda suka gane su sanar dashi ya zo ya ɗauke su, su koma.

ZARAHADDEEN Donde viven las historias. Descúbrelo ahora